← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 120

Sashe 18

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi Nadumbuza ya yi ya tashi ya ɗauko wannan ruwan ɓaki a cikin ƙwarya ya miƙa wa Alhaji ya ce "Alhaji burinka ya kusa cika ga wannan ka shanye shi tas, sannan ka ƙoƙarta ka ƙarasa ɗayan aikin kafin nan da wani lokaci. Shi kuma wannan za mu yi aiki a kansa yau ɗin nan, amma kafin a kai ga haka sai an yi masa tatar jini an ba wa Uwa Dudu ta sha kafin ta biya mana buƙata."

Da sauri Alhaji ya am shi wannan ɓakin ruwan ya shanye tas burinsa bai wuce ya ga an gama komai ba, Nadumbuza ya buɗe wata ƙwarya ya zaro wuƙa mai mugun kaifi ya nufi Zaiyan da ke kwance kamar gawa, saita maƙoshinsa ya yi zai yanka sai ya fasa ya sa aka kunce masa ɗaurin. Kan tsintsiyar hannunsa ya dan yanka sai ya ɗauko wani abu mai tsini ya soka a cikin yankan ya shige cikin hannun Zaiyan har sai da ya hudo ta baya sannan ya cire yana dariya, ƙwarya ya sa ya tari jinin da yake zubowa yana lashe baki tare da yin wasu irin yare yana ɗaga hannu yana shafa wa a jikin Zaiyan. Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci ƙwarya ta cika taf da jini amma jinin bai daina zuba ba, sai da ya sa harshe ya suɗe inda duk jinin ya zuba sannan ya koma gefen ƙwaryayyakin dake jere a wajan ya buɗe ɗaya daga ciki ya ɗauko wani magani, buɗewa ya yi ya zuba a ƙofar yankan da ya yi masa nan-da-nan jinin ya tsaya cak kamar ƙafewar ruwan sama . Jinin ya ɗauke ya dinga zagaye tsakiyar ɗakin yana surutai, bayan ya gama suka shiga wani ɗaki da ke cikin ɗakin. Ɗaki ne mai girma sosai yana da duhu sosai ko tafin hannunka ba ka gani, amma suna zuwa tsakiyar ɗakin wani irin ƙara ya dinga kai-kawo cikin kunnuwansu sai ga haske ya baiyana suka yi saurin zube wa a gaban Uwa Dudu suna faɗin "Uwa Dudu mai share mana kuka ke ce gatanmu ga sadaukarwar an kawo miki." Nadumbuza da Alhaji suka faɗa a tare.

Cikin wata iriyar murya aka soma magana.

"Tabbas yau kun faranta min , kuma kun cika masu biyayya a gare ni dan haka zan yi muku duk abin da kuke so, sai dai ku sani wannan mahaukacin da kuka ɗauko yana ɗauke da wani haɗari wanda ni kaina na kasa ganowa, tun da suka tunkaro gidan nan sandar girman Sarautar gidan nan ta girgiza abin da ba ta taɓa yin haka ba. Hakan yasa na gane cewa lalle fa jinin wannan bil'adaman shi ne jinin da zai ƙara min ƙarfi fiye da tunani, dan haka dole ne duk sati ake kawo min jininsa ina sha." Aka yi shuru sai ga wata halitta mai kama da Mage ta iso ta amshe ƙwaryar jinin ta ɓace, hakan yasa Nadumbuza ya ce "Mai girma Uwa Dudu yanzu to me ya kamata ayi akan wannan yaro?"

"Ni zan yi wannan aikin kawai ku tafi, kai ma Nadumbuza na ba ka izini ka je ka ga gida." Ana gama faÉ—in haka hasken É—akin ya É—auke É—if, hakan yasa suka yi saurin fita...

Alhaji ya É—auko kuÉ—i É—auri biyar na rafa ya aje wa Nadumbuza tare da yi masa kirari sannan suka fita shi da yaransa, shi ma Nadumbuza kalaman tsafi ya yi ta yi ya É—auke Zaiyan ya sa shi cikin É—aya É—akin sannan ya fita. Wani rami mai matakala Nadumbuza ya bi daga bayan dakunan ya shige ciki..

