← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 120

Sashe 52

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

To Suhal ya ce ya fita harabar gidan inda a nan suka hadu da Abdul da Abir sun iso gidan. Gaisawa suka yi sannan Suhal ya ce Sajida ta shiga mota, sai da ta iso kusan Abir ta ce "Abokiyar zama za mu wuce gida sai Allah ya kawo mana ke Niamey, na gode kwarai da kulawa Allah ya bar zumunci."

Murmushi ta yi ta dafa Sajida ta ce "Kar ki wani damu Æ´ar'uwata ko gaishe da gida."

To ta ce tana shiga mota.

Suhal da Abdul suka koma gefe suka yi magana wadda ba wanda ya san me suka faÉ—a, bayan sun gama ya ce wa Abdul yana so zai yi magana da Abir ya ce masa ba komai ya shige mota yana jiran ta.

Kallon ta ya yi ya ce " My Princess zan tafi ƙi kula min da kanki, ku kuma yi tunani na sosai kafin na isa gida na kira ki a waya."

GyaÉ—a masa kai ta yo saboda wata irin kunyarsa take ji ta mamaye ta, sai da ya sake magana sannan ta ce "To Ya Suhal a sauka lafiya Allah ya kiyaye hanya Mom da Grandma sun ce na gaishe da kai suna ma fatan alkhairi. Na gode sosai da karamci Ya Suhal?"

Murmushi ya yi ya ce "Ba komai ni ma ki ce ina gaishe su sosai, mu za mu wuce ki kula da Zaiyan da kyau."

Daga haka suka wuce, sai da suka ga tafiyar su kana suma suka tashi motar su, har Abdul ya ce su shiga Abir ta hana dole ya fasa suka tafi gida...

Sai da suka zo kofar gida ya yi ya kalle ta da wani kalar yanayi ya ce "Ki je gida tun da kin ce yau ba ki da school."

Raurau ta yi da idanu ganin yanayin sa, gabaÉ—aya ta kasa gane kan Yayan nata sai wasu irin halaye yake tsiro mata wanda ta kasa gane su, ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Yaya wai wani lefi na yi maka kake min irin wannan hukuncin? Why Yaya?"

Shuru y yi bai ce mata komai ba zuciyarsa sai tafasa take, wato ma b ta san b abin da ta mi shi? Kawar kai ya yi yana jiran ta fita, ganin ta É—ago za ta sake masa magana ya janyo ta ya rungume yana bubbuga bayan ta, so yake ya ja da baya da ita ko zai samu sassauci in auren ta ya zo, amma ita kullum sai kuka tana ce masa me ta masa ya daina kula da ita..

Sai da ya ji ta daina kukan ya sake ta ya haɗiye wani kakkauran yawu mai daci, ya sanyaye ya ce "Ki je gida in na dawo daga office zan same ƙi mu yi magana."

Jin haka ya sa ta tashi ta dauki Jakarta ta wuce, sai da ya ga ta shige sannan ya karya kan motarsa ya nufi Office..

Da dare ta yi ta jiran zuwan shi amma shuru, hakan ya sa ta kusan kwana tana kuka da tunani har sai da ta ji kanta n neman rabewa gida biyu ta haƙura ta kwanta..

Washegari ma haka ta yi dakon zuwan sa amma bai zo ba ta yi ta damuwa har Mom ta tambaye ta me ke damun ta ta ce ba komai...

Kwankwasa kofar ake ba ƙaƙƙautawa Grandma da k zaune ta kwala wa Laraba kira ta fito a guje, kofar ta nuna mata ta buɗe sai ta ga Abdul ne jikin shi duk jin, ai da sauri ta ja da baya tana dafe ƙirji ta ce "Yaya Abdul me ye a jikin kayanka?"

Duk da ba shiri suke ba amma yau sai ya ji ba zai iya hantarar ta ba, dogon numfashi ya ja sannan ya ce "Baby tana nan?"

"E ba su jima da dawowa daga makaranta ba ita da su Hafsat.". Bai sake cewa komai ba ya iso ga grandma da ke riƙe da baki tana bin shi da kallo har ya durƙusa ƙas, a ruɗe ta ce "Abdullahi me ya faru da kai na ga jini a jikin ka?"

"Riƙe kai ya yi da kyar ya ce "Grandma Mom ce mota ta buge ta, yanzu haka tana Asibiti b ta san wa yake kanta ba." Ya karashe maganar wasu zazzafan hawaye na zubo masa..

"Inna lillahi wa inna laihin raji'un!" Suka ji an furta daga bayan su, da sauri suka juyo suka ga Abir ta daura hannu a ka da Hafsat da Iman. Saurin isowa suka yi tana kuka ta ce "Yaya don Allah ka kai ni na ga Mommyna."

Miƙewa y yi ya kama hannunta Grandma ta tashi ta yafa mayafinta suka ɗunguma zuwa harabar gidan, Laraba ma ta wato hijabinta ta sa ta bi bayan su tana kuka..

Sun zoza su shiga sai ga Ammi ta fito cikin shirin fita, ganin su ya sa ta dakata da shiga motar ta yo wajan ta ce "Inna lafiya dai na gan ku wasu na kuka?".

"kayya ! Ina fa lafiya Farida wai Sa'ade ce mota ta bige ta yanzu hka ba ta san wa yake kan ta ba."

Dikira Ammi ta dauka ta ce "Ai kuwa bari na fasa fitar nan muje Asibitin, ke Hafsat da Iman ku zo motata."

Motar suka shiga cikin azama suka nufi Asibiti...

