← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 120

Sashe 87

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_" Kut! Kin yi me kika ce? To ba aure ba ko ke ce limamin da yake ɗaura aure sai kin kashe wannan auren kin aureni, ban taɓa cewa ina son abu ba kuma na rasa dole kema ki rabu da wanda kika aura ki zo gareni, idan har ba haka ba zan sa a nemo min inda kike a duk faɗin jahar Yola Wallahi. "_

Tsaki ta yi ta tura masa nata saƙon.

_"Kuma ai sai ka yi, kai É—in banza ka isa ka sa na kashe aurena na aure ka ban san kai ko a wacce duniya kake ba, to Wallahi ka yi kaÉ—an kuma ka jima ba ka binciko inda nake ba a Yola, aikin banza kawai."_

Emoji É—in love ya turo mata ta yi saurin fita ta sauka a online É—in ta kashe computer tana me da na sanin buÉ—e ta, tashi ta yi ta janyo pilow ta É—aga kan Zaiyan ta É—aura sannan ta fita É—an yi musu girki...

Tana fitowa ta ji ana ta zage-zage a wajan su Maman Samira, suna ganin ta Maman Amal ta ce "Yawwa zo ba mu kuÉ—in da kika satar wa Maman Samira."

Sororo ta yi tana kallon ikon Allah, kuɗi kuma? To waye ya ce musu ita ta saci kuɗin? Abin da tafi tsana a duniya sata, dan haka ta ji ranta ya yi mugun ɓaci ta kalli Maman Amal ta ce "Ban gane me kike nufi ba? Wai ni kike zargin na satar miki kuɗi?"

"Chass kuwa, billahillazi sai kin fito mana da kuÉ—in nan ko mu nakaÉ—a miki É—an banzan duka a gidan nan, ai me É—aure miki gindin ba ta nan bare ta shigar miki, mu za a nuna wa bariki da iya shege." Cewar friend É—in Ladidi mai suna Gamboliya...

Kasa ce musu komai ta yi jikinta sai rawa yake ganin yadda suka kewaye ta, ba ta ankara ba ta ji saukar mari tas! A zabure ta É—ago ta ga Maman Amal tsaye gaban ta tana huci, hannu ta É—aga za ta sake kai mata mari ta ji an daka mata wata gigitacciyar tsawa.

"Idan har kika sake É—aura hannunki akan fuskarta za ki ga abin da zai biyo baya!............"

_Maman Nusaiba ce_
[6/20, 8:43 PM] Ummu Amjad: *A HAKA NAKE SON SHI*

Shafi na (43)

Saurin waigowa Maman Amal ta yi idanunwanta suka sauka akan mai gidan da suke haya, a wuƙance ta sake kallon shi ta matsa daga kusa da Abir tana nuna ta da yatsa ta ce. "Ki fito min da kuɗina ko kuma na kai ƙaran ki wajan 'yan sanda."

Ƙarasowa ya yi yana baza babbar rigarsa tare da gyara zaman hula ya turo ta gaban goshi irin ba mutumcin nan. Kallon Abir ya yi da idanuwanta suka ƙafe saboda da tashin hankali, cike da tausayawa ya tsaya a gaban ta ya yi gyaran murya ta ɗan kalle shi, waro idanu waje ta yi baki na rawa ta ce. "Bawan Allah kamar na taɓa ganin ka."

Shi ma kallon sani yake mata can ya gyaɗa kai yana murmushi ya ce "Tabbas mun taɓa haɗuwa motata mai ya ƙare min a hanya kika ba ni galam a cike tab, ashe ma a nan garin kike kuma a gidana ki na haya, amma dai duk da haka ba ki jima da zuwa nan gidan ba ko?"

ÆŠan murmushi ta yi ta kai hannu ta shafa kuncinta da yake mata raÉ—aÉ—in zafin marin da aka mata, sunkuyar da kai ta yi ta ce "E ban jima da zuwa ba gaskiya."

Kallon Maman Amal ya yi yana haÉ—e rai ya ce. "Ke kuma baiwar Allah me ya haÉ—aki da ita kika daga hannu ki ka kifa mata mari kamar Allah ta aiko ki? Haka ake rayuwa? Bai kamata kuke faÉ—a ba kuna gida É—aya."

Haushi ne ya rufe Maman Samira ta matso tana hura hanci ta ce. "Alhaji wannan da kake gani ɓarauniya ce, kuɗi ta sace min har dubu ashirin da biyar." Ta faɗa kamar za ta kai mata duka. Girgiza kai Alhaji ya yi ya ce "Gaskiya ban yarda wannan nutsatsiyar yarinyar za ta ɗaukan miki kuɗi ba da sunan sata, ke da gani ma ai kin san tafi ƙarfin wata dubu ashirin da biyar, kin ga ta miki kala da mabuƙata?" Ya faɗa a fusace yana nuna mata Abir.. Kafin Maman Samira ta yi magana sai ga Ta Sakkwato ta shigo gidan ita da Ladidi suna tafa hannu ko Sallama ba su yi ba, riƙe baki Ladidi ya yi yana maƙale ɗayan hannun ya ce "Ni 'yasu! Me zan gani haka a gidan nan kun kewaye ta?"

Da sauri Abir ta É—ago ganin Ta Sakkwato sai ta ji kamar ta ga mahaifiyarta ne ta yo wajan ta da sauri ta faÉ—a jikinta ta fashe da kuka, sallallami Ta Sakkwato ta dauka tana rungume Abir bakinta har kumfa yake saboda masifa.