BAYAN KWANA

Abir na dawowa daga makaranta ta shirya ta matsa wa Abdul sai sun tafi Unguwar *Deboli*, bai musa mata ba suka tafi su uku har da Iman..

Suna fita sai ga Uncle Aruf ya karyo kwana layin, ganin motar Abdul sai ya dinga danna musu oda da ƙarfi yana bin su. Abdul ya ankare da motar da take bin su ya dakata, Uncle Aruf ya fito cikin gayun shi ya ce "Hello my Brother and Baby."

Cuno baki Abir ta yi tana jin haushin zuwa Uncle Aruf ganin zai tsayar musu da tafiya, ita kuma gabaɗaya hankalinta ya kasa kwanciya so take ta je ta ɗauko Zaiyan daga wannan ƙazamin wajan, ga kewar shi da ta addabe ta har gizo yake mata in ta zauna.

Murmushi Abdul ya yi ganin yadda ta yi kicin-kicin da fuska ya ce "Baby ki yi haƙuri Uncle ya zo yau ba za mu samu damar zuwa ba mu koma."

Nan-da-nan idanunta suka cicciko da hawaye ta kifa kanta a cinya ta soma rero kuka, shi kuwa Uncle Aruf ganin Abdul ya soma yin baya-baya da motar sai ya koma tashi suka dunguma cikin gidan.

Tana fitowa ta dinga kuka ta shige ciki suka mara mata baya. Da Sallama suka shigo inda suka samu Grandma da Mommy da kuma Laraba na mammatsa wa Grandma ƙafa tana zuba mata surutu....

"Good Afternoon Grandma, i miss you so much." Uncle Aruf ya faÉ—a yana wani É—age wa Grandma gira.

Ai kuwa kamar jira take ta amshe ƙafarta daga hannun Laraba tare da ƙanƙance idanu ta ce.....

_🤓an taɓo mana Grandma ɗin mu🤭_

_*Daku har kullum Maman Nusaiba ce*_
[6/20, 7:40 PM] Ummu Amjad: My Addatyna: _*~A HAKA NAKE SON SHI~*_

*Arewabooks.com: Saratalkasum1897*

+966577675904

Shafi na (11)

Ƙanƙance idanu ta yi cike da Jin haushin turancin da ya mata ta ce "Kai Arufullahi ka fita idona na rufe kafin na ci kan ubanka mai furfura." Ta faɗa tana hura hanci. Dariya Uncle Aruf ya yi ya tako ya iso gaban ta yana murmushi ya ce "Grandma ke ko irin ɗan missing ɗina ba ki yi ba? Da kika ganni maimakon ki tashi ki tarboni kina min oyoyo sai kuma ki ce haka, yanzu dai ya kike?" Ya faɗa yana kallon Laraba da ta ƙura masa idanu ta saki baki, ita tun da take ba ta taɓa jin wanda turancin shi ya shiga ranta ba irin Uncle Aruf ga ya ɗau wanka irin na gogaggun 'yan boko sai zuba ƙamshi yake, gyaɗa kai ta yi jin kamar an dafa ƙafadarta ta juyo dan ta ga waye haka, ganin shi ta yi yana mata murmushi ya ce "Hello beautiful how are you?"

Ai kuwa Laraba ta washe baki cikin jin daɗin ɗan gayu kamar Uncle Aruf ya kula ta , duk da ba ta iya turanci ba amma ta ji daɗi kuma ta san ba zai ce mata ƙazama ƴar ƙauye ba kamar yadda Abdul ke faɗa mata kullum. Baki ta riƙe tana ƴar dariya ta ce "Alkur'anin Allah i love you ɗan gayu, amma dai kai bature ne ko?"

