Sashe 39
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Girgiza masa kai Abdul ya yi yana miƙewa ya ce "Gaskiya da wahala dan yau aka kai shi Asibiti sai zuwa gobe za a dawo da shi, in za ka kai gobe to zan iya kaika ka gan shi."
Numfashi ya ja ya ce "OK to ba damuwa zan kai goben in sha Allah dan na gan shi, yanzu ayi min iso na gaishe da su Mom." Iman da Hafsat suka fita dan sanar da Mom zai shigo, bayan Iman ta dawo ta ce zai iya shiga suka miƙe su duka suka nufi palon su Grandma..
A sallama suka shiga Mom da grandma suka amsa musu, durƙusawa ya yi cikin ladabi ya soma gaishe da su, suka amsa masa cikin sakin fuska. Abir ta yi murmushi ganin Mom na kallon shi ta ce "Mom yana kama da Zaiyan ko?"
"Kwarai ma kuwa sosai suke kama?." Cewar Mom tana kallon shi.
Murmishi kawai ya yi wato dai in ya fahimta kowa kallon nasa da yake na kamannin shi da Zaiyan ne, tashi ya yi ya musu Sallama ya ce zai koma masaukin shi. Grandma ta riƙe baki ta ce "Haba dai ɗan nan, ka taso tun daga wata ƙasa ka zo wajan jikata kuma ka ce wai a hotel za ka kwana? Ai ka zauna a gidan nan za ka kwana ba in da za ka je." Ta gutsiri goron da ta kunce a leda ta ci gaba da magana "Ni ce nan Uwar ubanta ba ka ga muna kama da ita ba?"
Murmushi Suhal ya yi ya ji grandma ta birge shi, amma ba zai iya kwana ba a gidan su dan haka ya dubi Grandma ya ce "Allah sarki Kaka, ai da yau ma zan tafi zuwa dare, to na fasa ne saboda ban sani ba ko zan haɗu da wanda za mu yi meeting da shi ƙarfe huɗu da rabi, in ban samu mun haɗu ba dole na kwana."
Gyaɗa kai ta yi tana miƙe ƙafarta ta ce "To kai ko yaro daga wani gari kake a ƙasar Niger ? Sannan su waye iyayenka?"
Saurin kallon ta Abdul ya yi jin maganar da ta yi, ya daga zuwan baƙo sai tambayar su waye iyayenshi ? Murmushi ya kuma yi zai yi magana suka ji sallama su Abba, amsa musu suka yi suka ƙaraso ciki suka zauna. Suhal cikin ladabi ya juya gefen su Abba ta soma gaishe da su, cikin fara'a suke amsa mishi suna masa barka da zuwa yana sunkuyar da kai.
Grandma ta sake maimaita maganar da ta yi yanzu ganin za a manta, har Abba zai yi magana sai kuma ya fasa, Suhal ya ƙara sunkuyar da kai ƙasa ya soma musu bayanin asalin shi a takaice..
"Suna na Yarima Suhal Abdulwahid, mahaifina shi ne sarkin garin Niamey a yanzu ni ne ɗan shi na biyu, mahifiyata mu biyu ta haifa ni fa ƙanwata Ilikima, sauran kuma yaran abokiyar zaman Mamana ne." Ya ɗago ya kalle su jin sun yi tsit kamar ba kowa a palon, kowa ya ga shi yake kallo sake da baki fuskokin su na nuna tsananin mamaki, murmushi ya yi dan ya san dama za a rina dole su yi mamakin hakan, ci gaba ya yi da magana..
"Dama ƙarfin zuwa na Nigeria dan na zo gidan su Princess na ganta a zahiri itama ta ganni na kuma gabatar da kaina a gare ku."
Da wani irin sauri Abdul ya ɗago ya kalle shi, Salim ya riƙe baki ya ce "Ka gabatar da kanka kuma? Ka mana yadda za mu gane."
Numfashi ya ja sannan ya ci gaba "E kamar yadda na ce zan gabatar da kaina ga iyayenta." Ya É—ago ya kalli Abba da shima shi yake kallo ya ce "Abba ina neman izinin auren princess."
A zabure ta kalle shi ya juyo shi ma ya zuba mata idanu, wani irin bugu ƙirjin ta yake yi saboda ruɗewa, kenan dama Suhal dan sarki ne bai taɓa faɗa mata ba? Abdul kuwa kasa cewa komai ya yi, da ya yi niyar magana amma kalmar neman auren da Suhal ya faɗa ita ta tokare masa maƙoshi nan da nan ya bushe, wani irin tafasa zuciyarsa ke yi haɗi da wani kalar azababben zafi wanda yake jin shi har tafin ƙafarsa..
Grandma ta gyaɗa kai ta nisa ta ce "To amma kai kuwa yaro dama ka taɓa haɗuwa da ita ne? Ko kuwa sai yau ka ganta?"
Girgiza kai ya yi ya ce "Inna ai princess ba ta taɓa ganina ba sai a photo shima ɗaya ne wanda ya jima da yi, ƙanwata Ilikima kawai ta sani dan har gaisawa suna yi sosai, ta sha nacin na turo mata photona amma sai na ce mata ai ni bana photo da kyar na turo mata ɗaya shi ma na yayana ne na turo mata. Ta sha tambaya na ƙara turo mata Photona sai na ce ban samu na yi ba, da haka nake mantar da ita zancan, na kuma ce kar Ikilima ta tura mata in ta nema a wajan ta tun tana mita har ta gaji ta daina tambaya, ni kuma ina da photonta a wajena hakan yasa ba ta taɓa ganin fuskata ba ina daidai wannan shekarun, sai yau da ta ganni har take cewa muna kama da wani majinyacin su. Abba in har ka bani izini in na koma gida zan sanar da Babana ya turo ku yi magana."
