← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 120

Sashe 50

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cewar Doctor Hashim yana goge hawayen tausayin Zaiyan, shi kuwa Suhal tun da ya zo yake kallon Zaiyan ya rafka tagumi, ɗagowar da Zaiyan zai yi ya ga Suhal ya kafe shi da kallo, ai kuwa ya miƙe ya isa gaban shi ya tsaya. Kallon shi shi ma yake yana ɗan waro idanu kamar wanda ya ga wani abu a jikinshi, ganin yana kallon ƙafarsa shi ma sai ya kalli ta Suhal ya ga babu takalmi ya sunkuya ya fidda nashi takalmin ya miƙa masa yana yin fuskar tausayi ya ce "Ashe kaima abokina Babanka ba ya tsoron Allah shi ya sa yaƙi saya ma takalmi, to in dan wannan ne da kake ta kallo ga shi nan na ba ka kyautar shi har abada." Ya faɗa yana daura masa takalmin a cinyarsa.. Ɗaukan takalmin Suhal ya yi bai ce komai ba ya sake ɗagowa ya kalli kayan jikinsa, nan ma Zaiyan ya daure fuska kamar wanda zai dake shi ya ce "Dalla can meye kake kalle min abuna?" Sake kallon kanshi ya yi ya kuma kallon Suhal sai ya ga yana zubar da hawaye, sai ya saki fuska ya kama rigarshi ya cire yana fadin "Ka ga indai dan wannan kayan ne kake yiwa kuka ga shi nan na ba ka su kyauta, bari na ba ka har wandon ma dan na ga a gidanku babu masu tsoron Allah bare su ji tausayin ka tun da Mamanka ta mutu su saya maka kaya da takalmi." Yana maganar yana cire wandon ya haɗa da t-shirt ya rage sai shi sai single da wandon ciki iya gwiwa ya tsugunna ya aje masa a kusa da ƙafuwansa ya ci gaba da magana.

"Yanzu da ban ba ka nawa ba sai dai ka yi ta kuka dan ba ka da uwa? To yi shuru duk zan raba kayana na ba ka rabi sai kake sawa, amma fa karka bai wa Babanka tun da shi ba ya tsoron Allah irin na Babana da ya sace min Anty ya gudu." Tsit suka yi suna kallon shi su Abir masu ruwan ido a kusa tuni ta jima da yin sharkaf da hawaye, ganin kirar jikin Zaiyan ta ji ƙirjin ta ya buga ta runtse idanu tana sauke numfashi, ita in ba jikin Yayanta ba ba ta taɓa ganin jikin namiji haka ba.. Abdul ya girgiza kai ya ce "Zaiyan ɗauki kayanka ka sa ba ka ga shi ma yana da nashi ba?"

Hannu ya kai zai ɗauki kayan sai kuma ya yi saurin ɗauke hannun yana zare ido ya ce "Ka ga abokina ka yi haƙuri Wallahi ni ba bawaro ba ne aron kayan zan yi, amma tun da ba ka ba ni ba ga shi nan na aje ma kayan ka." kasa magana Suhal ya yi idanuwansa sun yi jajur hawayen ma sun kasa zubowa, wani irin zafi yake ji a zuciyarsa da zarar ya kalli halin da Zaiyan yake ciki. Abdul ya kuma cewa "Ka ɗauka ba sata ba ce ka yi."

Kallon Suhal ya yi ya ce "Shin za ka ara min kayan naka? Wai ka ji Baba ya ce na ɗauka ni kuma na san in na ɗauka ba ka ban ba ai sata ce na yi ko?" Murmushi Suhal ya yi hawaye suka zubo masa ya ɗauki kayan ya miƙa masa ya ce "Ai kai abokina ne tun da Babanka ya ce ka ɗauka ga shi na ba ka kyauta."

Dariya ya yi ya ƙi amsar kayan ya dawo wajan Abdul ya kai hannu ya taɓa gemunsa, waro idanu ya yi ya kuma taɓa gemun ya ce "Baba kaima irin na abokina gareka?"

GyaÉ—a masa kai Abdul ya yi yana murmushi ya ce "Je ka amso kayan ka sa."

Rausayar da kai ya yi ya ce "To amma dai Baba ka ji tsoron Allah ka daina sace mutane."

To kawai Abdul ya ce zai daina sannan ya isa ya amso kayan nashi ya mayar ya dawo kusan ƙafar Abir ya zauna, murmushi ta yi ta yi wa Suhal nuni da ya zo ya soma aikinsa ya taso ya iso, hannun Zaiyan ya kama cikin lallami ya ce " Abokina ka tsaya na duba ka in kana so mu tafi London ɗin." Da har ya kwace hannunsa yana kumbura baki jin abin da ya faɗa sai ya yi dariya ya miƙa masa hannun..

Gwaji ya dinga masa Doctor Hashim shi ma ya iso yana taya shi, ya auna jininsa ya ga ya yi ƙasa soaai, sai da suka gama sannan Suhal ya ce "Gaskiya jinin jikinsa ya yi ƙasa, in da hali za a iya sa masa leda biyu ta jini dan yana buƙatar shi yau ɗin nan."

Doctor Hashim ya ce "To ai kuwa bari na hanzarta na faÉ—a wa nurses É—in mu akwai jini irin nasa leda É—aya, in ya so sai a samo É—ayar ko zuwa an jima ne."

Mamaki ne ya rufe Abdul har ya kasa ɓoyewa ya riƙe baki ya ce. "Hashim ba ka ce min idan mutum ba shi da jini yana jin zafi a jikinsa ba, idan zai fita daga haiyacinsa har sai an sa masa jinin zai dawo daidai?".

