Sashe 118
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jinjina kai ta yi ta ce "Yaya Ibrahim ɗan'uwana ne, tun da na taso na mallaki hankalin kaina nake tsananin son shi shi ya sa ko a makaranta ba ni da aiki sai maganar sa duk da bai san ma ina yi ba, kwatsam rana ɗaya naji labarin an sa bikinsa da wata ba ni ba, a lokacin ina ƙasar waje ina karatu duk na kasa zama ina jiran lokacin biki ya yi na zo na ga wadda ta yi min Kwacan masoyi. Duk da haka ban haƙura ba na samu ƙawata da maganar ta ce na bari za ta je wajan wani malamin ta zai yi aiki a kan wadda zai aura. Lokacin biki na zo na ga matar Yaya Ibrahim kyakkyawar gaske ga shi duk dangi son ta suke, abin ya ƙona min rai na dinga bin malamai dan a fasa auren amma ina sai da aka yi, bayan aure naje wajan wani boka na sa a juye mata mahaifa kar ta haihu har abada ta nan ne Yaya Ibrahim zai ji ba zai zauna da juya ba ya sake ta sai a aura masa ni, da farko kamar na yi nasara sai ga shi suna cika shekara da aure ta samu ciki na tashi hankalin ƙawata muka koma wajan boka na ce masa asa duk cikin da za ta samu ya dinga zubewa. Wannan karon aiki ya ci dan duk cikin da ta samu zubewa yake amma duk da haka Yaya Ibrahim bai ji ya daina son ta ba sai ma ƙara kulawa da ita yake, ganin da gaske na rasa shi sai na dawo kan Kabir wanda shi kuma yake auren ƙanwata. A lokacin ba na shiga harkar kowa dan sai ayi abu a cikin family ban sani ba, saboda na haɗu da ƙawaye masu aji kamar ni sai na watsar da kowa na riƙe ƙawayena ko Hajiyata ba ta kula danginta iya mahaifin su Ibrahim kawai take iya zuwa gidansa in ana wani abin, shi ma a sosai ba dan ko auren Yaya Kabir ta ce min ba ta je, hakan ya sa da na tambayi Yaya Kabir Hajiya ta ce min matarsa ko ƙawar matar Yaya Ibrahim ce ko kanwarta ce, saboda ban tsaya naji maganar Hajiya da kyau ba na katse wayata. Shi kuwa Yaya Kabir sai ce min ya yi ƙawarta ce ba ƙanwata ba, hakan ya sa na ƙara jin tsanar Sadiya tun da cusa wa Kabir ƙawarta.
Haka zan zo na musu cin mutumci na zage su amma Sadiya da Hajara ba sa ramawa sai su barni na yi ta faɗa ni kadai, da Inna ta samu labari ta sa Yaya Kabir ya min iyaka da gidan hakan ya ƙara sa min tsanar su na tattara na koma England na ci gaba da karatu. Ina daga can nake sawa ayi min aiki a kan su har na ci nasarar kashe Hajara, ita kuma Sadiya a lokacin asirin da na mata ya karye ta ta haifi ɗiya mace, ban yi ƙasa a gwiwa ba na sa aka yi wa ƴar turan baƙaƙen aljanu ƙarshe aka sa mata cutar asma. Shi kan shi auren Yaya Kabir sai da haɗa da bin malamai tukun na shayo kansa ya yarda da aurena. Bayan auren na ci gaba da bibiyar Yaya Ibrahim ina neman shi da mu keɓe ba tare da mijina ya sani ba, ya min tas ya ci mutumcina abin ya ƙara fusata ni, naje gida muna hira da Yaya Sadisu sai yake ta faɗa yana cewa shi fa Yaya Ibrahim ya sa masa ido ba dama ya ɗauki wani abu sai ya tambayi dalili in da zai samu dama shi fa zai kawar da shi ma bakiɗaya ya amshe matsayinsa na MD ɗin companynsa na motoci. Bayan ya gama min bayani sai na ce masa me zai hana mu yi masa barazana mu ɗauke ƴarsa mu ce za mu kashe ta in bai yi abin da muka ce ba, hakan ya yi wa Yaya Sadisu daɗi ya tafi gidansa ni ma na tafi nawa, na dinga neman ta hanyar da za mu sace Abir duk in da na bi sai na ga hanyar ba mai ɓullewa ba ce sai na fasa, ana haka sai Yaya Sadisu ya ya je wajan wani boka ya masa aiki a kan Inna, washe gari ya je har cikin ɗakinta ya kanannaɗe ta da daɗin baki ya ce ta sa Yaya Ibrahim ya ba shi kuɗi masu yawa zai ƙulla kasuwanci da wani company a can England zai koma can da zama shi da matarsa, ya jeru mata ƙarairayi har sai da ta kira Yaya Ibrahim ta ba shi umarnin ya ba shi kuɗi masu kauri, duk da ba ya so haka ya ɗauko million 30 ya ba shi amma ya ce shi wannan ba zai ishe shi yin abin da yake so ba shi da zai yi kasuwanci da turawa, hakan ya sa Inna ta ƙara tursasa shi ya ƙara masa wata milion 20 ya haɗa ya yi hamsin.. Yana ta kasuwanci na a can England ashe sun haɗe baki da aminin