Sashe 17
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin fushi ya ce "E haka na ce! Kuma ke ba ki isa ki hana Mamana ta shiga cikin gidana ba kin yi kaɗan, Abdul kuma ba ki da ikon hana shi kiran ta ta zo inda yake a duk lokacin da yake so tun da jininsa ce in ba ki sani ba ma yau ki sani, Mahaifiyar Abdul Ƙanwar matar Yaya ce uwa ɗaya uba ɗaya." Ya faɗa yana nuna Mommy da hannu.
"Tsuww! To sai me? Ƙawar ta ce dai ba Ƙanwar ta ba malam gyara maganarka in mantawa ma ka yi." Umma ta faɗa cike da tsanar Mommy.
Daddy ya kuma yin magana a kufule "To yau ai sai ki sani Ƙanwarta ce dan haka banu ruwan ki da lamarin Abir da Abdul." Ya faɗa yana nuna ta da yatsa...
A masifance Umma ta miƙe tsaye ta ce...
*Hmm cakwakiyar familyn Maitama kenan mu je zuwa🤓*
Taku ce dai har kullum Maman Nusaiba.
[10/25, 3:38 Yamma] My Addatyna: _*~A HAKA NAKE SON SHI~*_
*Arewabooks.com: Saratalkasum1897*
_WhatsApp number: +966577675904_
Shafi na goma (10).
A masifance ta miƙe nuna Abdul da yatsa ta ce "Lalle Kabir ban san cewa kai munafiki ba ne sai yau, wai kana nufin Abdul ɗin ne ɗan sister Sadiya? To Wallahi ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa, ni za ku rainawa hankali?"
Sosai ran Daddy ya ɓaci har ya ɗago da niyar mayar mata da martani suka haɗa idanu da Grandma, hakan yasa ya sunkuyar da kanshi ƙasa yana kissima kalar rashin mutumcin da zai yi wa Umma in sun koma part ɗin su. "Na ga kun wani yi shuru kuna kallo na kamar wasu mujiyoyi kun zuba min idanu?" Ta kuma faɗa tana harare-harare saboda takaici, duk zaman ta da Daddy ba ta taɓa sanin Abdul ɗan sister Mommy ba ne sai yau, hakan yasa ta cika ta yi fam sai huci take kamar wata kasa dan ranta ya yi mugun ɓaci, sai yanzu da take kallon Abdul ta ga yadda kamanninsa da Mommy suka fito tar kamar fuskarta ce aka manne mishi. Wani irin tsaki ta ja tana sauke ajiyar zuciya.
Mami jin ta yi jam'i yasa ta kalle ta a wulaƙance ta ce "Duk iskancin ki Wallahi kika ce za ki ja da ni sai na nuna miki bakin rijiya a wajan wasan makaho makaho ne! Ki yi da waɗanda kika raina dai ba da ni ba dan na dama ki na shanye." Ta faɗa tana jan tsaki ta miƙe fuu ta bar palon, ganin haka yasa Fatima ta mara mata baya.
Zage-zage Umma ta dinga yi tana cewa Daddy ya ci amanarta da ya ɓoye mata wannan maganar, shi kuma bai ce mata komai ba ta yi ta faɗa har sai da ya gaji ya ce "Baraka naƙi faɗa mikin ki kama ni ki dakeni tun da ke kika haifeni." Ya faɗa a fusace. Ita ma a fusacen ta ce "Kai dai ka ji kunya, lokacin da na dawo daga America za mu yi aure ba ce min ka yi mahaifiyar Abdul ƙawar Sadiya ba ce? Ashe duk ka lumke ni a baibai ban sani ba ka mayar da ni wata sauna irin ka?."
Grandma ta kalli Umma ta ce "Ke dai Wallahi Baraka an yi asarar haihuwar ki, yanzu mijin naki ne kike faÉ—a wa maganar nan? To fita ki bar min gida ki koma naki tun da ba za ki tsaya a miki bayanin komai ba."
