← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 120

Sashe 22

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba su ba ta damar cewa komai ba suka ja gadon suka shige ciki, kuka ta dinga yi tana nuna hanyar da suka bi ta kasa magana har wasu daga cikin nurses ɗin suka fito daga ɗakin suka shiga ɗayan. Tana ganin sun fito da ɗayan kamar wacce aka tsikara ta miƙe zumbur ta tare su ta ce "Waiyo Allah! Ku buɗe min na gani." Da hannu Doctor Hashim ya musu alama da su buɗe mata ba muso suka buɗe mata fuskar, sake sakin wani kukan ta yi ta waiwaya inda Abdul ya ke tsaye kamar gunki ta ce "Yaya zo ka gani Wallahi Zaiyan ne shi ma ya mutu, La'ilaha illallah Muhammad Rasulullah sallallahu alaihi wa sallam." Ta ƙarasa ta yi baya luuu za ta faɗi. Sauri taro ta Abdul ya yi yana kallon fuskar Zaiyan da aka dinke masa goshinsa da kuma hannunsa, duk da bai taɓa ganin Zaiyan ɗin ba amma ya ji ya ba shi tausayi hakan yasa ya matsa suka wuce ita kuma aka kawo gado suka ɗaura ta aka shigar da ita ɗakin taimako..

Zarya Abdul ya dinga yi a wajan sosai ya shiga tashin hankali, gabaÉ—aya ya rikice da ganin Abie, wayarsa ya É—auka ya kira Abba yana É—auka ya saita muryarsa ya ce "Hello Abba ko mai kuke kai da Daddy da su Mommy ku zo Asibiti ku same mu."

Da sauri Abba ya miƙe tsaye ya ce "Waye ba lafiya Abdul?"

Girgiza kai ya yi kamar yana gaban shi, wani irin zafi yake jin zuciyarsa na masa maganar ma ta gagare shi, sai da Abba ya sake tambayar shi tukun da ƙyar ya iya haɗiye yawu mai ɗici hana runtse idanu ya ce "Ku dai ku zo Asibitin Doctor Hashim muna nan." Yana gama faɗin haka ya kashe wayar ya dawo zauna a kan ɗaya daga cikin kujerun da ke jere a wajan, tashin hankalin da yake ciki shi ne bai sani ba Abie yana raye ko kuwa dai ya mutu shi ne bai sani ba.

Yana zaune Doctor Hashim ya fito daga É—akin da aka sa Abir ya ce da Abdul ya biyo shi office.

Suna isa suka zauna Abdul duk ya ƙagu ya ji me Doctor Hashim zai faɗa masa, sai da ya gama rubuce-rubucensa sannan ya ɗago ya dubi Abdul ya ce "Am so sorry Abokina ba zan ɓoye maka ba Allah ya yi wa Abie rasuwa, dan ba ma yanzu ba ya rasu tun kafin su iso ya rasu, mun yi masa gwaje-gwaje mun gano kansa ne aka buga har jini ya haɗe da kwakwalwarsa hakan yasa kafin su iso ya rasu."

Tamkar saukar aradu haka Abdul ya ji furucin Doctor Hashim, da ƙyar ya daure ya ce "Inna lillahi wa inna ilaihin raji'un! Tun daga ina kuka ɗauko shi?" Ya faɗa wasu zafafan hawaye na sauka bisa kuncinsa. Shi kan shi Doctor Hashim sai da idanunsa suka cika da hawaye amma ya yi ƙoƙarin mayar da su dan kar ya ƙara karyar da gwiwar abokin nashi, a sanyaye ya ce "Wata number ce aka kira ake sanar da mu an buge wani mutum da mota amma masu motar sun gudu, shi ne aka tura ambulance inda da taimakon wannan mai kiran suka isa kusan ƙarshen gari a nan suka samu tsohon da ya kira su , inda yake sanar da su ai akwai wani ma gidansa da ya tsince shi da dare bayan ya dawo daga cikin gari ya nuna su shi ne suka ɗauko su gabaɗaya. Tun da suka tafi nake kiran number ka dan ku bi bayansu ku bincika komai to ba ka ɗauka ba har na gaji na aje wayar na kira Uncle Aruf shi kuma wayar ma a kashe take, ashe gawar Abie ce da wannan saurayin wanda na ga Abir ta ƙara shiga ruɗani da ta gan shi, ko ta san shi ne?" Ya ƙarashe maganar yana tambayar Abdul da ya yi ƙiƙam yana sauraron shi. Sai da ya buga tebirin gaban su sannan ya firgita ya dawo haiyacinsa ya yi saurin cewa me kake cewa Hashim?" Sake maimaita masa bayanin ya yi sannan ya ƙara da cewa "Yanzu sauran aikin na damƙa a hannunka."

Wani irin zafi zuciyarsa ke masa ya daure ya ce "Shi wannan wani ne wanda ya taimaki Baby shi ɗin ma sace shi aka yi kwanakin baya da suka wuce." Da sauri Doctor Hashim ya ce "To amma ai na ga kwakwalwarsa ta samu taɓuwa, a takaice dai ya haukace."

"Na sani." Abdul ya faɗa a takaice yana kai hannu ya goge hawayen da suka zubo amsa. Shi kuwa Doctor Hashim haƙuri ya dinga ba wa Abdul har Abba ya kira shi ya sanar da shi sun zo sannan suka fito tare. Kwatance ya musu na inda suke sai ga su sun nufo su, Mommy da duk ta fi su shiga damuwa a tunaninta Abir ce wani abin ya same ta tun da ta hango Abdul ba ta ganta ba ta yi sauri riga su Abba isa wajan, a ruɗe take tambayarsa "Abdul me ya faru da Abir ɗin?"

