← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 120

Sashe 51

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri Jarmai ya ce "Abu na farko da muke so Boka, muna son a kashe Damisa, na biyu muna son a sa wannan yarinyar ta tattaro duk wata kadara da mahaifinta ya bari ta kawo mana har inda muka cikin sirri bare da kowa ya sani ba, na uku kuma bayan ta gama kawo mana muna so a kashe yarinyar da uwar, shi kuma ɗan'uwan ta ya zama kamar karen mu duk wani abu da muke so a hukumance da mun ba sa umarni ya bi babu gargada. Sannan in mun tsunduma harkar siyasa mu yi nasara, muna so kowa da ke wannan Jaha tamu ta Yola ya ƙaunace mu ya zaɓe mu in lokacin zaɓe ya yi.."

"Hahaha! Sallamammu za ku samu biyan buƙata, amma fa aikin nan da za mu yi muku mai matuƙar wahala ne, dan haka dole abin daki-daki yadda komai zai tafi daidai. Abu ma fi sauƙi shi ne in kuka tsunduma harkar siyasa za ku yi nasara sosai mutane za su so ku fiye da tunaninku, na biyu kuma ba za a iya kashe Damisa ba saboda tun kafin ku zo wata yarinya ta taɓa kawo sunan shi a kashe shi, da na tura masa baƙaƙen aljannu babu wanda ya dawo a rayé duk ya kashe su, shi kan sa aljanin kan sa ne mugun hatsabibi ne. Maganar wannan yarinyar da mahaifiyarta shi ma ba za a iya kashe ta ba yanzu, saboda ƙaddararta mu mai yawa ce a rayuwarta. Yanzu haka maganar da nake muku wata gagarumar jarabawa na tunkaro ta ta zo kaf da faɗawa ciki, ba ku kaɗai ba ne kuke bibiyar rayuwar wannan yarinyar akwai masu son ganin bayan ta bayan ku ɗin nan, dan haka aikin ta mai wahala ne amma zan gwada na gani. Ɗan sanda shi nashi mai sauƙi ne da zarar ka aura masa ƴarka za ka kake samun duk wani lagon shi. "

Katse shi Alhaji Mustapha ya yi cikin jin daɗin bayanin Boka ya ce "Boka dama ina so na ma maganar ita ƴar wajan nawa da zan sa dole ya aure ta, ina so a cusa masa tsananin ƙaunar ta, ta yadda duk abin da ta ce masa ba zai mata gardama ba."

Dariya Boka ya yi ya girgiza kai ya ce "Wannan duk mai sauƙi ne, da zarar kun koma za kuke ganin aiki yana ci ɗaya bayan ɗaya, dokokin da sharaɗin wannan aikin wannan layar za ku samu gawa wadda ta kwana kafin a binne za a sa a bakin gawar a ɗinke bakin da zare da allura, wannan ɗayar layar ita kuma za ku samu maƙabarta ku je kan ƙabarin ƙaramin yaro wanda ba zai wuce shekaru 15 ba ku tona ƙabarin har sai kun tardo gawar sai ku saka layar a gefen shi ku mayar ku binne. Wannan ɗayar layar za ku samu rijiya tsohuwa wadda aka daina shan ruwan ta ku jefa ciki, idan har kuka yi haka a daidai to buƙata za ta biya. "

Ji suka yi kamar su kurma ihu dan dadi, dan wannan sharaɗin ai mai sauƙi ne a wajan su, Alhaji Mustapha da ya fi kowa jin daɗin wannan lamari musamman da zai aurar da ƴarsa wadda ta gagare shi marar jin maganar manya, ga shi idan har ta haihu zuwa shekara lokacin za su kashe Abdul sai dukiyarshi ta zama ta Hafsat, shi kenan komai ya zama mallakin su.

Tsawa Boka ya daka musu ya ce "Ku tashi ku tafi."

Jarmai ya sa hannu a aljihu ya fito da ɗaurin 'yan rafa guda biyar kowani dauki dubu 100k, aje wa ya yi a gaban Boka jiki na rawa ya ce "Boka gagara badau ga kafin alƙalami, idan aiki ya ci duk abin da kake so za ayi ma."

Ɓata rai Boka ya yi ya ce "Mu ba ma amsar kuɗi sai dai mu biya buƙata da mutum ko mace ce ko namiji ne, dan haka kowa ya shiga can na biya buƙata ta da shi."

Kallan kallo suka dinga yi, Alhaji ya ce "Kun ga na gane abin da yake nufi, dan haka indai muna son mu cimma burinmu to fa sai boka ya yi amfani da mu dan ya samu ƙwarin gwiwar yi mana aiki yadda muke so, abin da mun saba yi ko so kuke sai na muku gwari-gwari?" Jin abin da ya faɗa sai suka fahimta dan haka Jarmai ya tashi dan tuni Boka ya shiga ciki wata ƙofa yana jiran ɗaya daga cikin su ya zo, da ɗari-ɗari ya shiga ɗakin..

Sun fi awa kafin ya fito yana sharce zufa ya yi sharkaf kayan shi a hannu daga shi sai gajeren wando ya fito ko single É—in ya cire ta, Dariya Alhaji Mustapha ya yi yana kallon Jarmai da ya dawo wajan sa ya zauna yana sakin numfashi. Tashi Alhaji ya yi ya ya cire babbar rigarshi ya shige É—akin, shi kuwa sai da ya fi awa É—aya sannan ya fito yana É—aure zariyar wandon shaddarshi, murmushi ya yi ya kalli Alhaji Mustapha ya ce "Malam tashi ka je ko mun koma Legos."