Dariya ce ta so subcewa Abir jin bin da Laraba ta faɗa dan ta san dai Laraba ba turanci ta iya ba, amma ta fuskanci tana mugun son koyon turanci. Abdul ya ja tsaki ya dubi Uncle Aruf ya ce "Uncle wannan fa mai aikin Mommy ce har kake wani sakar mata fuska, sannan ba wani sanin turanci ta yi ba I love you ma da ta ce ma ba ta san mai kalmar take nufi ba." Ya faɗa yana hararar Laraba da ta yi lakwas, nan-da-nan nan hawaye ya cika kwarmin idanuwanta ta sa hannu ta goge, a ranta tana aiyanawa dole ma ta koyo turanci ko dan Abdul da yake mata cin zarafi yana kiranta da daƙikiya ƙazama, so take wata rana ta nuna masa ita ba daƙikiya ba ce kamar yadda yake kiran ta da kalmar. Sosai zuciyarta ke mata zafi da ƙuna ta ɗago ta dubi Uncle Aruf da bai ce komai ba sai kallon ta yake ta sa gefen hijabi ta goge hawayen da suka silalo kan kuncinta ta ce "Ni dama ban ce na iya Ingihi ba , dan ban yi makarantar boko ba sai Islamiya ita ma ta shekara ɗaya ce na yi, amma ai nasan kai ɗan gayu ne kuma ba za ka kira ni da daƙikiya ƙazama ba kamar hi?." Ta ƙarashe maganar tana zuba wa Uncle Aruf ido.. Ji ya yi ta ba shi tausayi ya ɗuka kusa da ita ýa ce "Beautiful ki rabu wannan shashashan yaron kin ji, karki sake kuka dan ya ce miki daƙikiya ke mai hankali ce kin fi ƙarfin daƙikiya." Gyaɗa masa kai kawai ta yi sannan ta tashi ta nufi hanyar da za ta sada ta da ɗakin kwananta...

Sai da ya ga ta ɓace wa ganinsa sannan ya sauke ajiyar zuciya ya dubi Grandma da ta harɗe hannayenta a ƙirji tana girgirza ƙafa, dawo da kallon shi ya yi a kan Abir ya ga ta yi fuska tausayi ya ce "Baby What happened?"

Girgiza masa kai ta yi ba ta ce komai ba dan ita gabaɗaya hankalinta yana can tunanin Zaiyan da son ta gan shi ya yi ta mata surutun nan nashi mai sanya ta nishaɗi, ajiyar zuciya ta sauke ta ƙara kawar da kanta dan kar ma ya kuma mata wata tambayar..

Mommy ta nisa ta ce "Aruf shi ne zuwa ba ko sanarwa? Sannan da ka iso ko ka zo gidan nan sai yau ka shirya ka zo mana?"

Gyara zama ya yi ya ce "Am so sorry Mom, Wallahi kin san bana son Khairat ta san na dawo shi yasa na yi zuwan bazata." Murmushi Mommy ta yi ta ce "To barka da zuwa ya mutanen can?"

"Suna nan lafiya sun ma ce a gaishe da ku, Grandma na miki odar goro daga can."

Jinjina kai kawai Grandma ke yi ta kuma ƙi ɗauke hannayenta daga bisa ƙirji, sai da ta shirya dan kanta ta sauke ta dubi Mommy ta ce "Sa'ade Wallahi suma Tallahi sai na ci mutimcin Abdullahi a gidan nan, akan me zai takurawa yarinyar mutane da ya zo ya ganta sai ya yi ta faɗa mata magana mai zafi? To ni ba ƴar banza ba ce da zan bari ana cin zarafin ɗan'adam ina zaune ina kallo ba zan iya tashi na maka dukan mutuwa a palon nan. Kai wa ya taɓa yi ma gorin ba ka da aure? Dan ka yi wani ɗan iskan bokon ka shi ne har kake wani gadara kai mai ilimi ne? To ka fita idanuna na rufe kafin na zazzabga maka mari irin wanda na taɓa yi wa ubanka Kabiru."
Chapter 18 · 0% Book details