← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 120

Sashe 60

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ajiyar zuciya ta sauke sai kuma ta sakar masa sanyayyan murmushi tana kallon shi, kallon kallo suke a tsakanin su ba wanda ya yi ƙoƙarin janye idanunshi daga kan na ɗan'uwan sa. A ɓangaren Abir ita tana masa wani kalar kallo ne wanda ita kanta ta kasa fassara shi, ga tsananin tausayin shi da ya mamaye mata gangar jiki da ruhi sosai take jin zafi mai haɗe da ciwo a cikin zuciyarta in ta tuna nan da kwanaki kaɗan za ta bar shi. Shi kuwa Zaiyan kallon da yake mata na sauraron amsar da za ta ba shi, amma ganin ta kafe shi da na mujiya sai shi ma ya ci gaba da kallon ta yana murmushi a tunanin sa wasa ne suke. Ita ta fara janye idanuwanta ta lumshe su cikin yanayi irin na musu rashin lafiya har wani jiri-jiri take ji saboda yadda zuciyarta ke bugawa da sauri-sauri, bude idanu ta yi a kan shi ta ga ya ɓata rai kamar zai yi kuka sai ta sakar masa murmushi ta ce "Zaiyan wa ya ce maka Baba saceni ya yi?"

Dariya ya yi yana tashi tsaye, miƙa mata hannunsa da ya yi ƙura ya yi ya ce "Za ki sha mangwaro Anty?" Ya faɗa yana nuna mata bishiyar mangwaron da ke gefen su ta yi ɗiya sosai amma ba su kai ga nuna ba. Tashi ta yi ta kalli bishiyar ta ce "To ai bai nuna ba ka bari nan da sati sai na sha." Ta faɗa tana sauke numfashi. Murmushi ya mata ya damƙi hannunta yana cewa "To zo muje Inna ta siya miki abinci ki ci, kin ga abokina tun da ya tafi bai dawo ba, kuma ya ce wai na yi ƙawance da mamansa yanzu Anty sai in yarda kawai dan yake cewa na amshe masa Mamansa?"

Dariya ta yi daidai lokacin suka iso palon sai ta yi sallama, amsa mata Inna ta yi tana mata sannu da zuwa ita kuma tana amsawa.

Bayan sun gaisa nan ta sanar da Inna an sa mata rana nan da wata daya mai zuwa, sosai Inna ta taya ta murna ta kuma sa mata albarka tana amsawa da amin. Suna a haka Baba ya zo suka gaisa Inna ta faÉ—a masa sa ranar auren Abir, ya ji daÉ—i sosai ya ce ai Abdul ya faÉ—a masa a waya..

Sai da Yamma lis ta musu sallama ai kuwa Zaiyan ya manne mata ya ce shi fa babu inda za ta tafi ta bar shi dama dan Baba yana sace ta ne yake hakura amma yanzu tun da ya dawo da ita to zai bi ta, dariya sosai Abir ta yi in ta ji ya ce wa Abdul Baba ta kama hannunshi suka nufo harabar gidan tana yi masa wayo dan ya bar ta ta tafi.

"Zaiyan ka koma ciki zan je na sayo maka kayan daÉ—i ne a kasuwa har da kaya duk zan sayo ma."

Maƙale kafaɗa ya yi yana turo baki ya ce "Ni dai Anty zan bi ki." Dafe kai ta yi ta juyo ta ga Baba ya nufi bayan ɗakunansu ita kuma Inna ta koma ciki ta sauke ajiyar zuciya ta ma rasa wata kalma za ta yi amfani da ita wajan ganin ya koma ciki, iska ta firzar ta kalle shi cikin idanu ta ce "Zaiyan ka yi hakuri ka koma zan dawo." Ta faɗa tana dan haɗe fuska.

Nan ma maƙale kafaɗa ya yi ya ce "Tab Alƙur'an in na yarda shege nake, salon ki tafi Baba ya sace ki."

Dariya maganar ta ba ta sai ta yi murmushi ta zarga handbag ɗinta da ke maƙale a kafaɗarta ta zaro 'yan dubu-dubu sun kai ashirin ta miƙa masa tare da cewa "To amshi wannan ka kai wa Inna sai ka dawo mu tafi."

Waro idanu ya yi yana kallon kudin ya ce "Kai kai kai! Duk wannan kudin zan kai mata?"

GyaÉ—a masa kai ta yi ta É—aga baki za ta yi magana ya warci kuÉ—in ya kwasa a guje yana É—aga murya ya ce "Ki tsaya yanzu zan kai mata na dawo."

Da hanzari ta fito da wayar ta jin yltana ringing sai ta ga Ali ne ta yi hamdala tare da dagawa ta ce "Hello Ali ka iso ne? Can kuma ta ce "OK yanzu zan fito kafin ya dawo." Da sauri ta fita daidai lokacin Baba ya dawo ganin yadda ta fita ya yi murmushi, ko ba a faÉ—a masa ba ya san abin da take yi wa sauri..

Tana fitowa yana isowa ta shiga ya ja suka bar gidan..

Zaune take a gaban wani ƙaton mutum ya sha rawani kamar Limani da ɗan gemunsa kamar na tsatso, gaban shi wani faranti ne cike da ƙasa yana ta zane a kai, can ya ɗago yana cewa "Hajiya gaskiya akwai matsala gagaruma."

