Sashe 16
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shuru ta yi tana goge hawaye ta kira Lanara ta ce ta ƙaro ruwa, da hanzari Laraba ta kawo ruwan Mom da miƙa wa Abir ta ce " Ƙara shan ruwan nan ko kin ji sanyin zuciyarki." A sanyaye ta kalli Mommy ganin yadda take zubar da hawaye, abin da ba ta taɓa gani ba hawayen Mommy sai yau, ita kanta ta gaji da abubuwan Familyn nasu, amsar ruwan ta yi ta shanye tas sannan ta miƙa mata cop ɗin tana fesar da numfashi mai zafi daga bakinta, sannan ta ce "Mommy zan je ki sa a kaini sai mu tafi da Yaya Salim tun da shi ba ya nan, nasan yanzu haka Baba na can yana jira na." Ta faɗa tana yin fuskar tausayi burin ta bai wuce ta je ta yi tozali da shi ba ya yi ta mata tambayar shirme tana ba shi amsa.
"Wallahi Baby ba kya jin magana, yanzu ki tashi daga sumar ki kuma ce za ki je Unguwa sai ka ce ba ki san ba ciwon rayuwarki? Sai ki kira shi ki ce masa sai gobe ko jibi za ki je." Salim ya faÉ—a yana haÉ—e fuska.
Cuno baki ta yi tana tuno da Zaiyan yadda yake mata Shagwaɓa yana kiran sunanta da Anty sai ta saki murmushi, kallon Salim ta yi ta ce "Yaya Salim alƙawari fa na yi yau zan je, ka ga bai kamata na karya ba tun da dai na ji sauƙi."
"To ai sai ki tashi ki tafi ko uwar kafiyar tsiya, tun da Yaya Abdul ba ya nan ki bari ya dawo mana sai ku tafi gobe in Allah ya kaimu." Ya faÉ—a yana hararar ta.
Ita ma hararar ta aika masa tana kumbura baki ta ce "To ka manta gobe Monday akwai Makaranta?"
Banza ya mata bai ce da ita komai, Mommy ta kira Abba ta ce masa lalle yau tana son ayi zama idan sun dawo daga aiki, cike da mamaki Abba ya ce mata to yana tunanin dalilin da zai sa Mommy ta bukaci ayi zama..
Firr Mommy ta ce Abir ba inda za ta je ta zauna sai Abdul ya dawo, ita kuma ta dinga kukan an hana taje sai faɗi take "Mommy alƙawari fa na yi, kin ga kyan alƙawari cikawa please ki ce Yaya Salim ya kaini." So take kawai ta buɗa idanunta ta yi tozali da shi amma Mom da Salim sun ce sam ba inda za ta je..
Ƙarfe 5:pm daidai na Yamma su Abba suka dawo daga kasuwa, burinsa bai wuce ya ji me Mommy take son faɗa, ya yi sauri ya watsa ruwa ko abinci bai ci ba ya fito daga ɗakin shi inda ya samu Fatima da Yasmin suna rigima, kallon su ya yi ya girgiza kai sannan ya yi gyaran murya suka tsaya kowacce ta runkuyar da kai. "Shashahun banza da girmanku da komai kuke rigima sai ka ce yara ƙanana."
Fatima ta ce "Abba wai dole sai ta saka min abayata da takalmi da jaka, dan ɓakin ciki ba za ta sa nata kayan ba sai nawa da suka matse mata jiki."
Saurin kai mata duka Yasmin ta yi tana harararta jin abin da ta faɗa ta ce "Wallahi Abba ƙarya take yi ba wani kayanta da na saka, ta nemi tata ta rasa shi ne ta ce wai wannan ce abayarta."
Za ta yi magana Abba ya É—aga hannu hakan yasa ta ja bakinta ta yi shuru.
"Ki kira Mamanku ku ce ta same ni a part É—in matar Yaya har ku gabaÉ—aya." Yana faÉ—in haka ya wuce daga palon.
Fatima ta shiga ta samu Ammi tana waya sai dariya take ganin Fatima yasa Ammi saurin cewa "Zan kira in an jima."
A fusace ta kalli Fatima ta ce "Ke wacce irin shashashar yarinya ce Fatima? Ya za ki shigo min É—aki ba izini?"
Murguɗa baki Fatima ta yi tana harare-harare tare yin ƙasa da murya ta ce "Yo izinin me zan nema in zan shigo? Ai nasan da wa kike wayar."
"Me kika ce Fatima?" Ammi ta faÉ—a a fusace.
Saurin girgiza kai ta yi ta ce "Ni babu abin da na ce Abba ya ce mu same shi a part É—in Mommy."
Wani dogon tsaki ta ja "Tsuwwww! Su kullum ayi ta tara mutane kamar wani abin arzƙi za a yi , sai ki juya muje gani nan." Ta faɗa tana faɗa wa toilet, ita kuwa Fatima ta juya ta fita..
5:30pm kowa ya hallara a palon har Grandma da ba ta fi minti 15 da dawowa daga ganin likita ba ita ma ta hakimce tana kaɗa ƙafa sai bin kowa take da kallon tara saura uku.. Abba ya dubi Mommy ya ce "Matar Yaya me ya faru kika kira taron gaggawa?" Sai da ta yi kwafa tana kallon Umma da ta yi kicin-kicin da fuska ta ce "Kabir ka shiga tsaknina da wannan katafilar matar taka, idan kuma ba haka ba zan aje duk wani ganin girma da ƙimarka da nake na maka ta a kotu a bi min haƙƙina da 'yata."
