← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 120

Sashe 24

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Antyy!" Ya faɗa cikin rawar murya wadda ta sa Abir ta ɗago cikin wani irin yanayi mai wuyar fassarawa ta zuba masa lulu eyes ɗinta farare tas. Duk da gabanta yana dukan uku-uku sai ta ji sunan har ƙasan zuciyarta, lumshe idanu ta yi tana yin hamdala da bai gudu ba suka zo, a hankali ta buɗe idanuwanta ta kalle su ɗaya bayan ɗaya, hannunta da ke cikin nasa ta ɗan ja tana son ya sake mata hannun. Ƙara matse hannun ya yi yana duddubawa kamar mai neman wani abu a jikin hannun nata, numfashi ta sauke zuciya na wani irin bugawa da mugun sauri, da ƙyar ta iya kallon su tana ƙoƙarin saita nutsuwarta cikin ƙasa da murya ta ce "Don Allah za ku iya ba mu guri za mu yi magana da Doctor?"

Ba matsala suka ce sannan suka fita daga ɗakin suna mamakin yadda ya yi luf da ya ganta, wani daga cikin su har ya kai bakin ƙofa ya kasa daurewa ya juyo ya ce "Ranki ya daɗe amma dai wannan ɗan'uwan ki ne ko?"

Gyaɗa masa kai kawai ta yi ba ta yi magana ba, Abdul da duk jikinsa ya yi sanyi ya iso ya samu waje ya zauna a ɗaya daga cikin gadajen da ke ɗakin, shi ma Doctor Hashim ya zauna a kusa da Abdul. Sai da Doctor Hashim ya ƙare musu kallo sannan ya ce "Ƙanwata zo ku zauna mana." Ya faɗa yana murmishi haɗi da mamakin Zaiyan.

Zama ta yi a bakin gadon ganin haka ya sa shi ma ya biyo bayan ta ya zauna a ƙasa kusa da ƙafafuwanta yana sa yatsu biyu a bakinsa, kallon shi ta yi cike da tausayi ta ce "Zaiyan tashi mana ka zauna a nan." Ta nuna masa kusa da ita. Murmushi ya sakar mata har sau da dimple ɗinsa ya lotsa haƙoransa suka bayyana wushiryar da ke tsakanin haƙoran na gaba da na ƙasa ta bayyana, baki ta saki tana kallon shi cike da mamakin ganin dimple a kumatunsa, saboda ita duk haɗuwar da take da shi ba ta taɓa lura yana da dimple ko wushirya ba sai yau ɗin nan. Takalmin ƙafarta ya shafo yana ƴar dariya ya ce "Anty bredi ne kika kawo min?" Ya faɗa yana ƙara shafa takalmin wanda yake irin mai laushin nan ne na yawo a cikin gida.

Murmishi ta yi ta ɗago kai ta kalli su Abdul wanda su ma ita suke kallo suna mata dariya, cikin dabara ta saɓule takalmin daga ƙafarta ta janye ƙafar ta sunkuya ta ɗauki takalmin sai shi ma ya yi saurin miƙewa tsaye yana kallon ta, ɗage gira ɗaya ta tana jin wani irin sanyi na ziyartar ta ta ce "Ka ga zauna a nan da na nuna ma." Ta kuma faɗa tana nuna masa gefenta.

Ɓata fuska ya yi ya ce "Ni to ki bani bredin na ci." Ya faɗa yana saɓa baki.

Dariya Doctor Hashim ya yi ban da Abdul da ya yi shuru yana kallon ikon Allah da jinjina girman Ubangiji, wai kamar wannan sabcecan saurayin ne yake yin Shagwaɓa irin ta yara ƙanana, lalle Allah shi ke tsara wa bawansa rayuwar da yake son ya yi a dauron duniya. Ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Hashim, yanzu meye mafita a kan lamarin bawan Allah nan?"

"E gaskiya ne meye mafita."

Zaiyan ya faÉ—a yana jujjuya takalmin.

Girgiza kai Abdul ya yi yana kallon fuskar Abir da ya hango murmushi bayyana a fuskarta ta, wani sanyi ya ji ganin yau ta saki ranta wanda rabon da ta yi murmushi tun kafin ma a kawo gawar Abie.

Tashi ya yi ya É—auko wata paper wanda take É—auke da duk abin da ya shafi rashin lafiyar Zaiyan, zama ya yi ya buÉ—e ya fara yi musu bayani..

"Ku yi haƙuri ranar kwana ukun Abie wani mutum ya zo nan yake sanar da ni wai shi ɗan'uwan Zaiyan ne yana so zai tafi da shi Kano, to ni kuma kawai sai na ji ban yarda ba da shi na ce masa ba zan iya ba shi Zaiyan su tafi ba har sai wanda suka bani amanar shi sun zo sun ce na ba shi zan yarda na ba shi. Mutumin nan ya dage sai na nuna masa ɗakin da aka kwantar da shi ni kuma na ce ban san maganar ba, ƙarshe na so na kira number ka na sanar da kai komai sai na tuna ranar kuna cikin jama'a, shi ne na kira Sajan ɗin Office ɗinku na sanar da shi ga abin da yake faruwa ya ce ga shi nan zuwa. Kafin na gama wayar tuni ya gudu ya bar ni a wajan na yi ta duba shi amma sam ban gan shi ba, hakan ya sa na sa aka ƙara sa idanu a ɗakin da yake ƙarshe ma na kai shi wani ɗaki wanda ba kowa ake kaiwa ciki ba."

Da sauri Abdul ya kalli Doctor Hashim yana gyaÉ—a kai, ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Hasashena ya fara zama gaskiya, tabbas akwai abin da ba daidai a cikin lamarin nan." Ya faÉ—a yana tuna abubuwan da suka kulle masa kai a baya yanzu a hankali yana samun mafita.

