← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 120

Sashe 77

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da hanzari ya tashi ya dauke ta ya nufi gidan ƙasa, stap bibiyu yake tsallakewa sai ga shi a palon ya zarce ɗaki ya kwantar da ita, inda kayan aikinsa suke ya nufa ya dauko abin gwaji ya soma gwada ta. Da farko taƙi ya taɓa ta ganin yana son cire mata rigar jikinta har sai da ya lallaɓata ta yarda ya zarge zip ɗin rigar. Bayan ya gama ya dauko allura ya ja ruwa ai kuwa tana ga allura ta zabura za ta gudu ya damƙo ta ya matse, kuka take tana ƙoƙarin kwacewa amma ta kasa saboda da yadda ya riƙe ta bai mata da wasa ba, ya tsira mata allurar ta ƙanƙame shi tana fadin "Mugu azzalumi." Sai da ya gama mata ya yi murmushi ya ce "Raguwa kawai, ke ba ki da lafiyar ma ba za ki daina rashin kunya ba?" Murguda masa baki ya yi tana kai masa duka ya kauce yana murmushi, tana cikin yi masa mita ta ji amai ya tafo mata ta yi saurin tashi daga jikinsa ta soma ƙoƙarin sauka a gadon, da sauri ya kamo ta a zaton shi gudu ne za ta yi. Raurau ta yi tana dafe kirji ta rufe bakin amma yaƙi sakin ta kawai ta miko kanta bakin gadon ta shiga kwara amai kamar za ta amayar da kayan cikinta.

Sai da ta gama yana riƙe da ita sannan ya dauke ta ya yi toilet da ita, wanka ya mata tana kuka tana ce masa ba shi da kunya shi kuma ya ce ya ji ɗin da haka suka fito. Shiryata ya yi a cikin wasu riga da wando masu kauri pink color kayan sun yi matuƙar dacewa da farar fatarta, mai ya shafa mata duk tana lafe a jikinsa tana masa mita yana rarrashin ta da haka ya shafe ta da mai ya dauke ta ya bi ta gefen da babu aman ya kwantar da ita tare da lulluɓe ta a wani tattausan blanket. Wajan ya shiga gyarawa wayarsa da ke gefen Iman ta soma ringing, bai bi takan wayar ba ya ci gaba da abin da yake amma hankalinsa na kan ta duk motsin da ta yi akan idanuwansa. Sai da ya gama gyara ko'ina sannan ya hayo gadon ya dauki wayar, ganin Mai martaba ne ke kira sai ya kalli Iman yasan dalilin kiran ba zai wuce na abin da ya yi wa Fauziya ba, dogon tsaki ya ja baya son ya tashe ta ganin ta fara bacci amma ba yadda ya iya ya yaye blanket ɗin ya dauki hijab ya sanya mata ya dauke ta suka fito..

A tsaye ya ga Jakadiya tare da Ikilima ya dire Iman, sai a lokacin ta buɗe idanuwanta ta ganta a palon Mamma ta ɗan gyara tsayuwa tana kallon Ikilima da ta haɗe girar sama da ƙasa.

"Ranka ya daɗe Mai martaba yana son ganin ka a ɓangarensa."

Kallon Iman ya yi da take lumshe idanu ya ƙara daure fuska ya dawo da kallon shi kan Jakadiya hakan ya sa ta yi gaba da sauri, a baya suka bi ta zuwa kiran Mai martaba yana riƙe da ita suna tafiya a hankali har suka isa ɓangaren Mai martaba..

_NIGERIA_

Tun safe Abir da Zaiyan suke harabar gidan suna ta wasa, ƙasa ya kwaba ta biye masa suka yi gida duk sun ɓata jikinsu.

Sai da suka gama komai ya kama ƙugu sai kuma ya zauna a gaban gidan ya ce. "Anty wannan shi ne dakinmu." Ya faɗa yana nuna mata ɗaki da toilet da shi da kansa ya yi, murmushi ta yi ya nuna dakin na gaba ya ce. "Wannan kuma na Baba da Inna ne, ɗayan kuma in na sayo ɗiya mai kyau irin ta kallo-kallon palon Inna zan aje ta a wannan ɗakin." Ya faɗa yana karkaɗe hannunsa a jikin rigarsa.. Ƴar dariya ta yi tana kallon inda ya ce na ɗiyar da zai samu musu ne, ganin ta yi shuru ya zagayo ta bayan ta ya rungume ta yana sauke numfashi ya ce "Anty zan ci abinci." Lumshe idanu ta yi tana jin saukar numfashinsa na sauka a dokin wuyanta, ajiyar zuciya ta sauke da kyar ta ce. "To tashi a jikina muje ciki sai na zuba ma abincin." Ta faɗa tana miƙa hannu ta tabo fuskarsa. Dagata ya yi ya tsaya yana jiran ta tashi, mikewa ta yi tsaye ta ji ƙaran hon sai ta cika da mamakin waye yake musu hon? Maigadi ya buɗe masa get ya shigo ciki tare da paka motar, shuru Abir ta yi tana kallon motar gaban ta na dukan uku-uku ganin wanda ya shigo, shin me ya zo yi a gidan nan? Ko dai cin mutumcin da sama yi mata ne ya biyo ta har gidanta zai mata? Sunkuyar da kai ta yi ganin ya fito ya nufo inda suke. Wani kallon banza yake watsa mata ya tsaya a gaban ta tare da jan tsaki ya ce. "Ke!"

A firgice ta É—ago ta kalle shi fuskar nan babu alamar rahama a tattare da shi, nusunawa ta yi cikin É—auri-É—auri ta ce "Yaya barka da zuwa."