Dafe ƙirji ta yi tana fadin "Na shiga uku! to yanzu Malam me ye abin yi? Dan ni Wallahi na tsani na daga idanu na ga yarinyar nan a cikin farin ciki, na tsane ta tsana mai tsanani tun da har za ta samu mijin aure ɗiyanmu suna nan ko mashinshini babu ba zai yiyuba, ina so ka sa mata baƙin jini ta yadda kowa zai tsane ta ya ji ba ya son ganin ta har familyn ta bana son kowa ya Ƙaunace ta so nake duk duniya kowa ma ya tsane ta kamar yadda na tsane ta. Kuma ina so auren nan duk ta yadda za ayi a ruguza shi Malam. " Ta faɗa tana hura hanci sama.

Murmushi Malam ya yi yana shafa gemunsa ya kuma share zanan da ya yi ya soma zana wani, É—ago da kai ya yi ya ce "A cikin 'ya'yanki wace ce Khairat?"

Baki ta washe ta ce "Babbar 'yata ce Malam wani abu ya faru ne? "

Girgiza kai ya yi yana cigaba da zanan can dai ya Goge gabaɗaya ya ɗauki Casbi ya ja sai ya aje a gaban ta ya ce "zaɓi ɗaya."

Zaɓa ta yi ta miƙa masa ya amsa ya ci gaba da ja har da wani lumshe idanu yake kamar bai yin hadda, sai da ya ɗauki lokaci kana ya aje ya sake zana ƙasar ya goge sannan ya ce "Hajiya wannan aikin da kika zo da shi ya sha bamban da duk aiyukan da nake miki a baya, tabbas ganin bayan wannan yarinyar abu ne mai wahala saboda tana da tsari sosai a jikinta ba ta wasa azkar ɗin safiya da maraice, sannan akwai wani haske da nake gani a tare da ita na kasa gane shi wanan haske mene ne shi? Tabbas dole ne sai an tashi tsaye indai har kina son wannan aikin naki ya ci, amma ko da kin yi ba lalle kowa ya tsane ta ba dole sai an samu mai son ta ko da ba cikin garin nan yake ba. Maganar a lalata aure wannan mai sauƙi ne za ayi ya dawo da shi kan ƴarki Khairat ita ce za ta zama matar Yarima Suhal, da fatan ya ci wannan magani da na ce a zuba masa a abinci? "

Wani irin daɗi Umma ta ji jin za a raba wannan aure, baki na rawa ta ce "Tabbas ya ci dan Iman ta tabbatar min sai da ya ci kana ta baro ɗakin, ni dai burina ta yi baƙin jini yadda bana son mahaifiyarta itama bana son ta dan haka a yi ko ma mene ne wanda zai ƙunsa mata baƙin ciki har mutuwar ta."

Jinjina kai Malam ya yi ya ce "Haka ne Hajiya, ki je gida za ki ga abin da zai biyo baya, auren ai kin ce saura sati biyu ko?"

Saurin gyaɗa kai ta yi tana jin wani farin ciki na mamaye ta, dole ne ma ta je ta soma gyara Khairat kafin satin nan ya cika, dan so take ko da Khairat ta je masarautar Niamey à gan ta Kamar ƴar gidan mulki. Har ta runƙuya za ta tashi sai kuma ta yi saurin dawowa ta ce "Malam ina son a kama mana Yarima a hannu ya haukace akan Khairat, so nake sai ranar ɗaurin aure ya ce ya fasa son Abir Khairat yake so zai aura, ina so taji baƙin ciki marar yankewa a wannan rana."

"Ba ki da matsala Hajiya ai yanzu haka tun jiya na soma aiki a kan shi kuma za ki ga mai zai faru ranar bikin." Godiya ta masa ta tafi tana ta dariyar ƙeta har Allah-Allah take ranar nan ta zo dan ta ga wata kalar suma Abir za ta yi...

Alhaji tun da Doctor ya ɗauki Sweet girl ɗin shi ya kasa samun nutsuwa da an jima sai ya kira ya tambaya ko ta farfaɗo, doctor ya ce masa da sauran lokaci dai, hakan na ƙona masa rai dan haka ya shirya ya je asibitin da kan shi har ɗakin da aka kwantar da ita, tun daga bakin ƙofa yake kallon ta har ya iso bakin gadon ya zauna tare da kama hannayen ta yana ɗago da ita ya rungume ta yana sauke ajiyar zuciya. Shi dai Doctor mamaki ne fal ransa akan lamarin Alhaji yana son ya tambaye shi amma mugun tsoron Alhaji ya hana ya yi tambayar dan haka ya bar maganar a ransa, sai da ya yi gyara murya ganin Alhaji na ƙoƙarin raba ta da rigar Asibitin da aka sa mata. Yi ya yi kamar bai san da shi ba ya sumbace ta a goshi ya juyo ya kalli Doctor ya ce "Likita yanzu yaushe za ta tashi wai? Bana son a samu matsala fa akan sweet girl ɗi na, in kuwa hakan ta faru Wallahi zan iya kashe kowa a kan ta saboda ina matuƙar son ta fiye da tunaninka."
Chapter 60 · 0% Book details