← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 120

Sashe 38

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sake da baki Suhal yake kallon Abir da ta soma fita daga haiyacinta, sunan da ya ji tana kiran sa da shi ya ba shi mamaki matuƙa, sai tambayar kansa yake waye kuma wani Zain? Ko kuwa gamo ta yi ne kafin ta shigo? Wayarsa da ta saɓule daga hannunsa ya ɗauka, numfashi ya fesar ya tsura mata idanu, tabbas ita ɗin kyakkyawa ce sosai, fuskarta da ta sha kwalliya yake kallo ba ko ƙiftawa, wani irin yanayi yake jin na fisgar shi game da ita. Ajiyar ya sauke tare janye idanunsa daga kallon da suke wa juna ita da shi, shi yana mata kallon ƙurulla ta masa kyau fiye ma da yadda ya gan ta photo, yayin da ita kuma take masa kallon ya ba ta amsar tambayar da ta masa amma ya yi shuru ya zuba mata na mujiya..

Gyara zama ya yi ya ce "My princess, wai waye Zain? Naji kina kira na da sunan shi dan gidan waye shi da har yake miki gizo?" Ya faɗa yana ɗan haɗe fuska, wani irin zafi ya ji da ta ce wai tana tsananin tunanin wani can da ban bayan shi ga shi a gaban ta da ya yo tattaki tun daga wata ƙasar ya zo dan ya gan ta eyes to eyes, dafe kai ya yi ya sake kallon ta..

Shuru ta yi tana kallon shi yana maganar, ta kasa yarda ba Zaiyan ba ne saboda shi ma Suhal yana da wushirya irin ta Zaiyan har sajan duk iri ɗaya ne. Ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ta sauke tana ɗan lumshe idanu, can dai ta buɗe su a kan shi nan dai ta ga bambancin da ke tsakanin shi da Zaiyan, shi yafi Zaiyan fari, sannan girarshi ta haɗe da ƴar'uwar ta saɓanin Zaiyan da tashi ba ta haɗe ba. Ji ta yi ta ɗan samu sassauci na ruɗewar da ta yi ta koma inda ta zauna a farko ta zauna, sai ta dafe kai ta saki ta kalle shi cikin wani irin yanayi ta soma magana.

"Am so sorry Yaya Suhal, Wallahi na ruÉ—e ne dayawa."

Saurin tarar numfashin ta ya yi, "Kin ruɗe kamar yaya My Princess? Ki faɗa min waye Zain?" Ya yi maganar yana ɓata fuska..

Ajiyar zuciya ta sauke ganin yadda ya ɓata rai sai ta ji ba daɗi, yana murna ya zo dan ya ganta ta ganshi sai tana kiran shi da wani sunan ai dole ma ranshi ya ba ci, a hankali ta ce "Zain wani majinyaci ne wanda muke kula da shi, kana matuƙar kama da shi sosai sai dai kai ka fishi fari shi kuma farin nasa na duhu ne, ka yi haƙuri ka ji Yayana, amma dai sai na ga kamar a photo ba ka yi kama da shi ba, a photon ka fi haka girma." Ta faɗa tana yi masa ƙayataccan murmushi mai sanyaya zuciya.

Shi ma murmushin ya yi ya kuma cika da mamakin wai yana kama da wajinyacin su, ai kuwa zai so ya ga wannan majinyaci dan ya ga yadda suke kama wanda har ya sa ta ruɗe da ta gan shi. Cikin nuna zallar farin ciki ya ce "Ƙanwata sarkin kuka da rigima, yo ai wancan ba ni ba ne Yayana ne, amma zan so na ga wannan bawan Allah mai kama da ni."

Riƙe baki ta yi tana tunano photonshi kwaya ɗaya tal wanda sai da ta yi masa fushi sati kana ya turo mata, ashe ma ba shi ba ne yayansa ne, harara ta aika masa ta ce " Amma ko kai kuwa Ya Suhal ka zama ɗan basaja, yanzu da yayan naka ka zo ai shi zan kalla ba kai ba." Ta karashe maganar tana murguɗa masa baki..

Kyakkyawan murmushi ya mata, ya ce "Ai dama na ce zan miki bazata, to wannan ita ce."

Murmushi ta yi ta miƙe ta isa gaban kayan abincin ta zuba masa lemo mai sanyi, a nutse ta miƙa masa tare da cewa "Yanzu dai bismillah ka sha wannan ka ci abinci, in yaso daga baya ma yi maganar." Amsa ya yi ya yi bismillah ya sha lemon. Abincin ta zuba masa farar shinkafa da wake da miya ta sha nama sai zuba ƙamshi take, ɗayar kular ta buɗe nan kuma dambu kuskus ne ya ji kayan kamshi shi ma yana tururi ta ɗago ta kalle shi tana ƴar dariya ganin yadda ya yi mata ƙuri da idanu ta ce "Ya Suhal wai wannan kallon fa? Ko ba haka ka yi tsammanin gani na ba? Ka ganni ƴar figigiya ko?" Ta ƙarashe maganar tana dariya.. murmishi mai sauti ya yi ya amshi cokalin da take miƙa masa ya ce "Tabbas ƙanwata na so na gan ki babba ki fini jiki ma."

Waro idanu ta yi tana rufe baki ta ce "Tamɗijam! Wai ni ɗin ce ka so ka ganni irin ƙatuwar nan?"