Bai amsa mata ba sai tambayar da ya jefo mata, "Baby ina ma'adanar bayanan da kika dauka a kayan Abie? Sannan ina takardar da ke wajan ki?" Ya faÉ—a cikin tsawa-tsawa.

Cikin rashin fahimta ta É—ago kai ta kalle shi ta ce "Yaya wacce takarda da ma'adanar bayanai kake magana?"

A tsawace ya ce "Ok tambaya ta ma kike saboda ba ki da kunya?"

Nan-da-nan idanunta ya cika da kwalla ta rausayar da kai ta ce "Wallahi ni Yaya ban san akan wata takarda kake magana ba." Iya fusata Abdul ya fusata jikinsa har tsuma yake ya daka mata tsawa ta ja da baya a ruɗe, biyo ta ya yi ya sabga mata mari cikin ƙaraji ya ce. "Ina takardar da kika dauka? Za ki fito min da su ko sai na miki dukan tsiya?"

Dafe kunci ta yi a gigice ta yi baya za ta faÉ—i ta ji an tare ta ta faÉ—a kan wani abu.....

_Maman Nusaiba_

[11/18, 9:28 Yamma] Anty Sarat (Mom Nusy 🌹): ~A HAKA NAKE SON SHI~

*Bonus fage*

Shafi na (38)

Runtse idanu ta yi sai ta ji ya ɗago da ita yana huci, a hankali ta buɗe idanu ta sauke shi akan shi yana kallon Abdul da ya yi tsaye a gaban su yana hura hanci. A fusace Abdul ya tako ya iso gaban su cikin ba da umarni ya miƙa hannu tare da cewa "Maza bani kafin na kakkarya ki."

Matsawa Zaiyan ya yi ya koma gefe ya yi shuru yana kallon su, ganin ya saki hannunta ta ja da baya tana girgiza wa Abdul kai ganin yana ƙara kusanto ta, hakan da ta yi ya ƙara tafasa masa zuciya iso ya damƙo ta ya tura ta can ta yi baya ta faɗi akan hannunta.

Ƙara ta ƙwalla tana birkitowa ta juya cikin tsananin azaba, ganin ya sake yowa kanta ta dinga ja da baya tana fashewa da kuka, ganin shi take tamkar zaki sai rawa jikinta yake, hannu ya miƙa mata ya ce "Idan na ƙyirga uku ba ki ba ni takardar nan ba sai na kashe ki na kashe banza a wajan nan." Ya faɗa yana sake kai mata duka ya ji an yi carab da hannun nasa. Da mamaki yake kallon Zaiyan da jijiyoyin kansa suka tashi idanuwansa suka yi jajur kamar an ɗiga masa jini, wani kalar huci yake fitarwa yana ƙara matse hannun Abdul ya sa ɗayan hannun ya kai masa naushi a baki, nan take bakin ya fashe sai jini ya dinga biyowa ta gefen bakinsa. Idanu rufe ya ƙara murda hannun Abdul sai huci yake ya tsare Abdul da idanu, Abdul jin azaba ta mamaye shi ya ɗaga hannunsa ɗayan ya kai wa Zaiyan naushi nan ya yi caraf da hannun, baya-baya ya dinga tura Abdul har sai da suka isa bishiryar mangwaro ya jingine shi yana fadin "Me ta maka kake dukan ta? Yau sai na maka duka tun da ka daki Anty." Ya faɗa yana kai masa duka ta ko'ina. Duk yadda Abdul ya kai ga ƙoƙarin kwacewa amma sam ya kasa saboda yadda Zaiyan ya yi masa matsar da duk ƙarfin da yake ji da shi ya kasa kwatar kansa a wajan shi. Da kyar ta miƙe tana yarfa hannu ta ɗingisa ta nufe su ganin yadda yake dukan Yayan nata, tana isa ta miƙa hannu za ta taɓa Zaiyan sai kuma ta fasa zuciyarta na ba ta umarnin ta bari ya masa dukan sakwara, ganin dai zai yi kisan kai ta miƙa hannu da kyar ta ce "Zain please ka rabu da shi Yaya ne fa." Ta faɗa tana kama damtsen hannunsa. Cak ya tsaya da dukan nasa zuwa lokacin Abdul ya yi laga-laga sai fitar numfashi yake a wahalce, amma duk da hakan bakinsa bai mutu ba sai cewa yake "Wallahi Baby in ba ki bani takardun da na buƙata a wajan ki ba sai na kashe ki."

Ba ta kula shi ba ta lallaɓa Zaiyan ya matsa daga gefen shi, goge hawaye ta yi zuciyarta na mata zafi wai yau ita ce Abdul ke furta mata kalmar zai kashe ta, durƙusawa ta yi a gaban shi ganin ya yi ƙasa ya zauna ba shiri. Kamo hannunsa ta yi Zaiyan da ke bayan ta ya buge hannun yana turo baki ya soma jan ta, turjewa ta yi ta sa masa kuka tana girgiza kai, hura hanci ya yi sai kuma ya sake ta shi ma ya rushe da kuka ya zauna a gefenta yana kallon Abdul kamar yadda itama take kallon sa. Hannun Abdul ta riƙe cikin raunanniyar murya baki na rawa ta ce "Ya.. Yaya don Allah ka yafe min in lefi na maka wanda har ka tsaneni haka, ban san akan wasu takardu kake magana ba ni babu komai a wajena. Ko a mafarki aka ce min irin wannan ranar za ta riskeni zan ƙaryata, sai ga shi wai yau Yaya ni kake duka kamar ka kama mai lefi why Yaya? Ashe ba za ka riƙeni amana ba kamar yadda Mom ta bar ma? Anya kana cikin haiyacinka kuwa Yaya?" Ta ƙarashe maganar tana ci gaba da kuka..
Chapter 77 · 0% Book details