← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 120

Sashe 48

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da wani irin mugun saurin Suhal da Abdul suka iso gaban ta kowa so yake ya taɓa ta, saurin ɗago da ita Abdul ya yi ganin Suhal na ƙoƙarin taɓa ta ya ɗaure fuska ya miƙe da ita cak ya dawo inda yake ya zauna. Ganin an ɗauko ta Zaiyan shi ma ya miƙe ya isa gaban Abdul yana kuka wiwi kamar ƙaramin yaro ya ce "Anty waye ya dake ki na rama miki? Ki tashi ki rakani mu tafi gidana sai mu yi zaman mu a can tun da su wanɗannan dukan ki suke, kuma in na yi kuɗi ba zan taimaka musu ba sai na kama su da kaina na kulle su a ɗaki." Zaman dirshan ya yi ya kamo hannunta da yake reto ya kalli zoben da ke yatsar ta tsakiya, baki ya riƙe yana juya hannun ya ce " lalala! Me ya sa kika sa wannan abin? Ki ga fa ya ɗaure miki yatsa bari na fitar miki da shi. " Idanu Abdul ya zuba masa yana kallon shi cikin taussayawa, ganin yana ƙoƙarin zare mata zoben ya kai hannu ya riƙe nasa ya ce "kana son Anty ta daina kula ka?"

Da sauri ya ɗago yana girgiza kai ya ce "Ka ba ta haƙuri Baba ba zan sake yi mata lefi ba, ka tashe ta na ce ta yi haƙuri." Ya rufe fuska yana kuka kamar an masa wani abin. Ajiyar zuciya ya sauke yana jin wani iri, Inna ce ta ƙaraso da ruwa da ta tafi ɗaukowa daga kitchen ta miƙa masa, amsa ya yi ya kurɓa ya fesa mata a fuska. Da sauri Zaiyan ya kalli Abdul ya sake fashewa da kuka yana faɗin "Baba me ya sa ka kashe Anty? Sai na rama mata abin da ka mata da ta farko daga mutuwa za mu tafi mu bar ku tun da ka kashe ta."

Hawaye ne ya cika wa Baba idanu bai san lokacin da ya gangaro ba sai da ji ɗumin su a kuncinsa, hannu ya sa ya goge yana jin tsananin tausayin Zaiyan na ratsa masa kowacce kafa ta jikinshi. Numfashi ta ja da ƙarfi ta soma buɗe idanu wanda tun kafin ma ta buɗe hawaye ke ta silalowa, tana gama buɗewa ta sauke kallon ta a kan Zaiyan da hawaye suka wanke masa fuska yana ta murtsa yatsunsa, da sauri ta tashi daga jikin Abdul ta sauka ƙasa ta zauna a kusa da shi duk bai san ta tashi ba. "Zaiyan." Jin ta kira sunan shi ya ɗago da sauri ya ga ita ce, ɗan waro idanu ya yi ganin ta a kusa da shi ya ce "Allah sarki Anty ashe kema dukan ki suke kamar ni, wannan mai min allurar har da nuna min irin wannan abar irin tawa da kika sayo min.Tun da ma haka ne tashi na kaiki gidana kin ga babu wanda yake son mu sai Inna, idan na kaiki sai ki goya ni muna zuwa yawo ko?"

Sake da baki take kallon shi, wato yanzu kamar an buɗe masa baki a yau ɗin nan sai surutu yake zuba mata ba kamar baya ba da in 'yan maganar ba su zo ba sai ya kwana bai ce komai ba, dogon numfashi ta ja tana gyaɗa kai ta ɗago ta kalle su wanda suma ita suke kallo. Girgiza kai ta yi ta ce "Ka gani ko Yaya? Na faɗa maka babu wani magani da suke yi masa sai ma cutar da shi da suke, yanzu a yanayinsa babu abin da ya ragu sai ma ƙaruwa da ya yi. Dama can dan ba ka nemi shawara ta da ba zan bari ka kaishi wannan Asibitin ba. Zaiyan kawo hannunka na gani. "

Maƙale kafaɗa ya yi yana turo baki ya ce "Dan ki yi min wayo ne ki gudu ko? To ba zan yarda ba ki soka min wannan abin mai tsini." Sake rushewa ya yi da kuka ya ƙara matsowa kusa da ita abin da ya ƙara tayar mata da hankali, Zaiyan bai fiya yin kuka ba ko da kuwa ta ce ta daina kula shi sai dai ya ba ta haƙuri saɓanin yau da tun da suka dawo ta ga ya canja sosai daga surutu sai kuka. Hannu ta kai ta goge masa hawayen tana girgiza masa kai cikin wani kalar yanayi ta ce "Babu abin da zan yi maka ka ji, mu ga hannunka sai na sayo maka kaya masu kyau irin na 'yan gayu." Ta Yi maganar tare da goge hawayen da suka zubo mata. Miƙe ƙafa ya yi yana haɗe hannayensa ya miƙa mata duka tare da cewa "Imm Anty dayawa fa nake so kayan." To ta ce masa ta kama hannun tana zubawa, ɗago kai ta yi ta kalli Suhal ta ce "Ya Suhal tabbas mafarkina ya zama gaskiya, wannan Asibitin ba magani suke yi wa Zaiyan ba jinin jikinsa suke ɗauka suna yin wani abin da shi, kalli nan ka ga inda suke daukan jinin." Ta faɗa tana nuna masa tsintsiyar hannunsa, ta ƙara da cewa "Tabbas akwai abin da yake faruwa da Zaiyan a ɓoye ba tare da kowa ya sani ba, ko ma meye wannan likitan da ke duba shi yasan komai game da ɗaukan jinin. Wata rana na taɓa ganin ƙuraje a daidai inda wannan ɗan ƙurjin yake, in ka tuna Yaya a Asibitin Yaya Hashim na nuna muku ya ce ba wata matsala ba ce babba za a iya sa masa magani ya warke, daga haka ban sake bi ta kan ƙurajen ba ganin sun yi baƙi alamar sun warke." Kanta ne ta ji ya sara mata ta dafe kan tana runtse idanu kamar daga sama ta ji ana mata magana a cikin kunnuwanta.

