← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 120

Sashe 98

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zama suka yi Fatima ta turo baki ta kalli Ammi ta ce "Ammi wai Grandma ce take tambayar su Abba ina Baby take? Shi ne fa na ce an mata aure duk suka nuna ba su san maganar ba, ni kuma tsaf nasan an yi mata aure kema kuma kin san da hakan, amma dai ga ki ga Abba ki faÉ—a masa ko zai yarda da gaske ne sun aurar da ita wa mahaukaci. "

A zabure Abba ya É—ago yana zaro idanu ya kalli Fatima cike da tsananin tashin hankali jin kalamanta na karshe, baki na rawa ya ce "Ba.. Ban gane me kike nufi ba Fatima? Mun aura mata mahaukaci kuma? Ba na son shirme fa."

Turo baki ta yi tana kallon Ammi da ta kalli Abba da mamaki, aje wayar ta yi ta gyara zama ta ce "Lalle Abbansu! Kai da kanka ka ba da aurenta wa mahaukaci wanda take jinyar shi ita da Abdul, amma tun farko ma kun nuna ba ku so.. Nan ta shiga faɗa masa yadda aka sha artabo da Abir akan aure ta kafe ta ce sai shi take so ta aura.." Salati Abba yake bai san ba lokacin da ya mike tsaye ya fice bai ce da su komai ba, duk ya kiɗime jikinsa ya dauki rawa da kyar ya iya buɗe ƙofar palon ya fita, Ammi ta riƙe baki ta ce " Ke ni ma fa har yau mamaki nake na auren Abir, kuma tabbas akwai abin da aka yi wa 'yan gidan nan har suka yi wannan aika-aikar ba tare da sun lura ba.."

Fatima ta matso kusa da Ammi ta ce "Haka ne Ammi, ni ma haka nake ji har yau, ko ba komai ai Baby jininmu ce ya kamata asan wa za ta aura saboda rayuwarta abin tausayi ce, ranar fa naje gidan Yaya Abdul muna hira da Hafsat take faɗa min irin rashin darajar da Abdul yake yi wa Baby, ni kaina na sha mamaki ganin yadda suke amma yake mata cin mutumci, lalle fa Ammi akwai abin da ake ƙullawa a gidan nan wanda ya haddasa faruwar duk lamarin nan. "

Ta ja numfashi ta kalli Ammi sai kuma ta ɗaura da cewa, "Anya kuwa Ammi ba ke ba ce kika ƙulla wani abu dan a manta da Baby? Saboda kin ce mana kin tsane ta dan ta fimu kyau da farin jinin jama'a ga Abie ya fi su Abba dukiya, mu ma kike saka mu muna tsangwamar ta in ta zo inda muke."

A razana Ammi ta kalli Fatima cikin tashin hankali, tashi ta yi daga inda take ta matso kusa da Fatima ta ruƙo hannunta murya na rawa ta ce"Ha.. Haba Fatima, yanzu da hankalina zan sa ɗiyar ɗan'uwana a wannan halin? Ko kin manta shi Yaya Ibrahim ɗin iyayenmu uwa ɗaya uba ɗaya suke? Ai duk tsanar da na yi wa Abir ba zan taɓa yi mata irin zalincin nan ba, ni fa dama ƙiyayyar tawa ganin ana fifita ta ne akan ku komai Abbanku ya samo sai ya ce mai Mamana, in daga Office ya zo sai ya sa a kawo masa ita nan ku kuma ya share ku hakan ne ya sa naji na tsane ta, amma in ba haka ba Wallahi ba zan iya yin wani abu da zai cutar da ita har haka ba, wata irin cuta ta kai a aura ma mahaukaci wanda ba ka san ranar warkewar shi ba?"

Shuru Fatima ta yi tana wani ya tsine fuska dan ita sam ba ta yarda da maganar Ammi ba, karshe ma tashi ta yi ta nufi part ɗin Umma tana yan wake-waken ta. Ko da ta isa tana daga tsaye ta gaishe da Umma tana done hanci jin wani ƙauri-ƙauri na tashi, Umma ta harare ta tana dauke kaskon turaren wutar da ta kunna tana baɗe gidan da shi ta kai kitcken, dawowa ta yi ta zauna tana kaɗa ƙafa ya ce "Ke kuma lafiya kika shigo min gida kika tsaya min a ka kamar na ci miki bashi?" Kallon hadarin kaji Fatima ta yi wa Umma sai kuma ta kama ƙugu cikin tsiwa da rashin kunya ta ce "Wato na ƙara tabbatar da duk wani abu da kuke ƙullawa a gidan nan ke da Ammi, ku ne kuka shiga ku ka fita har kuka sa su Abba suka aura wa Baby mahaukaci ba su sani ba ko? To billahil lazi sai na sanar da Grandma cewa ku ne mugayen da ku ka yi makirci kuka haɗa komai da ya faru ke da Ammi. " Ta faɗa tana murguɗa baki cike da rashin kunya..

