← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 120

Sashe 71

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zabura ta yi ta yi baya jikinta ya dauki rawa ta yi baya za ta buga kanta da jikin gado ya yi saurin taro ta, kuka ta sa tana faÉ—in "M....

Maman Nusaiba ce🤏🏻😎

[11/13, 11:34 Yamma] Anty Sarat (Mom Nusy 🌹): ~A HAKA NAKE SON SHI~

Shafi na (34)

"Me ya kawo ka ɗakina?" Ta faɗa tana runtse idanu da ƙarfi tare sake sakin kuka ta cigaba da cewa "Ni ka tafi ka ba ni guri ko kunya ba ka ji kake kalle min jiki." Nannauyar ajiyar ya sauke ganin ba rauni ko buga jikinta da wani wajan ta yi ba kawai dan ta gan shi take wannan ihun, zama ya yi a kan gado ya miƙa hannu ya ɗago ta tana zillewa tare da kai masa duka a duk inda hannunta ya kai, shi ko dariya yake mata ƙasa-ƙasa dan kar ta ji ya ƙara yin lefi, a nutse ya ɗago da fuskarta ya kai bakinsa ya sumbace ta a goshi ai kuwa ta kwalla ƙara tana fadin "Ni fa ba ƴar iska ba ce irin ka, Wallahi zan faɗawa Anty Baby kana nuna min iskanci." Ta faɗa tana turo baki. Hannu ya sa ya matse bakin nata ta shiga mutsu-mutsun kwacewa jin wani zafi ya kawo mata ziyara amma ta kasa saboda ta ko'ina ya riƙe ta gam, daina motsi ta yi ta bude idanuwanta a kan shi suka hada idanu, harara kawai take aika masa duk da ya matse mata baki amma ko ɗar ba ta ji ba idanuwanta cike suke da masifa har wani ja ya soma saboda faɗa na cin mata rai kuma babu bakin faɗa.

"In ki ka sake turo min wannan bakin naki kamar gidan tsutsa sai na cire shi, me ya sa ke kin cika neman rigima ne My Iman? Ko bakya so ki shiga aljanna?" Ya faɗa yana sakar mata bakin ganin hawaye sun cika mata idanu. Tana samu ya sakar mata bakin ai kuwa ta ɓarke da kuka har da ɗaura hannu a ka kamar wacce aka zane, girgiza kai ya yi ya tashi ya isa inda ta watsar kayan ta, a hankali ya tsuguna a gaban kayan ya kai hannu ya dauka tare daga su yana dubawa tare ta yin murmushin gefen baki ganin kayan sosai suka masa kyau, dan shi ya sayo su da hannunsa a Amerika da ya je wani taro wanda Abir ta zaɓa da kan ta tana zuzuta kyau kayan, lumshe idanu ya yi yana jin wani irin zafi marar iyaka a zuciyarsa sai ji ya yi an warce kayan. Da sauri ya ɗago suka hada idanu ta yi saurin kawar da kanta tana hura hanci, murmushi ya yi ya miƙe tsaye shi rashin kunyar da take masa birge shi yake a maimakon ya ji haushin ce mata ɗan iska da take. A hankali ya kai hannu ya riko nata hannun ai kuwa ta fasa ƙara ta tattaro dukkan ƙarfinta ta turo shi baya jikinta na rawa, da sauri ta gyara zaman towel ɗin da ta dauka ta ɗaura ta nufi gefen ɗaya tana kuka ai kuwa ta buga gwiwarta a jikin wani show glass da ke kusa da gadon ta fasa kuka tana yarfa hannu. Jin kukan nata ya bambanta da wanda take ya sa shi saurin ɗago da fararen idanuwansa da suka soma ja ya kalli inda take tsaye, waro idanu ya yi ganin jini na bin ƙafarta kamar kiftawa da bismillah sai ga shi a gaban ta a rikice yana tamabauar ta.

"Subhanallahi! Garin yaya kika ji wa kanki ciwo Iman?" Ya faÉ—a yana janye towel É—in zuwa kan gwiwarta inda ya ga rauni ta samu a gwiwa.

Kuka take tana yarfa hannu ya rasa yadda zai mata ga taƙi ya canja mata kaya sai harara take aiko masa tana kuka, ganin za ta ja masa lokaci ya dauke ta cak ya aje a gaban miro ya ɗauki mai da hanzari ya ɗago da ita ya zaunar akan cinyarsa yana jera mata sannu, ai kuwa ta kafe ta ce bai isa ya taɓa mata jiki ba ya ba ta kayan za ta saka ya yi banza da ita. Ganin za ta sa masa ciwon kai da ihun da take ya matse ta ya sanya mata kayan tana ce masa mugu ya ce ya ji ɗin, yana gama sa mata ya ɗago fuskarta da ta yi sharkaf da ruwan hawaye da majina ya sa hannu ya goge mata fuskar yana jin ba daɗi, numfashi ya fesar ya kura mata idanu yana kare mata kallo ta turo baki. Murmushi ya saka mata ya yi gyaran murya ya ce "Wai me ya sa kike jin tsoro na?"

