Sashe 93
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zaro idanu ya yi ya ce "Kamar yaya kenan?"
"Dad an kama wasu kaya da aka dauko su daga Legos zuwa nan Yola, kuma nasan kayanka ne haka suma direbobin suka ce kayan ka ne amma abinci ne da za ka rabawa talakawa, bana so Ogan mu ya samu labarin an kama kayan saboda ya soma zargin wani abu a game da kai. Yanzu duk inda kake ka zo a samu ka amshi kayan nan kafin ya ji labari. "
Zufa ce ta shiga karyo masa ta ko'ina ya sa gefen malum-malum ya sharce kamar mayen da ya ci ɗa a kasuwa ya juya ya ga kowa hulɗar gaban shi yake, marar gaskiya ko ruwa sai ya yi zuba! Ya sake matsawa ya ma rasa me zai ce saboda kaso biyu bisa uku na dukiyarsa ya zuba ya yo safarar wannan kayan tun daga ƙasar Japan, ja baya ya yi ya nisa sannan ya ce "Ga..Gani nan zuwa."
Yana sauke wayar ya ji ƙaran shigowa text message bai duba ba ya mayar da wayar a aljihu ya juyo zai tafi suka yi kiciɓus da Jarmai, kallon shi ya yi ganin shi ma a ruɗen yake ya ce "Jarmai ya dai?"
Nuna masa text ɗin da aka yo masa ya yi yana huci, kafin Alhaji Mustapha ya karanta kira ya shigo wayar, ganin sabuwar number ce sai yaƙi dauka yana kallon Alhaji Mustapha.
Sake kira aka yi hakan ya sa a fusace Jarmai ya É—aga kiran ya buÉ—e sauti dan Alhaji Mustapha ya ji, a kufule Jarmai ya ce "Wai uban waye kai?"
Dariya ya yi wadda ta sa su zabura suna kallo juna, sai ya yi gyaran murya ya ce "Ku har kun isa ku ci banza? To wasan ya kusa zuwa karshe wannan karon sai kun bambance tsakanin aya da tsakuwa."
Ƙara fusata Alhaji Mustapha ya yi, gabaɗaya ya rasa abin da yake masa daɗi ya ce "To kai waye?"
Sake yin wata dariyar ya yi sannan ya ce "Damisa bisa kanku..."
_Maman Nusaiba ce_
[11/30, 1:59 Safiya] Anty Sarat (Mom Nusy 🌹): *A HAKA NAKE SON SHI*
Shafi na (46)
A mugun firgice suka kalli juna suna zare na mujiya, jikin Jarmai ne ya ɗauki rawa ya saki baki ya bi wayar da kallo kamar ya ga wata sabuwar halitta, Alhaji Mustapha ya ja numfashi gabaɗaya ya gama jiƙewa da zuba sai zaro idanu yake, Jarmai ya mayar da wayar aljihunsa tare yin ƙasa da kai kamar bafade a gaban sarki, ya ce "Damisa nan yana shigar mana hanci da ƙudundune fa, shin ba Boka na kan dutse ya faɗa mana cewa ba zai sake waiwayar Nigeria ba? Ko kuwa dai akwai abin da muka yi ba daidai ba a cikin sharruɗan da Boka ya gindaya mana?" Ya faɗa yana ɗago da kai ya kalle shi cikin idanu.
Alhaji Mustapha bai ce komai ba, duk lissafinsa ya karkata ne kan kayansa da ke hannun 'yan sanda, ba ya so su buɗe su ga abin da yake cikin kayan duk da kuwa yasan abu ne mai wahala su iya buɗe kayan har su gani, amma hakan bai hana shi shiga ruɗu da tashin hankali ba dan duk wani ƙarfinsa ya ta'alƙa ne a kan kayan, dawowar Damisa ba ta girgiza shi ba kamar ta kayan dan haka ya harɗe hannaye a ƙirji tare ta kallon Jarmai.
Ganin ba zai tanka masa ba ya matsa ya juya zai tafi dan ransa ya sosu da hakan, kama hannunsa ya yi tare da cewa "Sorry Jarmai ina cikin yanayi ne, idan muka yi sake fa É—an zaki zai girma."
A fusace Jarmai ya juyo ya ce "Girma kuma na yaushe? Ai tuni É—an zaki ya gama girma har ma ya fito farauta." Ya faÉ—a yana hura hanci sama.
"OK yanzu ka je Office É—in su Abdul ayo belin kayan nan, ni kuma zan samu Alhaji mu tsara yadda Damisa zai faÉ—a tarkonmu, wannan karon na sha alwashi sai mun masa kisan gilla."
Bai ce komai ba ya wuce yana gyara zaman babbar rigarsa, shi ma tafiyar ya yi suka ƙarasa sallamar mutanen da suka zo sannan suka bar wajan..
Gana mostgo ɗinta ta cicciɓo tana nishi saboda kayan da ke ciki masu nauyi, palo ta iso ta aje tana haki ta kalli Grandma da su Abba duk sun hallara a palon har da Daddyn Aruf, da kallo duk suka bi ta ta yi kwafa a ɓoye tana sunkuyar da kai ta ce "Inna ni zan wuce ƙauyenmu sai kuma na ce Allah ya sada mu da alkhairi."
Kallon ta Grandma ta yi tana rike haɓa ta ce "Yau gani ga ja'irar yarinya, me ya yi zafi shi ba wuta ba? Ki mayar da kayan nan kin ji ƴar albarka."
Kukan karya ta sa tana durƙusawa a gaban ta ta ce "Babu abin da aka min Inna, kawai dai zan koma wajan mahaifiyata ne na ci gaba da kulawa da ita."