_Maijidda lalle ya zame miki dole ki sa idanu akan shi, in ba haka ba wata rana sai dai ku samu gawar Zaiyan an gama shanye masa jini, ki yi abin da ya dace kafin ki shiga gagarumar matsala wadda zai miki wahalar fita."_

ÆŠaga kai ta yi sama ta buÉ—e idanunta sai ta ji kan ya daina mata ciwo, ajiyar zuciya ta sauke ta kalle su tana gyaÉ—a kai tabbas zargin da take zai iya zamowa gaskiya, kamar dai yadda ta ji an sanar da ita mafi rinjaye na zuciyarta ya karkata a kan maganar da ta ji ta zo mata kamar wadda aka yi wa wahayi.

Suhal ya ce "Princess ba za mu iya tabbatarwa da maganar ki ba har sai na bincika na gani, sannan yana da kyau kai Abdul da za ka kai shi Asibitin nan ka yi bincike akan ta sosai, tabbas a cikin Asibitin nan akwai maciya amanar Asibitin kamar dai ɗaya daga cikin su da ya zubar wa da Sajida ciki. Ya kamata ka bincika wannan likitan. " Gyaɗa kai Abdul yake yana nazarin maganganun su, tabbas ya yi gangancin yanke hukuncin kai Zaiyan Asibitin nan, wanda bai nemi shawarar kowa ba sai ta abokin shi wanda a take yake sanar da shi sam kar ya kai Zaiyan wannan Asibitin ya bari in ya gama shan magani in ba a ga alamar sauki ba sai su fitar da shi waje, amma saboda gardama irin ta Abdul ya ƙi jin shawarar da ya ba shi ya ɗauke shi ya kai, yanzu ga shi matsala ta soma biyowa baya. Dogon numfashi ya sauke ya miƙe tsaye ya yi taku biyu tare goya hanayensa baya yana ta nazari, sai zuwa can ya juyo ya kalli Suhal da ya kafe shi da idanu yana jiran jin me za faɗa, cikin nutsatsiyar murya irin ta cikakkun maza ya soma magana.

"Dole zan koma Asibitin nan dan na nemi wannan likitan na masa tambayoyi, amma kafin nan ka duba mana shi mu gani ya jininsa yake."

Shi ma tashi ya yi ya kalli Sajida sannan ya dawo da kallon shi ga Abdul ya ce "Sai na koma masauki na kayan aikin suna can, minti ashirin zan dawo ko kuma a bari ma zuwa gobe sai na zo da safe na duba shi, in ma da buƙatar wasu abubuwan za ka iya yi wa abokin ka waya ya kawo mana sai mu yi aikin."

Gyaɗa masa kai ya yi ya dawo kusan Sajida ya ce "Ke kuma tashi muje yau nake son na kaiki Kano gidan su Mama su ganki, idan na shirya zan koma sai mu tafi tare. Amma kafin nan zan sake duba lafiyarki sai na kaiki." Ya faɗa yana miƙar da ita. Tana cije lips ta miƙe har yanzu ciwo mararta take sosai dauriya kawai take dan kar ta tayar wa da Suhal hankali, numfashi ta dinga saukewa zufa ta dinga yanko mata. Kallon ta ya yi da kyau yana jera mata sannu, da kyar take taka ƙafar ya musu sallama suka nufi kofar fita sai jin murya Zaiyan suka yi yana yi wa Suhal magana.

"Abokina kaima Baba ne ya haife ka? Za ka zama Abokina?"

Juyowa ya yi yana murmushi ya kalli Zaiyan da yake ci gaba da jaddada masa ya yarda su zama abokai, gyara tsayuwa ya yi ya ce "E na yarda mu zama abokai."

Miƙewa ta yi zumbur ya isa gaban Suhal ya zagaye su yana dariya, sai da ya zagaya su sau uku sannan ya dakata yana dariya ya miƙa masa hannu ya ce. "A ƙulla abokai zan ke zuwa gidanka." Murmushi Suhal ya yi ya miƙa masa hannu suka ƙulla sannan ya kalli Sajida da ya ga tana kallon shi kamar wadda take masa harara, riƙe haɓa ya yi tare da taɓe baki ya ce "Dalla can malama ke kuma meye kike wani harara ta? Haushi kike ji dan ban ƙulla abuta da ke ba? To ni sarki ne wannan shi ne Abokina ba ke ba ƴar ƙarama." Tsoro ne ya kama Sajida ganin yadda yake hura hanci, ta maƙale hannun Suhal ta ce "Don Allah mu tafi Suhal tsaro nake ji kar ya bigeni." Ganin ta ruɗe ya sa Suhal sake yi musu sallama suka fita Zaiyan na ce masa ya dawo fa an jima yana dariya ya amsa da to zai dawo sannan ya rufo ƙofar..
Chapter 48 · 0% Book details