Yaya Ibrahim suka nemo wasu matasa biyu da suke musu leƙen asiri a company Yaya Ibrahim, duk abin da yake wakana a company sai sun sani suna ta ƙoƙarin ganin sun durƙusar da cigaban da Yaya Ibrahim yake samu. Kwatsam wata rana suna tattaunawa a kan yadda za su amshi tayin wata ƙungiya da suke son a ke yo musu safarar ƙananan 'yan mata zuwa ƙasashe daban-daban, in da Yaya Sadisu ya ce zai sa a haɗa da Abir har ma mahaifiyarta in ta kama sai sun yi safarar ta ashe wani ɗan jarida na ɗaukan su, ba su ankare da shi ba har sai da suka gama magana za su fito Jarmai ya ga kamar gilmawar wani abu sai suka fito waje, ɗan jarida na ganin sun gan shi sai ya dinga gudu suka sa aka biyo shi amma sai ya samu ya tsere musu ya ɓuya. Wannan ɗan jarida ya yi ta zuwa Office ɗin Yaya Ibrahim amma masu tsoron wajan suka hana shi shiga, da kyar suka bari ya shiga yana ta musu magiya ya samu aka bar shi ya ga Yaya Ibrahim sai ya ba shi wannan ɗauka da ya yi ya kuma masa bayani cewar suna da gida a bayan gari wanda a gidan akwai gidan ƙasa a nan suke zuba yaran da suka sa aka dauko musu. Sosai Yaya Ibrahim ya girgiza da jin abin da ya faɗa ya masa godiya tare da yi masa kyauta mai tsoka ya adana wannan ɗauka, su Alhaji Mustapha suna neman wannan ɗan jarida amma sun kasa gane kamanninsa hakan ya sa suka tsorata kar ya je ya tona musu asiri, suna haka sai ɗaya daga cikin masu musu leƙen asiri a companyn Yaya Ibrahim ya faɗa musu ai ya zo ya ba da wannan ɗauka, nan da nan suka sa aka nemo shi aka kaishi wani ɗaki a gidan da suke kai mata ake gana masa azaba ƙarshe suka kashe shi. Ranar da muka ci nasara a kan Yaya Ibrahim shi ma da taimakon wani direbansa ya sanar da mu ya tafi gidan gonarsa in da ake kiwon kaji, a nan muka same shi.. Nan ta sanar da su duk abin da suka yi wa Abie har suka kashe shi tare da Maganer shi.." Ta ɗago fuskarta ta yi faca-faca da hawaye da majina ta ɗora da cewa "Su Alhaji Mustapha sun je har gida sun sharara wa su Yaya Sulaiman ƙaryar ana bin Yaya Ibrahim kuɗi har naira milion 50 aka ɗauka aka ba su. Suka kuma samun wata hanya da suke karɓar kuɗi daga hannun matasa 20 da ya buɗe wa shaguna a kasuwa na sayar da atamfofi, ya zuba musu kaya suke sayarwa ya ce musu shi iya uwar kuɗi yake so riba in sun samu su kula da rayuwarsu, sai suka zagaye suka ce ai shi ya ce riba ake raba ta gida uku su su ɗauki ɗaya su kawo kaso biyu, ba su musa ba dan a lokacin ganin Yaya Ibrahim wahala yake musu kuma sun san abokansa ne.. Yanzu haka maganar da nake muku sun tara yara sun fi talatin a wannan gida, wasu su suke lalata da su wasu kuma su fitar da su kasashen waje. Sai ku ji ana ta cewa an sace yara mata masu akasarin su su suke sace su duk suna nan a wajan su, wasu ma sun mutu saboda faɗen da suke musu su rasu, wasu kuma sun kai su ƙasar waje an juyar musu da tunani babu abin da suke sai yin zina da turawa suna biyan su maƙudan kuɗaɗe duk wata kuɗin yaran sai ya shigo account ɗin Yaya Sadisu daga ƙasar waje. Wannan yaron ma mai suna Damisa su suka sa mota ta kaɗe shi dan ya gano sirrin su, da suka ga bai mutu ba shi ne suka sa aka haukatar da shi, su yanzu haka ba su taɓa sanin kamannin Damisa ba duk abin da aka aiwatar ta ɓangaren Damisa ta hannuna ya biyo, na ga fuskar Damisa sau ɗaya shi ma sai da na sha wahala kafin na samu ganin shi lokacin an sallamo shi daga asibiti. Tun ganin farko da na yi wa Zaiyan lokacin da Abir ta kawo shi gidanmu na gane shi ne Damisa, amma kuma ganin a haukace yake sai na rabu da shi na ci gaba da harkokina, ko lokacin da suka ce Damisa ya yo musu saƙo na ce ba Damisa ba ne har yau a haukace yake amma suka ƙi yarda da maganata, ƙarshe ma nasa ita Abir ɗin ta aure shi suka bar garin.." Ta kalli barrister Huzaifa tana share hawaye ta ce "Wannan shi ne abin da ya faru wanda na sani ban rage ko ɗaya daga cikin abin da na sani da wanda na aikata da hannuna ba.." Ta fashe da kuka tana faɗin "Ina rokon Abir da ta yafe min lefin da na aikata a gare ta da duk wanda na zalinta."