Ras! Ras! Ras! Haka gaban Umma ke bugawa ba ƙaƙƙautawa ta ruɗe sosai da jin maganar Fatima, sai kuma ta masge ta kirkiro murmushi ta yi wa fuskarta kwalliya da shi ta ce "Haba Autar Ammi, ke fa daɗina da ke rashin kunya wani lokacin, yanzu ban da ma sakarci irin naki taya za mu sa Abir ta auri mahaukaci bayan ba mu ba ne za mu ɗaura mata aure? Kuma ma ne ya kawo wannan maganar bayan kin san da kanta ta ce a haka take son shi? "

Kallon uku saura kwata ta aika mata sai kuma ta zauna akan kujera ta zayyano mata duk abin da aka yi a part ɗin Grandma da kuma nasu, zufa ce ta dinga karyo wa Umma ta haɗiye yawu ba shiri, ganin ba za ta yi magana ba Fatima ta ja tsaki ta mike tana faɗin "Ai nasan dama kune mugaye azzalumai, Wallahi tsaf sai na sanar da su Abba kai har su Yaya Abdul sai na sanar da su kune ummal aba'isar lalacewar komai na gidan nan." Ta ƙarashe maganar tana banko kofar palon da ƙarfi ta wuce abin ta ta koma part ɗinsu..

Umma ta rikice sosai sai zarya take a palon, ganin in ta zauna wankin hula zai kaita dare ne ya sa ta figi mayafinta ta dauki jaka da makullin mota ta fita a harzarce...

ABBA na fita ya nemi Abdul a waya, bayan sun gaisa yake tambayar Abdul ina ne gidan su Baba? Jim Abdul ya yi dan shi ma sai ɗazu yake tunanin in ya tashi daga aiki zai je, kwatance ya masa sannan suka yi sallama ya karya kan motarsa ya nufi Unguwar su Baba. Yana isa ya yi hon Maigadi ya zo ya buɗe masa ƙofa ya kutsa kan motarsa ciki, yana gama packing ya fito suka gaisa da Maigadi sannan yake tambayar sa ko masu gidan suna nan? E ya ce mata ya nemi ya yi masa izini da masu gidan, ya amsa da to ya nufi ciki. A zaune ya samu Baba da Inna tana yanka masa lemon zaƙi ya sanar da su wani hamshaƙi mai kuɗi ya zo ya ce yana so a masa izini, cike da mamaki Baba ya ce "To fa! Waye kuma haka? Amma dai je ka ce masa ya shigo."

To ya faÉ—a ya fita ya sanar da Abba abin da suka ce, godiya ya masa ya nufi ciki yana addu'ar da ya shiga ya fara cin karo da fuskar Abir, Sallama ya yi suka amsa masa Baba ya mike tsaye yana murmushi ya ce "A a sannu da zuwa Alhaji yau kai ne a gidan namu?"

Murmushi Abba ya yi yana wurga na mujiya ko zai ga ta inda za ta ɓullo, ruwa Inna ta kawo masa ya ɗan sha kaɗan dan kar Baba ya ce yaƙi cin abincin gidansu, bayan sun gaisa ne Abba ya yi shuru ya ma rasa ta ina zai fara yi wa Abba bayani, Baba da ya gane akwai abin da Abba ke son faɗa masa sai ya gyara zama tare da cewa "Alhaji lafiya dai ko?"

Girgiza kai Abba ya yi da kyar ya iya cewa "Baba ina Mamana? Na ga ba ta fito ba ko ba ta ji muryata ba ne."

Kallon rashin fahimta suka masa Inna ta ce "Wace ce kuma mai suna haka Alhaji?"

ÆŠago kai ya yi ya ce "Abir nake magana."

Shuru duk suka yi ba su ce masa komai ba, Abba ya ƙara shiga tashin hankali ganin fuskokinsu sun bayyana damuwa, a sanyaye ya ce "Malam ba ku ce komai ba ina take?"

Labarin guduwar ta cikin dare ya sanar masa, ya tashi ya dauko masa wasiƙar da ta rubuta musu da za ta bar gidan, Abba ya dafe kai yana faɗin "Inna lillahi wa inna laihin raji'un!" Daga haka bai iya cewa komai ba ya tashi ya tafi ko sallama bai musu, da kallo suka bi shi cike da mamakin wannan lamari na Abba Inna ta nisa ta ce "Gaskiya Malam akai abin da yake faruwa a gidan su Hauwa'u."

Baba ya yi shuru yana tunanin abubuwan da suka wuce, shi kansa tun da aka yi auren nan lamarin ke damun shi har ila yau da Abban ya zo neman ta, duk tsayin watannin nan ba su zo sun neme ta ba sai yanzu da su kan su ba su san a wata duniya suke ba? Girgiza kai ya yi ya tashi tare da yi wa Inna sallama ya ce ko ma meye za su sani.

Yau tun da wuri ta gama yi wa masu zuwa kitso wajan ta, wanka ta yi ganin ta samu tsarki ta gabatar da Sallar La'asar, fitowa ta yi ta zauna ana ta hira amma duk hankalinta baya kan hirar, tun safe take jin muguwar faduwar gaba haka ta daure dai ta yi wa wanda suka zo kitso cikin ƙarfin hali. Sai gaf da Magariba ta nufi ɗaki dan ta dauko kayan girki, turus ta tsaya ganin shi zaune dafe da kai ya jingina da bango, ƙarasowa ta yi ta iso gaban shi a ɗarare ta kai hannu ta taɓa kafaɗarsa, ɗagowa ya yi suka haɗe idanu ta yi saurin janye nata saboda da yadda ya mata kwarjini a idanun gani, a sanyaye ta ce "Zazzabin ne dai bai sake ka ba?".
Chapter 98 · 0% Book details