Sashe 101
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kamar wata ƙadangaruwa ta gyada masa kai, ta nemo photon Family ta ta nuna masa ɗaya bayan ɗaya, amma ba ta sanar da shi labarin Suhal ba dan tana so wata rana ta masa bazata. Shi kuwa duk tausayin ta ya cika masa zuciya, ya kuma ƙudurta a ransa ko ba ya son ta zai zauna da ita saboda haliccin da ta masa a rayuwar da suka yi, a hankali ya miƙa hannu ya janyo ta jikinsa ya rungume yana shafa bayanta, ita kuwa jin ta a jikinsa sai ta yi lamo tana sauke numfashi.. Sun dauki lokaci a haka ta ji ya ɗago ta tare da ɗago fuskarta ya manna mata kiss a kumatu ya kuma mata a goshi, duk da tsoron sa da take ji hakan bai sa ta ja da baya ba sai ma lumshe idanu ta yi tana jin yadda yanayin ta yake canjawa. Janye jikinta ta yi ta janyo wayarta ta duba lokaci ta ga karfe 10:a.m har ta yi, da hanzari ta yunƙura za ta tashi ya yi saurin kamo hannunta ta dawo ba shiri ta zauna, ƙara ta sa tana yarfa hannu ya kalle ta yana jero mata sannu ta kwace hannun ta kuma miƙewa tana hararar shi.
"Ina za ki tafi?"
Haushi ya rufe ta ta sunkuya ta ɗauki abincin su na jiya ta fita ba ta ce masa uffan ba, ganin ta fusata sai ya koma kan katifar ya kwanta yana lumshe idanu, tambayoyi yake son mata amma ya ga gabaɗaya ma tsoron shi take ji, tuna abin da ya faru tsakanin su ya ƙara jin tausayin ta sai kuma ya tashi zaune, so yake ya ƙara ganin yadda ya koma dan sosai ya yi mamakin ganin girman shi a photo, Janyo computer ya yi sai ya ga akwai code ba zai iya amfani da ita ba, sunanta ya sa amma aka nuna masa error ne ya saka, sai ya sa sunansa da ta faɗa masa ya ga ta buɗe abin ya ba shi mamaki yana kuma jinjina zallar tsagwaron son da take masa, photunan ya kuma bi yana kallo ganin yadda ya tara gemu ga saje, ya riƙe baki yana yi wa Allah godiya da ya ba shi lafiya...
Haka ta daddaure ta dumama musu abincin, bayan ta gama ta kuma tafasa wani ruwan zafin sai ta zuba ɗan kaɗan a coup ta koma ɗakin. Yana ta daddanna computer ta same shi kawai ta share shi ta isa ta haɗa shayinta mai kauri ta ɗauki wayarta ta fito da cup ɗin a hannunta tana hura hanci, wato ma shi ko a jikinsa ta kuma yin kwafa ta zauna a waje tana kallon su Amal da suke wasa ita da ƙannanta biyu. Sai da ta shanye shayin tas sannan ta dawo ɗakin ta tsaya masa a ka ƙerere, kallon ta ya yi da alamar tambaya sai ta turo baki ta ce "Ka ɗauko min ruwa a waje na dafa."
Bai ce da ita komai ba ya janye computer ya fita ya ga babu kowa sai wasu yara biyu, ya kalli gidan ya ga dai lalle fa a gidan haya suke, dauko ruwan ya yi ya kawo mata zai aje ta ce ya zuba mata irin na asuba, ya zuba mata sannan ya fito. Kayan wanka ta dauka ta shige abin ta ya bi bayanta da kallo, mamaki sosai yake yadda ta jure rayuwar irin ta talaka saboda shi, ta baro ahalinta gidan da ko maigadin gidan ya fi ƙarfin ya zauna a irin wannan gidan ballantana ɗiyar masu gidan, komawa ya yi ya kwanta jin yadda kuzarinsa ke yin ƙasa, wata irin kasala ce ta rufe shi sai miƙa yake karshe sanyi ya kama shi ya janyo abin rufa ya rufa ya ƙudundune. .
Umma hankali a tashe isa gidan Malam, koda ta isa ta soma zaiyano wa Malam shiri fa na neman wargajewa, sai da ta gama yi masa jawabi bai ce da ita komai ya yi tsumu-tsumu kamar É—an tsakon da ya faÉ—a ruwa. Kallon shi Umma ta yi cike da mamaki ta ce "Malam ya ka yi shuru ba ka ce komai ba?"
Gyara zama ya yi yana muzurai ya janyo farantin gabaɗaya komai a sanyaye yake aiwatarwa, bayan ya gama duddubawa ya ɗago ya kalle ta ya ce "Ba komai duk za a gyara da alama dai ke ce kika ɓata aikin."
Dafe kirji ta yi tana zaro idanu jin abin da Malam ya faÉ—a, a ruÉ—e ta ce "Malam ni dai don Allah a taimaka min kar aikin nan nawa ya samu matsala, yanzu fa gabaÉ—aya family Maitama ya hargitse sai neman wannan yarinyar suke."
Kwantar mata da hankali ya dinga yi ya sanar da ita zai gyara komai sannan ta tafi.
