Sashe 100
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Har ta fidda rai da zai tashi taji yana numfarfashi karshe ma tari ya sarke shi, tun yana yi a kwance har ya tashi zaune idanuwansa a rufe ya dafe ƙirji, daga karshe ya dinga attishawa ba ƙaƙƙautawa har ita kan ta abin ya tsorata ta, can da ta lafa ya ja dogon numfashi sai ji ta yi yana faɗin "La'ilaha illallahu Muhammad Rasulullah sallallahu alai wa sallam."
Daga haka bai kuma cewa komai ba, ta maƙure tana kallon ikon Allah jin ya yi kalmar shahada, bude idanu ya yi a hankali ya sauke shi akan ta ya zabura yana ja da baya baki na rawa ya ce "W..Wace ce ke?"
Gaban ta ya faɗi ya kalli kansa ya ga ba shi ta komai ya yi sauri janyo kayan shi ya sa yana a'uziya sai ƙara tambayarta yake ita wace ce? Da ta gaji da tambayar ta tabbatar dai lalle fa ya samu lafiya ta nisa ta ce "Matarka mana."
Sororo yake kallon ta irin ya ga abin al'ajabin nan, sai da ya kuma kallon nan ya gane abin da ya faru ya yi baya ya dafe kai, sai nanata Kalmar mata yake yi to yaushe ya yi aure bai sani ba? Kuma shi da bai ma isa aure ba ya aka yi har Mamansa ta bari ya yi aure?
😂😂😂Cakwakiya Iyar Haidar tamu ta gargajiya ki zo ki yi wa Zaiyan bayani...
_Maman Nusaiba_
[6/20, 8:43 PM] Ummu Amjad: A HAKA NAKE SON SHI*
Shafi na (49)
Ganin ba shi da wanda zai ba shi amsa sai wannan yarinyar da ya gani a kwance cikin yanayi ya nufi ƙofar da yake kyautata zaton bandaki ne, ita kuwa da kallo ta bi shi tana sharar hawaye cike da tausayin kanta, wai yau ita ce Zaiyan ke cewa wace ce ita? To amma ai ba lefin shi ba ne dole dama ya yi wannan tambayar, da kyar ta daure ta juya ta lalibo dogon hijabinta har kasa ta sa ta rufe jiki da shi. Tana nan kwance sai ga shi ya fito ɗaure da towel idanuwansa a kan ta dan gani yake kamar mafarki yake, yunƙurawa ta yi ta duƙa za ta rarrafa ta ji ya ce "Dakata!"
Cak ta tsaya tana kallon shi cike da takaicin dakatar da ita da ya yi, ga ya sanyo towel É—in da take son in ta yi wankan tun da a cikin banÉ—akin yake ta sanyo, a fusace ta ce "To ka kaini banÉ—aki. "
Da mamaki ya kalle ta sai kuma ya basar ya soma dube-dube, ganin bai samu abin da yake nema ba ya juyo da kallon shi gareta ya ce "Kayana fa."
Maimakon ta ba shi amsa sai ta sa masa kuka, ba yadda ya iya ya sunkuya ya dauke ta ya kai ta banɗaki, kasancewar ba ta rabuwa da ruwa mai zafi ta ce ya kawo mata ruwa da ta aje, yana son ya tambaye ta a cikin me amma ba ya son ta kuma fusata ya fita. Sai da ya jima kafin ya gano ruwan a inda take zubawa ya kinkima ya kai mata, ba ta ko kalle shi ba ya fita zuciyarsa cike da tarin tambayoyi, wayar da ya gani a gefen katifar ya ɗauka ya danna ya ga har ma an fito a Masallaci, har zai aje ya kuma kallon kan screen ɗin wayar inda ya yi arba da photonsu shi da ita sun haɗa kai waje ɗaya suna murmushi ita da shi, tsananin mamaki ya kuma rufe shi ya soma yarda da cewar da ta masa ita matarsa ce, ganin lokaci na tafiya ya yi saurin yaye abin shinfiɗar ya sa wani sannan ya zo ya tada iƙama..
Ita kuwa sai da taji ruwan zafin ya huce sannan ta tashi tana daddafa bango har ta miƙe tsaye, alwala ta ɗaura ta gwada tafiya ta ji ba ta jin ciwo mai tsanani dan haka ta daure ta fito ba komai a jikinta tana kumbura baki, ganin ya kai goshinsa ƙasa ta ɗaure ta cije lips ta janyo towel ɗin da ya cire ta sanya duk da ya jiƙe, ta tsaya a tsaye kamar soja ta zuba masa idanu ganin yadda yake Sallah a nutse. Zama ta yi a kan katifar tana runtse idanu sai kuma ta yi saurin tashi ta kalli katifar ta ga an cire abin shinfiɗa an sa wani, dogon numfashi ta sauke ta rarrafa ta kwanta tana jiran ya gama itama ta gabatar da Sallah, shi kuwa duk abin da take yana jin motsin ta, bayan ya gama ya shafa Fatiha sannan ya juyo ya kallo inda take, ƙura mata idanu ya yi gaban shi na faɗuwa tarin tambayoyi sun cika masa ciki ya ma rasa da wacce tambaya zai fara yi mata, tashi ya yi ya dawo kusa da ita ganin idanuwanta a rufe ya dan bubbuga gefen ta ta yi saurin zabura ta tashi, da kallon mamaki ya bi ta ganin yadda ta firgita ya girgiza kai tare da nuna mata dadduma.. Turo baki ta yi ta tashi tsaye ta nufi wajan kayansu ta buɗe, wani babban Hijabi ta dauko wanda sau ɗaya ta taɓa saka shi dan har jan ƙasa yake, zura shi ta yi tana ɗan ɗingisawa ta iso ta tayar da iƙama cikin dauriya. Da kyar ta gama Sallah a tsaye tana yi tana zubar da hawaye, ƙarshe ma da ta je sujjadar karshe ta fashe da kuka tana rokon Allah ya kawo mata ɗauki a halin da take ciki, hankalinta a mugun tashe yake da ta tuna tambayar da Zaiyan ya mata wai ita wace ce? Maganar na firgitar da ita da haka ta gama Sallar ta zauna akan daddumar ta sunkuyar da kai dan kar ma su haɗa idanu. Shi kuwa shuru ya yi yana jin abin da take faɗa sai ya ji ta mugun ba shi tausayi, hakan kuma ya tabbatar masa lalle akwai abin da yake damunta matuƙa, kusa da ita ya matso ya sa hannu ya ɗago fuskarta ita kuma taƙi su haɗa idanu sai ta runtse idon, iskar bakinsa ya fesar yana jan numfashi ya saita nutsuwarsa sannan ya ce "Ya sunanki? Kuma nan ɗin a ina muke? Ina mamana take? Yaushe na aureki?"