"Wace ta ta dakeki? Tashi ki hwaÉ—a min wacce shafaffiya da mai ce ta saka ki kuka?" Ta faÉ—a tana É—ago da ita.

Kasa ce mata komai ta yi dan sai yanzu take jin mugun zafin ƙazafin satar da aka manna mata, Alhaji ya dubi Ta Sakkwato ya ce. "Wai ta ce kuɗi ta sace musu dubu ashirin da biyar, ni kuma ban yarda ta dauka ba."

"kan balastin can! Wallahi kin tabo masifa da bala'i a gidan ga, mi ankayi da wata banzar dubu 25? Wace ta ta taɓa ki hwaɗa min kar ki ji tsoron kowa?" Ta faɗa tana hura hanci sama sai jijjiga jiki take.

Tsayar da kukan Abir ta yi ganin yadda ake ta cacar baki tsakanin su Maman Amal da su Ta Sakkwato, Alhaji da ya ga abin ba na ƙarewa ba ne ya ce "Wallahi yanzun nan zan kira mazajenku su zo, wannan wacce irin rayuwa ce? Ni zan biya kuɗin kar na kuma gani ko da kallon banza kun mata, dan Wallahi daga yau ma ta daina biyan haya kyauta na bar mata daƙin ta yi zaman ta har lokacin da ta ga za ta bar shi."

Ta Sakkwato ta girgiza kai ta ce." Wallahi ina iya waca ma mari Gamboliya, da kai anka haɗe baki anka ƙulla mata sharrin masu sharri?"

Wani farr ya yi da idanu ya kalle ta, gyara zaman jakarsa ya yi ya ba su labarin komai da ya faru har marin da Maman Amal ta yi wa Abir, wata zabura Ta Sakkwato ta yi ta wanka wa Maman Amal mari ta kuma ƙara mata, tana huci ta nuna ta da yatsa ya ce "Wallahi ina iya sumar da ke a gidan ga, ta taɓa zuwa ɗakinki kun yi ɗumi da ita ko amsar wani abu? To ki fita idona in rufe in ba haka ba kotu ce za ta raba mu da ke. Yarinyar ga tun da ta zo nan gidan ga ba ta taɓa ɓata muku rai ba, amma saboda rashin adalci ku ce ta satar muku kuɗi?"

Sosai Maman Amal ta ji zafin marin da Ta Sakkwato ta mata, idan ta ce za ta tanka tasan halin Ta Sakkwato yanzu nan sai ta hau kanta da duka, hakan ya sa ta yi shuru amma haushin Abir ya cika mata zuciya..

Hayaniyar su ce ta tayar da Zaiyan ya fito yana mutsitsika idanu, hango ta ya yi tana goge hawaye kafin ka ce me sai ga shi a gaban ta, a ruÉ—e ya kama hannunta yana kallon ta ya ce. "Anty waye ya sa ki kuka?"

Sabon kuka ta kece da shi ta ruko nasa hannun ta ja shi suka koma gaban ƙofar daƙinsu, hannu ya sa yana share mata hawayen sai tambayarta yake wa ya sa ta kuka? Amma ta kasa ce masa komai. Da wata kalar murya wadda ya yi magana da ita a dajin nan ya ce "Waye ya sa ki kuka Anty."

Da sauri ta kalle shi taga yadda yake tsuke fuska, ba ta san lokacin da ta nuna masa Maman Amal ba cikin kuka ta ce. "Wai ta ce na satan mata kuÉ—i."

Saurin sakin hannun ta ya yi ya yi dogon zari uku sai ga shi a gaban su, tamkar wani zaki haka ya dinga huci ya nuna Maman Amal da hannu ya ce. "Ke!"

A firgice duk suka kalle shi, Maman Amal kuwa ji ta yi kamar ma ta saki fitsari saboda tsoro, huci ya yi ya ce. "Anty ba ta ɗaukan abin da ba nata ba, me ya sa kika saka ta kuka?" Ya faɗa yana ƙoƙarin damƙo ta.

Da sauri Ta Sakkwato ta shiga tsakanin su tana girgiza masa kai ta ce. "Yi hakuri ka ji ɗana, ai na rama mata duk abin da ta mata kar ka ce mata komai mun bi mata haƙƙinta." Ta faɗa tana sa hannu daga baya ta tura Maman Amal baya da ta sanƙare jin muryar Zaiyan kamar wani Soja.

Janye hannunsa ya yi yana huci sai kuma ya yi baya ya koma bai ce komai ba ya dawo inda take, kowa sake da baki yake kallon shi Abir da ta ƙame a jikin bango ta ji ya taɓa fuskarta.

Firgigit ta kalle shi sai ta ga yana ɓata rai kamar zai yi mata kuka, dafe kai ta yi gabadaya ta ma rasa a wani bangare za ta jingina mijin nata, a mai hankali ko mahaukacin da ta sani tun farko? Ko kuma mai ɗan tabin hankali kaɗan? Hannunsa ta ja suka shige ɗaki, ruwa mai sanyi ta ba shi ya sha yana jan numfashi ya kwanta kawai sai bacci. Tagumi ta rafka tana kallon shi cikin wani yanayi na alhini da al'ajabin abin da yake yi wani lokacin, tashi ta yi ta fito waje ta ga duk sun watse ta Sakkwato na ƙofar dakinta sai faɗa take tana gyara kayan miya, murmushi Abir ta yi ganin yadda Ta Sakkwato ta damu da ita kamar ita ta haife ta, ta juya ta dauko wake mai cakuɗe da fari da ja ta iso ta zauna a kusa da Ta Sakkwato suka soma hira...
Chapter 87 · 0% Book details