Karfe 1:30pm daidai shi ya riga ta tashi ya shige banɗaki ya yo wanka ya fito, yana goge jikinsa ne ya ga tana motsawa sai ya juya mata baya dan kar taƙi tashi. A hankali ta soma buɗe idanuwanta har ta gama buɗe su a kan shi, saurin tashi ta yi ta zari hijabi ta wuce banɗaki kanta a ƙasa, da kallo ya bi bayanta cikin yanayi mai nuna zallar tausayin ta, girgiza kai ya yi ya sanya kaya ya shinfiɗa musu dadduma ya zauna zaman jiranta ta fito. Jim kaɗan sai ga ta ta fito ta nufi wajan kayan su, sai da ta juya ta ga ba ita yake kallo ba sannan ta yi saurin sa kaya cikin rawar jiki. Duk abin da take yana kallon ta ta gefen ido, ganin yadda take sauri sai abin ya ba shi dariya wai duk dan kar ya ga jikinta ne take wannan abu kamar mazari, tana gamawa ba ta ce masa komai ba ta iso kan daddumar, shi kuma ganin haka ya tada iƙama.
Bayan sun gama ne ya juyo tare da gyara zama cikin nutsuwa ya sa hannu ya matso da ita kusa da shi ganin tana takurewa a waje ɗaya , ba dan ta so ba dai ta zauna. A hankali ya ɗago da fuskarta ya tsura mata idanu, itama tun tana ƙin kallon sa har ta saki jiki ta ɗago ta kalle shi. Sun jima a haka sannan ita ta fara janye nata idanun sai a lokacin ya motsa lips ɗinsa cikin sayayyar murya ya ce "Jiddo."
Da sauri ta kalle shi ta yi sauri sunkuyar da kai, murmushi ya yi sannan ya É—aura da cewa, "Kin san asalin sunana kuwa?"
Tana daga haka ta girgiza masa kai sai kuma ta ɗago tana kumbura baki, murmushi ya kuma sakar mata ya sa hannu ya bubbuga kumatunta, saurin ɓoye fuskarta ta yi a jikinsa ya ɓamɓaro ta tare da cewa "Kin ga tashi mu yi magana mai mahimmanci, ina so na sanar da ke ni ko waye."
Lumshe idanu ta yi wani sanyi ya ziyarce ta har kasan zuciyarta, dama abin da take son tambayar shi yau ɗin nan tun da ta ga yanzu duk wani abu na rayuwarsa zai tuna a cikin kwana biyun da ya yi na samun lafiya, zama ta yi akan cinyarsa ya tallafo ta ta baya ta kalle shi tuna wani da ya yi mata kawai sai ta sa dariya tana rufe fuska, shi ma murmushi ya yi yana mamakin abin da ya sa ta yin dariya, sai da ta tsagaita ya ce "Me kike yi wa dariya?" ƙunshe baki ta yi tana son ta daina dariyar dan ta sanar da shi, sai da ta tsayar da dariyar ta sauka akan cinyarsa ta zauna a gefen shi ta ce "Na tuna wani lokaci ne da ka min wankan taɓo har da cewa nan wajan bai samu ba. Nan dai ta shiga faɗa masa abin da ya faru ranar da ta same shi yana ɗakin ƙasa har kuka ta yi dan takaicin abin da ya mata."
Ƴar dariya ya yi dan yanzu ya daina mamaki in ta ce masa ya yi wani abu a baya, agogon da za sayo masa ya janyo ya kalli lokaci ya ga ai har karfe biyu ta gota, kallon shi ta yi yana shirin ta yi ya ce "Bari na fita ko ma dako ne na yi na nemo mana abinci, har yau ina ƙara jinjina miki akan yadda kike ɗawainiya da ni na tsayin lokaci." jinjina masa kai ta yi dan ta so ya sanar da ita asalinshi, amma kuma ta hakura sai ya dawo ta masa Allah ya kiyaye har zai fita sai ta dauki waya ta miƙa masa, kallon ta ya yi ganin waya kuma ba tata ba ce, amsa ya yi yana juya wayar tare da mata kallon ta yi masa ƙarin bayani. Sunkuyar da kai ta yi ta ce "Jiya na ga Ladidi zai sayar da wayarsa shi ne na saya maka kafin ka samu ka yi sabuwa, na sa ma har layi da number na a ciki da ta Mama da ta mijinta." Ta faɗa tana tashi tsaye.
Rasa me zai ce mata ya yi kawai ya janyo ta ya rungume, murya can ƙasa ya ce "Jiddo ke matar rufin asiri ce, ke mace ce wadda kowanni namiji zai so samu Allah ya miki albarka, Ubangiji ya ba ni ikon kyautata miki fiye da yadda kika min."
Murmushi ta yi ta É—ago daga jikinsa ta ce "Amin mijina Allah ya tsare ka a dawo lafiya."
Fitowa suka yi a tare tana riƙe da hannunsa, Tasakkawato da ke shirin fita ta tsaya tana kallon su cike da burgewa, murmushi Abir ta yi ta ƙaraso kusa da ita ta ce "Mama ina zuwa? Jiya fa da dare kika dawo ko hira ba mu yi da ke ba, shi ne yanzu za ki kuma tafiya ba ko gaisuwa?"
Zaiyan ya matso tare da É—an rusunawa ya ce "Mama ina yini?"
Baki buÉ—e take kallon Zaiyan da ya sha wanka sai kuma ta ce "Jiddo shin wanga mijinki na ko kuwa dai ba shi na ba?"
Ƴar dariya ta yi ta ce "Shi ne fa Mama yanzu dai bari na raka shi zai fita sai na dawo mu yi magana."