_Taku har kullum Maman Nusaiba ce_

[10/30, 1:27 Safiya] Anty Sarat (Mom Nusy 🌹): ~A HAKA NAKE SON SHI~

+966577675904

Shafi na (26)

Gudu sosai Abdul yake hankalinshi a matuƙar tashe, yadda ya bar Mommy yake ta tunawa sai zufa yake sharcewa yana fesar da zazzafar iska daga bakinsa. Abir kuwa ciwon ta ne ya tashi saboda hayaƙin da ta shaƙa da danger ta tsayar da su ta leƙo kai da kai dan ta ji iska wani mai mashine ya baɗe wajan da hayaƙi, hakan ya sa ta mayar da kanta da saurin gudun kar ta shaƙa, amma Inna har ta shaƙa nan-da-nan ta dinga tari tana laliben jakarta ta tuna ko wayarta ba ta dauƙo ba saboda kiɗimewa da ta yi.. Jin tarin nata ya yi yawa ne Abdul ya ɗan juyo ya ga tana dafe ƙirji, da sauri ya kalli Grandma ya ce "Grandma ɗaga nan please ki ɗauko wa Baby maganin ta ciwon ya tashi." Ya faɗa yana nuna mata lokar da ke gefen hannunta.

Da sauri Grandma ta buɗe hannu na rawa ta fito da shi, zuwa lokacin har ta soma fita daga haiycinta ta juyo ta janyo hannunta ta kafa mata maganin a baki, sai da ta danna ta shaƙa sau uku kafin ta ji ta dawo daidai..

Suna isowa duk suka fito suka nufi ciki da sauri yana riƙe da hannun Abir, emergency room suka nufa gaf da wani ɗaki wanda in har aka shiga da mutum to fa lalle hatsarin da ya yi ko cutar da ke damunsa ta mugun tsananta. Kuka ta dinga yi tana addu'ar Allah ya fito mata da Mommynta, ganin tsayuwar ta yi yawa ne suka koma kan kujerun da ke gefe suka zauna suna jiran fitowar likitocin..

Sun fi awa biyu suka suna zaune har Ammi ta fara ƙosawa saboda kiran da ake mata a waya sai aka buɗe ƙofar, da sauri duk suka tashi suka yi kan doctor suna tambayar shi ya jikin Mom?

Buɗe baki Abdul ya yi zai yi magana ya ga an turo gadon da aka ɗauki Mom da shi, dam! Gaban shi ya faɗi ya ƙura wa gadon idanu, ganin za su wuce Abir ta kalli Doctor Hashim cikin kuka ta ce "Yaya Hashim ina Mom ɗi na?"

Girgiza mata kai ya yi sannan ya ce "Gaskiya jikin nata ya tsanan ta amma ta ce tana son ganin Abdul da ke."

Da sauri ta damƙi hannun Abdul tana kuka ta ja shi suka nufi ciki, a kwance suka gan ta an sa mata ƙarin jini ɗayan hannun kuma ruwa ne aka jona mata, na'urar da ke nuna yadda numfashinta ke tafiya Abdul ya kalla ya ga tana tafiya ahankali-ahankali. Lumshe idanu ya yi yana jin gaban shi na ƙara tsananta bugawa, hannu ta miƙa musu ganin haka ya sa Abir ta rushe da kuka ta isa kusa da ita ta kwanta kanta a cikin Mom tana rera kuka mai tsuma zuciya. Da ƙyar Mom ta ɗaura hannunta a kan Abir cikin wata kalar murya mai karyar da zuciyar mai karatu ta ɗago da idanuwanta ta kalli Abdul ta ce "Yarona zo nan."

Zama ya yi a ɗayar kujerar ya kama hannunta wanda ta ɗaura akan Abir ya janye ya riƙe cike da rauni yake kallon Mom, ba zai kwatanta tashin hankalin da yake ciki ba na ganin wadda ta kasance Yayar uwa a gareshi kuma gurbin uwar da ta haife shi a wannan halin, lumshe idanu Mom ta yi ta sauke ajiyar zuciya tana fitar da numfashi a hankali ta soma magana..

"Abdul ga ƙanwar ka nan ka kula da ita, ka maye mata gurbin uwa, uba ɗan'uwa, ka zame mata bango abin jingina da za ta raɓa ta ji daɗi. Abdul ka da ka bari Abir ta zubar da hawayen maraicin uwa da uba, ka kula min da ita ka ɗaura ta akan hanya mai kyau kar ka bari ta tara ƙawayen banza wanda za su ɓata mata tarbiya."

Hawaye ne ke bin kuncin Abdul duk dauriyar shi ji ya yi ya kasa, kai ya jinjina wa Mom ya ce "Mom ki daina irin wannan maganar in sha Allah za ki tashi, kuma dama Baby ai tawa ce ko kina raye nine zan kula da komai na rayuwarta har ƙarshen tawa rayuwar.."

Murmushi mai ciwo Mom ta yi ta nisa ta ce "A kullum kana tambaya ta shin ina dangina suke? To yau zan sanar da kai asalin mu ni da Æ´ar'uwata marigayiya, har da tarihin Maitama family duk zan sanar da kai in Allah ya ba ni damar faÉ—a ma duka."

Gyaɗa kai ya yi yana goge hawaye, ya ɗauki shekaru sama a ashirin yana tambayar Mom ina ahalinta suke? A wata ƙasa suke? Ko daga ita sai mahaifiyarsa kawai ba su da kowa? Har Baba Malam ya je ya tambaya amma ya ce bai san komai ba, kallon Mom ya yi ya ce "Mom ina jin ki ko na ce muna jin ki."
Chapter 52 · 0% Book details