Sashe 25
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Murmushi ta yi ta ce "Yaya ka rabu da shi kawai, indai maganar cewa yunwa yake ji ne abin ya zame masa jiki ko abinci yake ci za ka ji ya ce yunwa yake ji zai ci abinci." Dafe kai ya yi ya ja motar suka wuce...
Sai da suka kusa zuwa gida ya tuna bai fa sanar da kowa ba za su kai Zaiyan gidan, hannu É—aya yasa ya É—auko waya ya danna wa Abba kira, bayan ya É—auka suka gaisa nan ya soma masa bayanin komai.
"Abba dama mun É—auko Zaiyan ne za mu kawo shi gida, amma ya kake ganin za ayi da shi? Mu kai shi nan gida ko mu kai shi É—ayan gidan a samo mai kula da shi?"
Daga cikin wayar Abba ya nisa yana aje borrow da ke hannunsa ya ce "Yanzu dai ku fara zuwa da shi nan in ya so sai mu yi shawarar abin da ya dace, zan kira Kabir da Jabir sai a zauna ayi maganar da an jima in mun dawo gida." Godiya ya masa sannan suka yi sallama.
Suna isa gida ya fito yaran sa suka sara masa ya É—aga musu hannu, Abir ta fito daga motar ta zagaya ta buÉ—e masa sai kawai ta ga yana bacci, ta kalli Abdul da ya yi tsaye yana jiran ta ta ce "Yaya bacci fa yake yi."
Yaran sa ya yi wa nuni da cikin motar, mutum biyu suka iso bakin motar suka buÉ—e tare da É—auko shi suka nufi ciki..
Yasmin da ke tsaye ita da Fatima za su fita suka ga an É—auko kyakyawan namiji sai suka cika da mamaki, Fatima ta fara cewa "Anty Yasmin ko dai wancan shi ne mahaukacin da aka ce yana Asibiti wanda ya taimaki Baby?" GyaÉ—a kai ta yi itama ta ce "Tabbas wannan shi ne mu koma mu faÉ—a wa Mami kin ga Abba ya kusa dawowa sai muje mu gani da idanunmu."
Juyawa suka yi da hanzari cike da zakuwar son ganin kamannin Zaiyan suka faɗo palo, Mami da ke waya ta zabura jin an faɗo palon ba sallama, ganin su Yasmin ne sai ta daka musu tsawa tana zagin su su kuma sai kumbura baki suke. A fusace ta ce "Wallahi Yasmin sai na ci ubanki in Kuka sake shigo min waje ba neman izini." Ta nuna su da hannu kamar za ta kai musu duka. Tana kumbura ta soma magana ƙasa-ƙasa ta ce "Mutum shi ba shi da aikin komai sai yin waya da an zo kuma ya hau mutane da faɗa. "
"Magana kike ne?"
Saurin cewa ta yi "A a ban ce komai ba." Sake tsare gida Mami ta yi ta ce "Me kuka ji ina faɗa da kuka shigo? Sannan wa ya ce ku dawo bayan kun ce min za ku gidan ƙawar Yasmin?" Ta jero musu tambayoyi.
"Mu babu abin da muka ji , kawai dama mun dawo ne dan mu ce miki mun ga an kawo wannan mahaukacin da aka ce yana Asibiti. " Fatima ta faÉ—a tana kallon Mami.
Dafe ƙirji Mami ta yi cikin zare idanu ta ce "What? Mahaukacin ne aka kawo mana cikin gida dan ya kashe mu? To ni kan babu inda zan fita."
Dariya Fatima ta yi sanin halin Mami da mugun tsoron mahaukaci ta ce "Ina jin fa har yanzu bai farfado ba daga sumar, dan yanzu ma sai da aka ciccibe shi aka shiga da shi part É—in su Baby." Ajiyar zuciya Mami ta sauke ta ce su zauna in Abba ya zo za su ji komai a bakin shi...
Suna shiga Grandma ta miƙe za ta kwasa a guje Abdul ya yi saurin cewa "Grandma tsaya su IB ne fa."
Dafe ƙirji ta yi tana mayar da numfashi ta koma ta zauna ba ta ce komai ba har suka kwantar da shi a kan doguwar kujera suka fita, sai a lokacin ta samu damar sauke hannayenta da ta ɗaura sun da ta yi a ƙirji ta kalli Zaiyan da yake ta bacci, a sanyaya ta ce "Amma kai kuwa Abdul ina gaf da cin ubanka a gidan nan, taya za ka shigo mun palo da gardawan maza sun yi ɗamara?" Ta faɗa tana hura hanci.
Murmushi Abir ta yi ta dawo kusa da Grandma ta zauna tana faɗin "Grandma yau dai ga wanda ya taimake ni mun kawo shi har gida." Saurin kallon shi Grandma ta yi ta miƙe ta iso ta tsaya a daf da kujerar ta zuba masa idanu tana kallon shi, ba zato suka ga tana goge hawaye ta zauna a ƙasa, Abdul ya ce "Grandma kukan fa da kike na mene ne?"
"Kayya É—an nan! Bar ni na yi kuka, ji na yi yaron nan ya bani tausayi ya kuma shiga raina, ga mutum har mutum amma babu hankali Allah ya ba ka lafiya ya ma sunanshi?" Ta faÉ—a tana waiwayen Abir. Muskutawa ta yi sannan ta ce "Sunanshi Zaiyan ne."
Jinjina kai ta yi tana faÉ—in "Allahu akbar."