Girgiza mata kai ya yi Abba ma da ya ƙaraso ya tambaya lafiya? Bai ce da su komai ba sai ganin Abir suka yi ta fito daga ɗakin da aka kwantar da ita tana kuka ganin su Mommy yasa ta ƙara wa kukan ta volume, duk suka dinga tambayar ta me ya same ta amma ta isa ce musu komai, hakan yasa Doctor Hashim ya ce "Abba an tsinci gawar Abie ne yanzu haka yana ɗakin aje gawa."

Zaro idanu duk suka yi a kuma tare suka ce "Wani Abie É—in?"

"Abie dai wanda kuka sani. Bayanin komai ya musu har da na Zaiyan ya faɗa musu, Mommy kuwa tun da aka ce Abie ya rasu ta suma a tsaye sai da Abir ta taɓa ta ta ga ta yi baya za ta faɗi ta yi saurin kamo hannunta tana kuka ta ce "Mommy don Allah kema kar ki tafi ki barni."

Kan kujera aka aje Mommy Doctor Hashim ya sa aka kawo ruwa mai sanyi suka shafa mata ta sauke kakkarfar ajiyar zuciya sai kuma hawaye suka soma zarya kan kuncinta. Abba ya ce su je a ba su gawar Abie za su masa sutura ya kai su har kan gawar, sai da Daddy ya buÉ—e gawar ya ga tabbas wannan Abie ne a lokacin ne ya ji wasu hawaye sun silalo masa ya yi saurin gogewa..

Mota biyu suka zo da ita aka saka gawar a motar Abdul Abba da Daddy suka shiga, Mommy da Abir direban da ya kawo Mommy shi ya É—auke su É—ayar motar suka bar ta nan suka nufi gida..

Tun kafin su je Abie ya kira Daddyn Aruf ya faÉ—a masa abin da yake faruwa ya ce ga su nan shi da Aruf. Suna packing Abba ya fito ya kamo gawar Abie Daddy na taimaka masa suka fito da ita sai ga motar Daddyn Aruf da kuma ta Salim sun zo a tare, su duka suka shiga part É—in Mommy da gawar inda suka kai ta É—akin Mommy.

Maigadi da sauran ma'aikatan gidan duk ruÉ—ewa suka yi da ganin an fito da gawa, sai bayan sun shiga Direba ya sa hannu ya goge hawayen da suka zubo masa tuna irin tarin alhairan da Abie ke masa, babu abin da yake yi na gidan Abie ne ya É—auki nauyin komai nasa kuma duk wata a biya shi albashinsa mai tsoka. Bai san ba san da ya dafa mota yana kuka tare da faÉ—in "Allahu akbar! Allah sarki Alhaji mutumin kirki mun yi rashi babba a gidan nan, Allah ka haskaka makwancin Alhaji yadda yake haskaka rayuwar bayin Allah kamar ni."

Da sauri Maigadi ya matso kusa da shi cikin kiÉ—ima ya ce "Kai wai waye ya rasu?"

"Alhaji ne aka tsinci gawar shi." Ya faɗa yana tsayar da kukan. Salati Maigadi ya ɗauka yana dafe kai, tabbas sun yi babban rashi na uban gidan nasu mai kima da daraja a gare su har da danginsu, shi ma goge hawayen ya yi yana girgiza kai ya ce "Allah sarki Alhaji damo sarkin haƙuri, kamar yasan mutuwa zai yi duk ya ba mu albashin shekara-shekara. Ko da na ga kuɗin na sha mamaki saboda bai taɓa mana irin biyan nan ba, ashe dai a ranar ganin ƙarshe muka masa mishi, Allah ya jiƙan bawan Allah nan mai tausayi a taimkon na ƙasa da shi." Amin suka ce duk suka koma inda Maigadi oe zama suka zazzauna cikin jimami, sosai mutuwar ta daki zuciyoyinsu kowa sai girgiza kai yake yana faɗin hidimar da Abie yake yi da shi...

Grandma ba wanda ya sanar da ita komai sai da aka kawo ta gida ta ga part ɗin Mommy ya cika da 'yan gidan da kuma makota abin da ya ba ta mamaki, tambayar su take " Kun ji jama'a lafiya dai kuka tare a nan?" Ba wanda ya ce mata komai sai da ta hango Mommy na kuka ta ƙara shiga tashin hankali, Mommyn Aruf ce ta kama hannun Grandma ta ja ta suka shiga har ɗakin Mommy. Wani irin dafe ƙirji Grandma ta yi tana kallon gawa kwance a tsakar ɗaki, su Abba suka kamo ta ta durƙusa a gaban gawar hannu na rawa ta buɗe ta yi arba da fuskar Abie.

"Inna lillahi wa inna ilaihin raji'un! Ibrahimu! Ashe ba zan sake ganin ka ba sai dai na ga gawar ka? Allahu akbar kabiran Allah mai kyauta da karɓewa, Allah ya jiƙan ka Ibrahimu." Ta ƙarashe maganar tana goge hawayen da suke ambali a kan kuncinta..

Addu'a ta dinga yi masa su Abba na amsawa da amin har ta gama, da ƙyar Daddy ya fito da ita daga ɗakin ya kawo ta palo ya zaunar da ita a kusan Mommy.

"Yi kuka Sa'ade." Ta faÉ—a tana dafa kafaÉ—ar Mommy da ta yi kim tana kallon 'yan palon masu kuka na yi masu tagumi na yi.
Chapter 22 · 0% Book details