Kara cuno baki ta yi tana dafe gwiwar da ta ji ciwo ba ta ce masa komai ba, shi ma bai wani damu ba ya sauke ta tare da cewa "Oya muje Momma na jiran mu za mu ci abinci." Ya faɗa yana kama hannunta suka nufi kofar fita daga dakin, sosai ta ji gwiwar na mata zugi dan haka ta dinga ɗigisawa tana yarfa hannu tare matse hawaye dan ta ƙagu su isa wajan Mamma..

Jakadiya ta fara ganin su ta dafe ƙirji tana bin Iman da kallo ganin jini ya biyo jikinta, kallon ta Ikilima ta yi ganin yadda ta rikice ta ce "Ya dai Jakadiya?"

Saurin yin ƙasa da kai ta yi tana kallon Mamma cikin yin ƙasa da murya ta ce "Ranki ya daɗe da alama fa Gimbiya babu lafiya a tattare da ita." Ta faɗa tana zare idanu kamar maye ya ci ɗa a kasuwa.

Kallon hanyar ɗakin Suhal Mamma ta yi ai kuwa ta yi arba da su Iman sai yarfa hannu take tana kwaɓe fuska shi kuma yana lallaɓa ta suna ci gaba da tafiya, gaban Mamma ne ya faɗi amma ta dake tana jiran su iso dan ta tabbatar da abin da idanuwanta suka gane mata.. Suna gaf da isowa ta sa kuka tana kwace jikinta daga rukon da ya mata ta nufo kan Mamma ta faɗa jikinta ta ƙara wa kukan ta volume, da sauri Mamma ta rungume ta tana bubbuga bayan ta alamar rarrashi, Jakadiya da ta kasa hakuri ta ɗan matso ta ce "Gimbiya wai me yake faruwa kike kuka?"

ÆŠagowa ta yi daga jikin Mamma ta kalli sashen da yake suka hada idanu ya yi wani kicin-kicin da fuska sai ta kuma sakin wani kukan har da shashsheka, ita dai Mamma shafa bayanta take ita ba bakin magana gareta ba ballantana ta rarrashe ta da kalamai masu daÉ—i. Sai da ta yi me isar ta sannan ta kalli Jakadiya tana goge hawaye ta ce "Ba shi ba ne ya ...

Kasa ƙarasawa ta yi saboda kukan da take ya hana ta yin maganar, Jakadiya da son gulma ta kama hannunta ta ce "Haba Iman to meye na kuka kuma? Ai kowa haka yake fara rayuwar aure ki yi haƙuri." Ta faɗa tana gyaɗa kai.

"To amma Jakadiya ai sh..

"Jakadiya tashi ki b mu waje za mu ci abinci." Suhal ya faÉ—a fuska ba annori, nan da nan ya dawo mata Yarima Suhal É—in da ta sani ta yi saurin tashi jikinta na rawa ta fita..

Kallon shi Mamma ke yi ta tambaye shi da maganar kurame me ya yi wa Iman É—in haka?

Nisawa ya yi ya ce "Ni fa babu abin da na mata buge gwiwa ne ta yi a ɗaki, shi ne taƙi na gani sai rigima take yi wa mutane." Ya faɗa yana rausayar da kai ganin Mamma ta tsare shi da kallo..

Ikilima ta dannawa likitan su kira ta ce ya zo ya duba Matar Yarima ta samu rauni, to ya ce mata ga shi nan zuwa sannan ta kashe. Shi dai kallon su yake ganin yadda suka mayar da shi gefe sai rarrashin Iman suke ta lafe a jikin Mamma tana hararar shi da zarar sun haÉ—a idanu, kwafa ya yi yana kaÉ—a kai sai ga doctor mace an yi mata iso ta shigo. Rauni ta wanke mata aka sa mata magani a wajan, ko abinci ba ta ci ba bacci ya yi gaba da ita. Sai da Mamma za ta tafi wajan Maimartaba ya amshe ta suka nufi É—akin su, itama Ikilima ta wuce nata É—akin tana yi wa Suhal dariya jin ya ce wai Iman ta yi nauyi sosai..

Kwantar da ita ya yi ya lallaɓa shi ma ya kwanta tare da dauko ta ya mata masauki a jikinsa ta ci gaba da bacci, shi kuwa kasa bacci ya yi yana ta saƙa da warwara da kyar bacci ya yi gaba da shi..

Jakadiya na fita part ɗin Kilishi ta nufa inda Hadiman part ɗin ke gaishe da ita, cikin gadara take amsawa kamar ita ce matar sarkin har ta iso babban palon Kilishi wanda yake shuru ba kowa a palon sai ƙaran AC da ke tashi, mamaki ne ya kama ta ganin rigar Kilishi a palon haka dai ta danne ta nufi ɗakin. Kwalalo idanu ta yi lokacin da ta shiga ɗakin ganin mutum a kwance a gadon Kilishi ita kuma ba ta ma ɗakin, jiki na rawa ta yo baya sai ta ji ƙaran bude kofar bandaki sai ta yi gyaran murya tare da cewa "Ranki ya daɗe Jakadiya ce ina son yin magana da ke mai muhimmanci."
Chapter 71 · 0% Book details