Jin ana kiran Sallar La'asar yasa Abdul ya miƙe ya shiga ɗakin Mommy ya sanar da ita sun zo da Zaiyan zai fita a kula da kyau kar ya gudu, da to ta amsa sannan ya fita..
Tare suka dawo da su Abba har da Daddyn Aruf da Salim suka zarce part É—in Mommy. Da Sallama suka shigo ciki aka amsa musu suka zauna, Abba ya yi tsaye yana kallon Zaiyan da ke ta bacci fuskarsa É—auke da murmushi, wata irin faÉ—uwar gaba ya ji ta ziyarce shi ya yi saurin zama a gefen kujerar da ke kusan tashi yana sauke numfashi. Sai da suka zazzauna sai ga su Mami sun hallara, bayan kowa ya yi shuru Abba ya ce "To yau dai ga wanda ya taimaki Mamana an kawo shi, dan haka muna so mu ga inda ya dace a aje shi a ci gaba da masa magani."
Mommy ta nisa ta ce "Allah sarki bawan Allah! Ubangiji ya ba shi lafiya mai ɗaurewa, amma ni a ganina da an gyara wancan ɗaki a saka shi a ciki tun da yana da ƙofa daga waje, inyaso sai a samo wanda zai ke kula da shi kafin mu ga abin da Allah zai yi." Ta faɗa tana kallon shi ganin yana motsawa alamar zai farka.
Daddy ya ce "Kuma fa kin kawo shawara matar Yaya, amma mai kaku gani za ayi." Ya faÉ—a yana kallon Abba da Daddyn Aruf. Abba ya ce "Kawai ayi haka."
Jin abin da ya faÉ—a Daddyn Aruf ya ce shi ma abin da yake son faÉ—a kenan, kawai yanzu a samo mai kula da shi. Mami ta yi caraf ta ce "Ba shakka! Wato mu saboda ba a É—auke mu a zaman mutane ba shi ya sa ba a ji ta bakinmu ba ko?"
Abba ya zuba mata idanu ta wani masge tana harare-harare Umma ta amshi zancen da cewa "Ato gane mini hanya, makaho ya zo gulma! Yanzu da Mahaukaci kamar wannan sabcecan saurayin za mu zauna gida ɗaya? Mu je muna bacci cikin dare ya lallaɓa ya kashe mu ko ya tsinna mana wuta mu ƙone."
Daddyn Aruf da yake ya fi su saurin fusata ya ce "Last warning! In ba a saka ku ba cikin magana kar ku yi wa mutane magana indai ba alkhairi za ku faÉ—a ba, na ga dai ba a part É—in ku za a aje shi ba a na mahaifiyarmu ne ko?" Ya faÉ—a a fusace kamar zai kai musu duka. Murmushi Abba ya yi ya kalli Abdul da shi ma Daddyn Aruf yake kallo yana murmushi ya ce "Ka ga Jabir rabu da su mana, su za su faÉ—a mana yadda za mu tafiyar lamuran familynmu?"
Abdul ya gyara zama ya ce "Abba duk ku bari ni nasan me zan yi a kai." Ya faÉ—a yana haÉ—e rai dan kar ma wani ya ce masa me ya sa.
Zai sake magana suka ga Zaiyan ya tashi zaune yana mutsitsika idanu, ganin mutane dayawa a palon sai ya waro idanunsa da bacci bai gama sakin su ba, kallon ko'ina yake a palon sai ya yi murmushi, saurin zuro ƙafafuwansa ya yi fuskarsa na nuna alamun tsoro ya ce "Ƙundun uban can! Alkur'an na zo faɗa." Ya yi maganar yana hilla ƙafarsa kana dariya. Kowa shuru ya yi ba wanda ya tanka masa har ita oganninyar ta zuba masa idanu, ganin ba su ce komai ba ya kuma cewa "Nan masarautata ce ko?" Ya shafa kujerar da yake kai yana murmushi.
Yasmin ta ce "Wow! Ke Fatima kalli ki ga Wallahi mahaukacin nan da yana da hankali handsome boy za a yi a wajan nan, dubi dimple ɗinsa har ma da wushirya gare shi." Ta ƙarashe maganar tana ƙara yin ƙasa da murya dan kar Abdul ko Abba ya ji su.
Fatima ta ce "Ai kuwa dai duk da ba a cikin sutura mai kyau yake ba, amma Wallahi ya haÉ—u sai dai rashin hankalin dai, maza É—auko mana video shi kar Yaya Abdul ya gani."
Saurin saita wayarta ta yi ta rakube a bayan Yasmin kamar mai chatting ta dinga É—aukar shi video.
Zaiyan ganin ba su ce masa komai ba sai ɓata fuska kamar zai yi kuka ya ce "Anty." Jin abin da ya faɗa sai Grandma ta ce "To wace ce kuma Anty?"
Kallon Grandma ya yi sai ya tashi ya nufo ta , saurin maƙalewa ta yi a jikin kujera tana faɗin "In yana duka kar ku bari ya iso inda nake." Abdul ya gumtse dariyarshi yana kallon Grandma har ya ƙaraso kusa da ita ya zauna a ƙasa sai gani suka yi ya saka kuka, dariya Yasmin ta yi Abba ya harare ta sai ta yi saurin rufe baki.
"Mama ina Anty?" Ya tambayi Grandma.
Abir ta leƙo da kanta daga gefen shi ta ce "Gani nan ba ka ganni ba?" Jin muryarta sai ya yi saurin juyowa inda ya ji muryarta suka haɗa ido, dariya ya yi ya ƙara matsowa kusa da ita ya ce "Anty bredi fa ba ki bani ba."