Gyaɗa mata kai ya yi dan ya fara cin abincin, turo baki ta yi tana hararar shi ba ta ce komai ba ganin ya soma cin abincin. Satar kallon shi take idan ya sunkuya kai zai ɗauki shinkafar in ya ɗago sai ta yi saurin janye idanuwanta kamar ba ita ba, shi kuwa yana kallon ta duk abin da take yi sai ya ji ta ƙara shiga ranshi yadda take turo bakin sai ya ji wani abu na fisgar shi ya lumshe idanu yana zaune tsokar naman da ya saka a baki, in ka kalle shi sai ka ɗauka daɗin abincin ne yake kai masa har kwanya yake lumshe idanu, shi ko ba wani daɗin girkin ba ne ya sa shi hakan yanayin da ya shiga ne ya sa ya lumshe idanu. Bayan ya gama ta ƙara zuba masa lemo tana sakin murmushi ta ce "Ya Suhal manya."

Hararar wasa ya mata yana goge bakinsa, gira ya É—age mata ya ce "To Princess ya gida ya su Mommy? Ina wajan Yaya Abdul?"

Rufe fuska ta yi tana ƴar dariya, ita fa daɗi take ji in yana ce mata princess, sauke hannun ta yi ta ce "Yaya yana nan lafiya an jima ma za ka ganshi dan ya kusa dawowa daga wajan aiki, kuma na ce masa in ka zo ya zo ku gaisa ya ce zai dawo da wuri, Mom kuma tana ciki." Ya ɗaga baki zai yi magana Iman da Hafsat suka shigo bakinsu ɗauke da sallama, amsa musu suka yi Suhal ya kame yana wani shan ƙamshi ganin yadda Hafsat ta ƙura masa idanu, zama suka yi Iman ta ce "Yaya Suhal barka da zuwa, ya gidan?" Ta faɗa cikin nutsuwa.

ÆŠan sakin fuska ya yi ya amsa mata gaisuwar, itama Hafsat ta gaishe shi tana sakar masa murmishi ya amsa ba yabo ba fallasa..

Sun jima suna jan shi da hira shi kuma yana bin su da E ko a a, kallon Abir ya yi da ta gama amsa waya ya ce "Princess ki min iso wajan su Mom mu gaisa ina son na tafi zan bi jirgin ƙarfe tara da rabi na tare." Ya yi maganar yana rufe hasken wayarshi..

Ɓata fuska ta yi ta ce "To Yaya ya ce ga shi nan zan shigo ya dawo, ka bari mana sai gobe ka tafi." Girgiza mata kai ya yi bai ce da ita komai ba, suna haka sai ga Abdul da Salim sun yi Sallama a palon suka amsa musu..

"To uwayen surutu kun zo kun sa baƙo a gaba kuna zuba masa zance, sai ku tashi ai ku fita." Salim ne ke maganar yana miƙa wa Suhal hannu suka yi musabaha. Iman ta yi masa kallon to sannu ubanmu ta kawar da kai, ita kuwa Hafsat Abdul ta kafe da idanu yana gaisawa da Suhal har sai da ya ɗago suka haɗa idanu ta yi saurin ƙasa da nata cikin jin kunyar ya kama ta tana kallon shi, ɗan ƙaramin tsaki ya ja wanda ba kowa ya ji ba sai Abir da ke zaune kujera ɗaya da shi, gyaɗa kai ta yi tana danne dariyar ta dan ta san da wa yake...

Shuru Abdul ya yi yana tunanin inda ya san wannan fuskar, sai can Zaiyan ya faɗo masa ya ɗago ya kalli Suhal da shi ma yanzu ya fahimci yana masa kallo irin wanda Abir ta masa, gane hakan ya sa ya yi murmushin gefen baki ya ce "Yaya Abdul Princess ta ce Wai ina matuƙar kama da wani majinyacin ku?" Ya faɗa dan ya ƙara tabbatar da abin da yake son sani..

Salim ya kalle shi yana ɗaga kai sama, can ya dube shi ya ce "Gaskiya dai bro kana kama da wata fuska da na taɓa gani, amma ban san a ina ba ne na kalli mai kama da kai."

Itama Iman haka ta faɗa Suhal ya ƙara cika da mamaki, ko dai mafarkin shi ne yake son tabbata? Girgiza kai ya yi ya ce "Zan so na ga wannan mutumin."

Sai da Abdul ya gama jin maganganun su sannan ya ce "E tabbas kana kama Zaiyan majinyacin mu wanda yake fama da matsalar ƙwaƙwalwa, da ba dan ka fishi haske ba da sai na ce kaine Zaiyan." Ya faɗa yana jinjina tsananin kamar da suke..

Suhal ya gyaÉ—a kai ya ce "Don Allah zan iya ganin ko da photon shi ne?"

Abir Abdul ya kalla ta buɗe wayarta ta, gallary ɗin wayar ta shiga ta nemo wanda suka yi a tare ta miƙa masa ya amsa. Hasken wayar ya ƙara ya kalli photon, dam! Ya ji gaban shi ya faɗi sakamakon yin arba da photon Zaiyan, tabbas in wani ya gan shi zai ce shi ne jikin wannan photon ya yi shigar mahaukata, na gaba ya janyo inda suka yi dariya shi da Abir, bai san ba lokacin da ya ce "Ikon Allah.! Hannu ya kai ya shafa fuskarsa yana kallon photon, ya jima yana kallon photunan sannan ya ci karo da video su, saurin buɗewa ya yi ya ga yana bin Abir ita kuma tana guduwa yana ce mata yunwa yake ji, ita kuma tana ce masa ba za ta ba shi ba.. Bayan ya gama gani ya miƙa mata wayar zuciyar shi cike da son ganin wannan mahaukaci mai kama da shi, a nutse ya ce "Don Allah zan iya ganin shi?"
Chapter 38 · 0% Book details