Tashi ya yi shi ma ya shige, shi ma kamar na Alhaji ya fi awa kafin ya fito rigarshi saɓe kan kafaɗarsa, Boka ya fito yana wani tanɗe baki ya zauna a wajan zamansa ya kwashe da dariya, suma dariya suka yi ya nuna su da hannu ya ce " Ku tashi ku tafi in kun ga wani abu ba daidai ku dawo, ku fita da baya-baya."

Haka suka tashi suka fita boka na musu rakiya da ruwan ashar har suka fita. Da sauri suka dinga sauka lokacin har dare ya yi dan a lokacin ƙarfe 10:pm na dare, da haske wayar su suka haska suka fita suka dinga tafiya har suka zo inda suka faka motarsu suak shiga suka bar wajan..

Suna isowa Legos ƙarfe 12 ta buga suka samu hôtel suka kwana washe gari suka Legos zuwa Yola..

Yau Suhal ya shirya shi da Sajida za su koma gida ba dan ya so tafiya ba sai dan kiran da Maimartaba yake masa da kuma Ikilima suna tambayar ko lafiya bai dawo ba, haka dai ya tattara ya nufi gidan su Baba dan ya musu sallama. Suna isa suka samu Zaiyan a harabar gidan ya ɗane kan bishiya mangwaro dake ɗan gefe da inda suka paka mota yana lilo. Sai ya kama rishe ya zuro kanshi ƙasa ya maƙale ƙafafun a jikin rishe ya dinga lilo yana ta dariya, jin ƙarar mota a gefen shi sai ya daina lilon ya tsaya cak shi bai sauko ba kuma bai koma ya zauna akan rishen ba kansa yana reto yake kallon motar har Sajida ta fito Suhal ya fito, ganin wanda ya fito sai ya sheƙe da dariya ya ce "Shege abokina ashe shi ma yana da jirgin sama."

Da mamaki Suhal yake kallon Zaiyan ganin yadda ya ɗane sama ya zuro kai, ƙarasowa ya yi ya kalle shi ya yi murmushi ya ce "A a abokina me ya sa ka hau sama?" Lumshe idanu ya yi ya ce "Sabuwar masarautata ce nake son yin gini mai kyau, shi ne fa ka ga na zo ina koyon yadda ake ginin dan bana so Baba ya ce ba ta yi kyau ba."

Dariya Suhal y yi har ita Sajida, kallon shi ya yi ganin yana masa dariya sai ya koma samar rishen yana Ɓata fuska ya ce "Ni fa na faɗa ma ka daina kula wannan Maman taka tun da haushi take ji dan ban ƙulla abota da ita ba, amma dai zan ke kallon ta tun da ita Mamanka ce."

Sajida ta gumtse dariyar ta ta kalli Suhal ta ce "Allah ya ba ka haƙuri Zaiyan, ni ai bana jin haushi dan ba ka ƙulla abota da ni ba."

Tim! Suka ji a bayan su suka waiga da sauri sai suka ga shi ne ya faÉ—o daga sama, tashi ya yi yana karkaÉ—e jikinsa ya ce "Ke dai Maman abokina bakya tsoron Allah, ki faÉ—i gaskiya kawai in ba wannan hular tawa kike so zan ba ki ita sai kike sakawa, ni fa da kike ganina na iya komai."

Kamo hannunsa Suhal ya yi ya ce "Ka ga abokina rabu da ita muje ciki mu gaisa da su Inna za mu tafi Niger."

Turus ya tsaya yana kallon Suhal, sai can kuma ya yi dariya ya ce "To amma abokina in ka tafi wa zai zuwa gidan mu yana sayo min wannan alewar mai zaƙi da kayan wasa?"

Shafa kai Suhal ya yi yana yi murmushi ya ce "Ai a can ake yi shi ya sa zan je na kwaso ma mai yawa wadda za ka daÉ—e kana sha, kai har ma da kayan wasan zan sayo ma masu kyau."

Tsalle ya yi ya rungume Suhal yana tare ya ce "Ashe kana tsoron Allah abokina?"

Duk da Suhal ba ma'abocin dariya ba ne wannan karon sai da ya yi dariya jin abin da Suhal ya faÉ—a, É—ago shi ya yi ya ce "E ina tsoron Allah mana."

Kama hannunshi Zaiyan ya yi suka nufi ciki yana kwara wa Inna kira.

"Inna! Inna!".

Da sauri Inna ta fito daga ɗaki a firgice dan ba ƙaramin tsoro ta ji ba da kiran da yake mata, ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Au ashe kune yake ta kira na? To sannun ku da zuwa."

Suhal ya ce "E Inna mun zo yi muku Sallama ne daga nan za mu tafi Kano sai mu wuce gida daga can."

"Allah sarki yaron nan Allah ya maka albarka, mun gode da taimakon da ka yi wa Zaiyan Allah y saka da alkhairi." Ta faÉ—a tana share hawaye.

Murmushi ya yi da ya zame masa jiki ya ce "Haba dai Inna meye kuma na kuka ai a kowani lokaci za ku iya ganina na dawo nan garin, ina Baba yake?"

"Malam bai ya nan, ya fita zuwa can unguwar da muka taso an yi wa maƙocin sa haihu ne ya je wajan bikin."

Sallama ya mata tare da aje mata É—aurin kudi ya juya zai tafi ya ji Zaiyan na magana.

"Abokina kake jin tsoron Allah zan ke zuwa gidan ku gobe da jibi."
Chapter 51 · 0% Book details