Shuru Abba da Daddy suka yi suna nazarin maganar shi, sai can Abba ya yi ƙarfin halin cewa, "Suhal ita Maman nawa ta san kana son ta?"
Girgiza kai ya yi hakan ya ba wa Abba damar ci gaba. "To ka nemi soyayyar ta in har ta amince tana sonka mu ba mu da matsala, amma ka sani Æ´armu tana da lalura za ka iya auran ta a haka?".
Saurin ɗaga kai Suhal ya yi cikin wani irin farin ciki ganin ya soma samun ƙwarin gwiwa ya ce "Abba ai Princess ko guguwa ce zan aure ta kuma na kula da ita na daraja ta, ta faɗa min cutar asma gare ta ba ta son hayaƙi da duk wani abin da zai sa ciwon nata ya tashi."
Lumshe idanu Abdul ya yi sai yanzu ya ji ya É—an samu sassauci a zuciyarshi, ko ba komai Suhal na son Abir da gasken gaske. Daddy ya yi murmushi ya ce "Mu yanzu abin da zamu ce kawai Allah ya tabbatar mana da alkhairi, ka je ku daidai kanku kai da ita in ta amince sai mu mu shigo lamari."
ÆŠadi sosai ya mamaye zuciyar Suhal, a nutse ya ce "Na gode sosai Baba."
Abba ya dubi Abir ya ce "Mamana shin kina son shi?" Shuru ta yi ba ta ce komai ba, ita yanzu me za ta ce akan hakan saboda ba ta taɓa masa kallon so ba, sai da Abba ya sake maimaitawa ta ɗago ta kalle su ta ga duk ita suke kallo amma ban da Abdul, tashi ta yi da sauri ta bar palon ta nufi ɗakinta.. Da kallo suka bi ta Daddy ya ce kawai ya nemi soyayyar ta in ya samu su ba su da matsala za su yi bincike a kan shi, cikin jin daɗi ya musu sallama zai koma Abdul da Salim suka fito da shi dan su masa rakiya.
A bakin mota ya juyo ya kallo Abdul da ya É—aure fuska kamar haÉ—arin da ya so zubo ruwa, É—an murmushi ya yi ya ce "Yaya Abdul don Allah ka shayo min kan princess Wallahi in ta ce ba ta sona zan iya rasa raina."
Saurin kallon shi Abdul ya yi cike da mamaki, kenan in mace ta ce ba ta sonka sai ka mutu kamar wata ɗiyar roba? Wani haushi ya ji ya ba shi ji yake kamar ya shaƙe shi saboda ya ce wai son Baby yake amma ya danne bacin ran ya ƙirƙiro murmushin yaƙe wanda ya fi kuka ciwo.
Ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Karka damu Suhal, ai indai Baby ce za ta ma soka in sha Allah." Godiya ya musu suka yi musahaba ya shiga mota ya tafi..
A fusace Abdul ya dawo ciki inda ya samu palon sai Iman da Hafsat suna hira, tsaki ya ja ganin yadda Hafsat ta tashi tana masa wani irin kallo ta ce "Yaya Abdul ba ko magana ma?"
Bai kula ta ba ya juya ya nufi part din su yana tafiya yana jan tsaki kamar jikan tsaka.
Iman ta dawo part din su Umma da tun da aka ce mata wani ne ya zo wajan Abir ta kasa zaune ta kasa tsaye ganin dalleliyar motar da ya zo da ita, ba ta ƙara ruɗewa ba ma sai da Iman ta ba ta labarin daga a har z tana yi tana murna Abir za ta auri dan sarki. A fusace Umma ta ce "Kut! Yaranmu suna nan duk sun fita komai amma ya ce sai ita yake so? To Wallahi ba zai yiyuba." Fuuu ta wuce ɗaki Iman ta bi ta kallo tana girgiza kai, ita ta ɗauka faɗa matan da ta yi za ta yi murna ne tun da kullum cewa take ba ta son ganin ta a gidan yanzu za ta bar gidan ai sai ta yi murna ba ta fusata ba. Sunkuyawa ta yi ta ɗauke parantin da Umma ta jero abinci ta kai kitchen ta dawo ta wuce ɗakinsu..
Daret masaukin shi ya nufa cike da zallar farin ciki. Yana isa wanka ya yi ya gabatar da Sallar La'asar wadda tun a hanya ya ji ana kiran Sallah, abinci ya yi magana aka kawo masa mai rai da lafiya ya ci ya ƙoshi sannan ya ɗauki computer shi ya soma duba saƙonni, sai da lokacin da zai fita su hadu da wanda za su haɗu ya yi ya rufe computer. Wanka ya sake ya saka ƙananan kaya farare da baƙar cap ya feshe jikin shi da turare masu ƙamshi ya fita..
Sai kusan karfe 11 ya dawo hotel É—in a gajiye dan sun sha meeting sosai, abinci ya sa aka kawo masa ya ci ya koma kan gado ya janyo computer shi ya soma rubutu a wata number..