Dafe ƙirji Umma ta yi tana kallon Mommy a masifance ta ce "Kan uban can! Sadiya wai saboda ni aka yi wannan taron? Me na miki da kike son zubar min da girma na a gaban yara?" Ta faɗa kamar za ta kai mata duba.
"Kin fi ɗan takon kano sanin hanyar tasha! Ki fita harkar 'yata da ɗan'uwanta tun da dai ai ba ke kika haife shi ba ballantana ki ce in ya sake shiga lamarin ta za ki tsine masa, ke ba ki isa ki raba Abdul da Abir ba dan ba ki da haɗi da shi iyakacinki ke matar Babansa ce ba uwarsa ba." Mommy ita ma ta faɗa a zafafe yau ji take duk abin da aka mata ya zo ƙarshe, kuma ta daina ɗauke kai a lamuran gidan.
"Lalle Sadiya kin ci kin sha kin tada kai dole ki faɗa min wannan maganar, yau ni kike yi wa gorin haihuwa Sadiya? Daɗin ta ma ni ma ba juya ba ce na haifi biyu ga su nan a zaune. Sannan da kike maganar Abdul ina ruwana da lamarin shi, kenan ɓakin ciki kike dan ina riƙe shi saboda ni matar uba ce duk abin da ya faru a tsakanin su sai a manna min laifi?"
A fusace Mommy ta ce "Duk abin da kika ce haka ne! Na faɗa miki dai ki daina shiga harkarsu tun da ba ke kika ji ciwon kawo ɗaya daga cikin su duniya ba, in kuma akwai wanda kika haifa sai ki mana bayani mu ji. Wallahi haƙura na gaf da ƙarewa a gidan nan, idan da kun ci mutumcina na rabu da ku kuna cin darajar mazajenku to yanzu zan aje ganin girman su nake rama duk abin da kuka min, haba ina dalili ina mafari na gaji!" Ta ƙarashe maganar cikin ɗaga murya gabaɗaya jikinta rawa yake saboda in har ranta ya ɓaci ko'ina na jikinta rawa yake.
Kukan ƙarya Umma ta fashe da shi tana sa mayafinta ta rufe fuska "Waiyo Allah! Wai yau ni ake yi wa gorin haihuwa? Laifin ka ne Daddyn Abdul da ba ka bani Abdul na rike ba ai da ba a min gorin ba ni na haife shi ba, sannan ke da kike wani tunkaho ke nawa ɗiyan gareki? Ba ɗaya tal gareki ba kamar rai? Ita ma sunan ɗayar ce dan rabi cuta ta cinye ta, ɗiyar da ba za shiga kitchen ta miki girki mai hayaƙi ba meye amfanin ta?" Ta faɗa tana shafe fuskarta tare da hararar Abir da ta yi kicin-kicin da fuska tana kallon Abdul.
Wani irin zafi da raɗaɗi ne suka ziyarci zuciyar Mommy, ta danne hawayen da ke ƙoƙarin zubo mata ta ce "Alhamdu Lillah duk da haka ina gode wa Allah da ya bani mai cutar ma, nasan dai ai ba ita ta ɗaura wa kanta rashin lafiyar ba Allah ne ya jarrabe ta da ciwon, idan ya ga dama lokaci ɗaya zai yaye mata."
"Tsuwwww! To yaushe kin taɓa gani mai cutar asma ya warke ya dawo irin na kowanni ɗan'adam?" Cewar Ammi.
Kwafa Mommy ta yi ta ce "Ke kuma faÉ—i ba a tambaye ki ba wa ya kasa da ke da har kika tsoma mana tsantsaman bakinki a cikin magana? Ki bari kema ina nan dawowa kanki Wallahi." Ta faÉ—a tana gyara zama..
Tun da suka fara cecekucen Abba da Daddy suka zuba musu ido suklna kallon ikon Allah, ganin ba za su ƙyale ba ya sa Abdul cewa "Mom don Allah ki rabu da su a tattauna a shayo kan wannan matsalar, da girmanku da komai kuke sa'insa a gaban yara."
"Dama sai ka ce ta rabu da mu mana tun da ga mahaukata ka samu."
Banza Abdul ya yi da Ammi bai ce komai ba,
dan in ya ce zai kara magana ba zai faÉ—i kalma mai daÉ—in ji ba.
Abba da ranshi ya gama ɓaci ya ce "Wallahi ban ji daɗin abin da kuka yi ba."
Daddy ya ce "Yanzu dai duk ba wannan ba matar Yaya ki faÉ—a me ke faruwa."
"Kabir meye ma bai faru ba, ba wannan karon kaɗai na ne Matarka take son kashe min ɗiya, da zarar ta ga ta je part ɗin ta sai ta kunna hayaƙi alhalin ta san lulurar ta ba ta son shaƙar hayaƙi, amma dan mugunta sai ta yi dan haka wannan ya zama shi ne karo na ƙarshe da za ta kuna wa 'yata hayaƙi dan ta je part ɗin su." Labarin yadda Salim ya kawo Abir ta ba su ita ma Abir ta faɗi farkon shigar ta babu wani hayaƙi a palon da ta fito ne ta ga ya turnike ta..
Sosai ran Daddy ya ɓaci da jin abin da Umma ta aikata ya ce "Amma Wallahi Baraka kin ba ni mamaki."
Saurin katse shi Umma ta yi ta ce "Ok haka ma za ka ce?"