Su Abba suka yi ta fama ta haƙura ta ƙara ko da wata 6 ne in ya so sai ta tafi amma ta nuna musu ita fa ta gaji ta aikatau ɗin nan hutawa take son yi, babu yadda suka iya haka suka haƙura suka rabu da ita ta mike ta dauki kayan, har Abba ya ce ta tsaya a kai ta har garin nasu amma ta ce za ta biya gidan da kawarta take aiki direban gidan zai kai su, haka dai Abba ya dauki kuɗinta na wata biyar da ba a ba ta ba ya miƙa mata tare da cewa "To ga haƙƙinki ko."
Sunkuyar da kai ta yi ta ce "Ni ai tun kafin Abir ta yi aure ta biyani kuÉ—in shekara, dan haka ba sai kun ba ni kuÉ—i ba an biyani tun kafin ma na yi watannin."
Wani irin nauyi ne ya danne musu zuciya gabadayan su jin ta ambaci sunan Abir, har Abba zai yi magana amma ya kasa saboda bakinsa ya masa nauyi, yana so ya tambaye ta a ina Abir ɗin take amma nauyin da ya danne masa zuciya ya hana shi furta hakan, ita kuwa duk tana kallon fuskokinsu ganin yadda lokaci ɗaya suka canja ta jinjina kai ta musu Sallama ta wuce suka bi ta kallo ba wanda ya ce mata a sauka lafiya, itama ba ta damu da hakan ba dan tsare ta da tambaya da suka yi sun kusa ɓata mata lokaci. A harabar gidan ta ci karo da Adul ya fito daga cikin motarsa, da kallo ya bi ta cike da mamaki ganin ta dauko kaya ta nufi get, da hanzari ya kira sunanta ta waiwayo ya mata alama da ta zo, ba muso ta iso gaban shi tana sauke jakar ta rusuna tare da cewa "Yaya Abdul barka da rana, ya wajan Anty Hafsat?"
"Barka dai Laraba ina zuwa haka na ga kin kinkimo gana mostgo kamar Æ´ar yawon cirani?"
Kallon ba ka da aikin yi ta masa dan mugun haushinsa take ji in ta tuna irin dukan da ya yi wa Abir, ta wani sashen kuma ya ba ta tausayi ganin yadda ya fige ya rame duk ya yi baƙi ya zama kamar wani dolo, kamar waina a tanda sai juya shi ake son rai.
" Gida zan koma Yaya Abdul."
Da mamaki ya kuma kallon ta sai ya basar ya zaro kuɗi ya miƙa mata tare da cewa "Ga wannan duk da ban san ba a nawa Mom ta dauko ki duk wata."
Kallon hadarin kaji ta masa ta mike tsaye ta ɗaura gana mostgo ɗinta a ka ta kalli kuɗin, wani maƙoƙo ne ya tokare mata maƙoshi ta nisa ta ce "Ka aje kuɗinka an biya ni haƙƙina sai an jima."
Ba Ta ma tsaya ta ji mai ce mata ba ta wuce da sauri ganin time na tafiya ta buÉ—e get ta wuce abin ta mai gadi na mata Allah kiyaye tana amsawa da amin har ta bar gidan..
Tafiya take da sauri kamar za ta kifa, sai da ta isa bakin babban titi ta tari mota ta ce ya kai ta airport, nan ya sanar da ita dubu uku za ta ba shi tun da ita ɗaya ce ta ce ba matsala. Tun da suka kama hanya ta ciro iPhone ɗinta nan ta ga saƙon shi ya ce mata karfe 11 na rana zai sauka, agogon wayar ta duba ta ga 10:40am ta sauke ajiyar zuciya tana murmushi. Suna isa ta biya shi kuɗin sannan ta nufi filin jirgin ta samu waje ta zauna, tana nan zaune jirgin su ya sauka aka buɗe mutane suka dinga fitowa ɗaya bayan ɗaya, cikin shigar shi ta ƙananan kaya masu yi masa matuƙar kyau ta hango shi yana taka matakalar jirgin yana saukowa, sosai ya mata kyau ya sha baƙin glass sai wani shan ƙamshi yake cike da izza da nuna shi ɗin mai aji ne yake saukowa, yana fitowa ya zaro wayarsa a aljihu ya danna mata kira, tana murmushi idanuwanta a kan shi ta daga kiran.
"Hello Jk kin iso ne?"
Ɗagowar da zai yi suka haɗa idanu ta mike tsaye tana ƴar dariya, yadda Ogan nata yake ɗaukar wanka abin na ba ta citta, har ya iso ba ta sani ba sai da ya ɓala yatsunsa ta firgita tana sa ƴar ƙaramar dariya ta ce "Welcome to Nigeria again sir."
Murmushi ya yi mata tare da cewa "Thank you." Kayan nata ya amsa ya É—aura akan akwatinsa ya dube ta yana yin gaba ya ce "Jk duk meye a cikin jakar nan ta yi nauyi?"
Gefen shi ta dawo suka jera ta ce "Computer guda biyu ce a ciki sai tufafina wanda Abir ce ta ba ni su masu kyau."
Jinjina kai ya yi bai sake cewa komai ba ta ga sun nufi wata baka mota mai kyau, shiga suka yi direban ya ja suka wuce. Sai da suka bar Airport din direba ya ce "Welcome back Oga, Ni ai na dauka kai da Nigera da sunan aiki ka gama sai dai ka zo dan hutawa, ko da ma za ka zo É—in ba dai Yola ba sai dai ko Abuja ko Kano."