"To in kuwa haka ne Yaya mai zai hana mu É—auke shi mu tafi da shi gidanmu." Abir ta faÉ—a tana kallon Zaiyan da ya kamo mayafinta yana wasa da shi.

Doctor Hashim ya gyara zama ya ci gaba da cewa "Bayanin abin da ya shafi rashin lafiyar sa ya kamata mu ba wa muhimmanci in ya so kai Abdul sai ka ji da sauran."

Jinjina kai kawai Abdul ya yi bai ce komai ba ya yi shuru.

"To Yaya Hashim yanzu wani magani za ku ɗaura shi a kai wanda zai ci gaba da sha kafin wani lokacin mu ga mai Allah zai yi." Ta faɗa tana janyo mayafinta rabi ta rufe ƙirjinta rabin kuma ya riƙe gam yana naɗawa a hannunsa yana warwarewa.

"Kwarai kuwa da gaske ni nasan komai zan saya miki takalmi Anty, na kawo miki bredi ki ci?" Zaiyan ya tari numfashin Doctor Hashim da Ke shirin yin magana..

Ɓata fuska Abir ta yi tana kallon shi cike da tsananin tausayi, kuka take son yi ko za ta ji sassaucin abin da take ji a gangar da ruhinta amma ta yi ƙoƙari ta danne kuka sai sauke ajiyar zuciya take.

"Gaskiya ciwon nan nashi ya kai matakin ƙarshe, amma duk da haka ba ta ɓaci ba da izinin Allah sai ki ga an dace ya ji sauƙi. Akwai wani Abokina da can Amerika zan sa ya turo min da wani magani, wanda nake kyautata zaton in sha Allah zai ji sauƙi in kuka saya masa shi yana sha. Wannan raunin na hannunsa da na kunce mi shi ɗaurin sai kawai na ga babu shi babu alamar sa, na yi mamaki matuka saboda wajan an sa wani abu mai tsinin gaske an huda kuma ba wai huda ƙarama ba."

Da sauri Abir ta kalli Zaiyan ta ɗago hannun nasa ta ga babu komai, saurin ja da baya ta yi tare da jafe ƙirji ganin ɗayan hannun wasu ƙuraje ƙanana sun cunkuso masa. Baki na rawa ta ce "Yaya ka ga dibi wasu ƙuraje da suke fito masa a hannu."

Doctor Hashim ne ya miƙe ya ce "Karku damu da wannan zan rubuta muku wani pharmacy sai ku biya ku saya kuke shafa masa."

Ajiyar zuciya ta sauke ta gyara zama ta ce "To yanzu ka nuna masa maganin mu gani ko ya ka ce Yaya?" Ta ƙarasa maganar da tambayar Abdul.

"Haka ne Baby, yanzu ya kamata mu É—auke shi tun kafin wanda ya zo É—aukan shi ya dawo ya sace shi ba ku sani ba." Ya faÉ—a yana tashi tsaye.

Hararar shi Doctor Hashim ya yi yana faÉ—in "Haba dai Aboki ya zan yi sake wani ya shigo har Asibitin nan ya sace shi?."

Hararar shi ma Abdul ya mayar masa ya ce "Malam kawai ka yi abin da na ce." Ya faÉ—a yana isa inda suke ya dubi Zaiyan ya ce "ÆŠan'uwa tashi mu tafi gida."

Maƙale kafaɗa ya yi yana cuno baki gaba ya kalli Abir ya ce "Anty wai ya ce min ɗan'uwa mu tafi gida?" Ya faɗa yana nuna Abdul da hannu irin yadda yara suke in za a ɗauke su daga wajan iyayensu in ba su so.

Tashi ta yi tsaye shi ma ya tashi yana riƙe da mayafinta ta kalle shi ta ce "E ɗan'uwanka ne ko ba ka so ka je gida ne?"

Saurin kallon Abdul ya yi sai kawai ya yi dariya ya ce "To ina rawanina yake?"

A yadda Abdul yake da saurin fusata bai fusatar ba sai ya girgiza kai kawai yana tausayawa Zaiyan, kamo hannunsa ya yi ya ce "Shi ma yana gida muje sai a ba ka." Sake maƙale kafaɗa ya yi ya ƙara komawa bayan Abir kamar wanda ya ga abin tsoro, ganin haka ya sa Doctor Hashim yin ƴar dariya ya ce "Ƙanwata in fa ba ke kika ce masa ku tafi ba, to fa sai dai ku yi ta tsayuwa a nan."

Ajiyar zuciya ta sauke ta dube shi ta ce "Zaiyan muje gida ka ji zan ba ka rawanin naka in mun je."

Da murna ya fito ya ce "Babba fa nake so wanda zai kai haka." Ya faÉ—a yana yin faÉ—i da hannayensa. To kawai ta ce masa suka fita mayafinta rabi a hannunsa Abdul na biye da su a baya har suka fito harabar Asibitin, sai da Doctor Hashim ya ga tafiyar su sannan ya koma ciki..

Suna cikin tafiya a hanya ya dami Abir da yunwa yake ji zai ci abinci, jin haka ya sa Abdul samun wuri ya taka birki a gefen titi ganin wasu masu abinci. Har zai fita kuma sai ya fasa yana tunanin ya wuce ajin ya sayi abincin bakin hanya ana ganin shi da kima da daraja a cikin gari. Kallon shi ta yi ta ce "Yaya lafiya dai ka tsaya?"

Girgiza kai ya yi ya ce "Dama shi zan sayo wa abinci sai kuma na ga hakan bai dace da ni ba."
Chapter 24 · 0% Book details