Saurin buÉ—e idanuwanta ta yi tana rawar jiki gabaÉ—aya tsoro ya dabaibaye ta, yanzu kenan ta zama ba ta kowa a kusa da ita? Shi wanda take gani ta ji sanyi yau ga shi Allah ya nufe shi da samun lafiya ya nuna bai san ita ko wace ce ba, hawayen da suka cika mata kwarmin idanu ne suka zubo ta kai hannu za ta goge sai ta ji ya sa lallausan hannunsa yana share mata, sai da ya sake tambayar ta a karo na biyu sannan ta tsagaita kukan ta ce. "Sunana Hauwa'u Maijidda amma an fi sanina da Abir, nan kuma muna a gidan haya ne su kuma da Jiddo suke kirana, sannan ni ban san ina mamanka take ba dan ba tare da ita ba na ganka."
Saurin sakin fuskarta ya yi yana kallon ta, to in ba ta san mamansa ba waye to ya shige masa gaba har aka yi masa auren? Girgiza kai ya yi cikin wani kalar yanayi har idanuwansa sun soma canja launi ya ce "To waye ya nema min aurenki indai ba ki ga mamana ba?"
Tashi ta yi ta isa ta zauna a bakin katifar ta janyo computer ta ta daddanna, ɗago kai ta yi ta dube shi ta masa alama da ya zo ya tashi jiki ba ƙwari ya isa gareta ya zauna a gefen ta, photunan su shi da ita ne suka bayyana ga su nan bila'adadin har da video ta miƙa masa, jan majina ta yi ta ce "Ka duba ka gani.."
Ɗaya bayan ɗaya yake ganin photunan wani suna rungume da juna, wani kuma ya kwanta kansa a cinyarta ta ɗan ranƙwafo ta dauke su selfi, wani kuma suna harabar gidan duk sun ɓata jikinsu da ƙasa ta musu photon, ya kuma yin ƙasa inda ya dauko video da suke tsare da shi tana dauka yana bin ta, sake ɗauko wani ya yi ya ga yadda ya yayyaga kayan jikinsa sabbin fil ita kuma tana gefe ta kama kunnensa, sake yin ƙasa ya yi sai ya ga video da yake kiran ta da Anty, al'ajabi, mamaki, tsoro, firgici, duk suka kawo masa ziyara a lokaci ɗaya.. Ɗago kai ya yi ya kalle ta cikin wani kalar yanayi ya ce "Anty."
Jinjina masa kai ta yi tare da matsowa daf da shi ta ce "Sunan da kake faÉ—a mini kenan tun farkon haÉ—uwa ta da kai ka taimakeni."
Mayar da kansa ya yi ya ci gaba da kallon photunan, ganin haka ta miƙa hannu ta dubo photon Baba da Inna wanda ta musu su huɗu ta nuna masa tare da cewa "Waɗannan sune a matsayin iyayenka, kuma su ne suka nema ma aurena."
Shuru ya yi yana kallon su Baba yana ƙara zuƙo fuskar Baba, sai can ya nisa ya ce "Wannan bawan Allah kamar dai na san shi can shekarun baya, mun taɓa zuwa gidan wani mai kama da shi ni da Mamana." Ya ɗago ya kalle ta sannan ya ɗaura, "To yanzu ina su waɗannan bayin Allah suke?"
Ajiyar zuciya ta sauke ta rausayar da kai ta ce "Suna Yola mu kuma muna Kano."
Da mamaki ya ce "Kano kuma? To me ya kawo mu Kano bayan kin ce su suna can a Yola?"
Ganin dai suna jan maganar ta soma faɗa masa duk abin da ya faru da su tun daga farkon haɗuwar su har auren da aka musu da yadda su Baba suka riƙe shi kamar su suka haife shi, ta kuma sanar da shi tarihin rayuwarta da yadda kowa ya tsane ta har da Yayanta Abdul har izuwa gudowa da suka yi daga Yola suka dawo nan Kano da gwagwarmayar da take wajan ganin ta ciyar da su ta tufatar da su....
"Inna lillahi wa inna laihin raji'un! Wai kina nufin ki ce min duk tsayin shekarun nan ciwon hauka nake fama da shi?"