.

"Kwarai kuwa haka ne Abdul, ni kaina na yi mamakin ganin ba shi da jini isasshe amma bai nuna alamun da za a gane hakan ba, alama É—aya kawai na gani ita ce ya yi fari sosai ya koÉ—e fiye da baya, amma bayan haka ban ga komai ba abin nan ya ba ni al'ajabi fa."

Duk shuru suka yi Abir ma shuru ta yi tana danganta hakan da wannan Aljanar da take bibiyar su, ko dai ita ce take zuƙe wa Zaiyan jini? Dam! Zuciyarta ta buga ta sauke numfashi ba ta ce komai illa kallon Zaiyan da take yana ta yi wa Suhal maganar tafiyar su zuwa London shi kuma ya ce masa za su je sai an jima..

Hashim ya kira ya tambayi nurse É—aya daga cikin su ina jinin yake, ta faÉ—a masa ai yanzu suka saka wa wata mata, dafe kai ya yi ya aje wayar yana kallon su ya ce "Wai babu jinin yanzu mu tafi da shi Asibiti mu ga ko za a samu na sayarwa a wajan wani abokin aiki na, mu a Asibitin mu wahalar samu yake."

Suhal ya yi murmushi ya ce "Kar ku wani damu zan ba shi nawa ko leda uku kuke so ku ɗiba a jikina, jininsa irin nawa ne mai wuyar samu in kwanan mutum ya zo ƙarshe kafin a samu mai irin jininsa asa masa sai ka ga ya mutu." Wani sanyi Abir ta ji ya ratsa ta, ita kuwa da me za ta sakawa Suhal da wannan karamci da yanuna mata akan amanarta? Lumshe idanu ta yi tana yi wa Suhal addu'a..

Abdul da Suhal da Doctor Hashim ne suka tafi Asibitin ita kuma Abir Abdul ya sa aka mayar da ita gida ba dan ta so ba..

BAYAN SATI BIYU.

Yau su Alhaji Mustapha suka shirya tsaf suka nufi gidan Boka na kan Dutse. Jirgi ya É—auke su daga Yola zuwa Legos, daga nan suka kutsa cikin dajin oready dama tuni sun sa wani yaron su dake Legos ya tanadar musu mota suka shiga suka tafi..

Sai da suka wuni liƙis suka tafi gaf da faɗuwar rana suka iso gindin dutsen, haka suka dinga hawa suna bin wata matakala da ke jikin dutsen har suka hau can sama tsololokuwa. Wata hanya suka gani wajan kamar ɗaki wanda aka yi shi da dutse, kamar yadda Zee ta musu bayani Alhaji Mustapha ya ce "Boka dan gidan Iyami jikan Jahun, waye ya ce da kai ba kai ɗan butar uwa?"

Wata irin girgiza dutsen ya ɗauka suka maƙale juna cike da tsoro, Alhaji Mustapha ne ma wanda ya dan fi su dakewa ya tsaya ƙam yana muzurai, wani gajeran mutum ne ya fito baƙi wuluk da manyan idanu jajaye. Sanye yake da ganye a ƙugunsa ya masa kamar baza, wuyansa wasu layu ne kala-kala haka ma damtsensa kambu ne mai haɗe da laya har zuwa tsintsiyar hannunsa, hannunsa riƙe da wani gashi fari kamar na tinkiya. Hannu ya daga sama ya kwarara ihu ya yi wa kansa kirari sannan ya nuna musu inda ya fito ya ce "Kun zo inda za a share muku kukan ku iyalan sheɗan, ku shiga muje ciki."

Da É—ari-É—ari suka shiga sai ga su a wani babban É—aki wanda aka masa ado da fatocin namukan dadi kala-kala, samar wasu kawuna ne a jere sun kai goma kamar na mutune..

Jiki na rawa suka zauna Jarmai zai yi bayanin abin da ya kawo su Boka ya daka musu tsawa ya ce....

_*Taku har kullum Maman Nusaiba*_
[6/20, 7:53 PM] Ummu Amjad: ~A HAKA NAKE SON SHI~

+966577675904.

Shafi na (25)

Boka ya daka musu tsawa ya ce "Ba a yi mana bayani in ba mu muka ba da dama ba, duk an faɗa mana abin da yake tafe da ku iyayen sheɗan, kuma buƙatarku za ta biya matuƙar kuka yi abin da na sa ku."

Jiki na rawa Alhaji Mustapha ya ƙara duƙar da kanshi ƙasa kamar zai yi wa Boka sujjada ya ce " Ai duk dokokin da ka shinfiɗa mana za mu bi boka matuƙar buƙatar mu za ta biya, kai ko mutum kake so mu kawo maka da rai za mu nemo a kawo ma ko nawa kake so za mu iya, mu dai kawai burin mu ayi mana aiki yadda ya kamata."

Zaro jajayan idanunsa Boka ya yi ya tashi tsaye yana zagaye su yana wasu irin yarika, sai da ya gama zagaye su son ransa sannan ya dawo ya zauna yana kallon su, hannu ya saka a cikin wata buta da ke gefen shi ya fito da wasu layu guda biyu ya aje a gaban su ya ce "Kun ga wannan layun? "

A tare suka gyaɗa masa kai sun amsawa da "E Boka mun gani." Dariya ya yi ya ɗauke layar ya jimƙe su a hannu yana ta surkunlan shi, bayan ya gama ya sake aje musu wannan karon kuma layar sai ta zama uku ya soma magana yana muzurai.

"Me kuke so ayi musu su duka."
Chapter 50 · 0% Book details