"Dama Inna ai haka za ki ce, saboda mu ba ƙaunar mu kike ba shi ya sa har da ke aka rufe ni da maganar nan."
"To wai dole ne sai an faÉ—a miki dangantakar Mamana da Mommy ne? In an faÉ—a mikin ma mai zai amfane ki da hakan?" Abdul ya faÉ—a yana zaro mata idanu.
"Kai dalla matsa ka ba wa mutane waje, ni ba da kai zan yi ba da ubanka nake da kuma wannan munafukar da take wani cewa za ta yi ƙarana." Ta faɗa tana nuna Mommy ta wuce fuu tana sababi.
Iman ta tashi ta isa gaban Daddy ta durƙusa fuska dauke da damuwa ta ce "Daddy don Allah ka yi haƙuri ka da ka kula Umma, ni na ga lokacin da ta sa hayaƙi dan ta ga Anty Baby ta shigo gidan, ke ma Mommy ki yi haƙuri kar ki biya Umma kin ji." Ta faɗa a sanyaye.
"Ba komai Iman ba zan biya ta ba Allah ya miki albarka." Cewar Mommy.
Amin ta amsa tana dawowa kusa da Abdul ta ruƙo hannayensa murya na rawa ta ce "Ya.. Yaya don Allah ka yi haƙuri da abin da Umma take ma, Wallahi ina ciwon yadda take muku mummunan furuci." Ta ƙarashe maganar tana faɗa wa jikinta, sosai take kuka akan halin mahaifiyarta ta..
Rungume ta ya yi yana shafa bayanta, sosai yake jin son ƙanwa tashi na ratsa shi saboda hankali da nutsuwarta. Ɗago da ita ya yi ya share hawayen har yanzu ya kasa ce mata komai, sai da ta ƙara komawa jikinsa tana faɗin "Don Allah Yaya ka yi haƙuri." Sai a lokacin ya mutaa lips ɗinsa saboda mugun takaicin Umma da ya tsaya masa a rai, ya rasa mai ya mata da take bin da da mugun nufi? Lumshe idanunsa ya yi wanda suka yi jajur saboda ɓacin rai ya buɗe su yana kallon Iman da ta yi lamo a jikinsa tana kuka marar sauti.. "My little karki damu kin ji, ki daina damuwa da halin Umma." Ya faɗa yana sauke numfashi a wahalce saboda da yadda ƙirjinsa ke masa wani kalar zafi..
Murmushi ta yi ta goge hawaye ta ce "Love you Yaya." Ta ƙarasa tana manna masa kiss a kumatu. Shi ma kissing ɗin ta ya yi kamar yadda ta masa sannan ta tashi ta dawo kusa da Abir, kumatunta ta kamo tana murmushi ta ce "Anty Baby kin haƙura ko?"
Kallon ta ta yi cike da so da ƙauna, tana jin daɗin yadda Iman ke damuwa da damuwar su ita da Abdul, ga kuma duk gidan ita kaɗai ke shiga harkar ta su yi wasa da dariya har take mata kallon ƙawa kuma aminiya mai saka ta farin ciki in ta gan ta a damuwa. Itama kumatunta ta ja tana murmushi ta ce "My little ai ni dama kodayaushe ina cikin yim haƙuri karki damu." Ta faɗa tana shafa gefen fuskarta..
Dariyar jin daÉ—i ta yi ta gyara zama..
Daddy ya dubi Grandma ya ce "Wallahi Inna kawai alfarmarki Baraka ke ci am.. Daga masa hannu Grandma ta yi ta ce "Kar ka ƙarasa Kabiru na san da hakan ba daɗin zama kake ji da ita ba, ka yi haƙuri komai zai wuce." To kawai ya ce sannan suka ci gaba da tattaunawa....
Motar da ta ɗauki Zaiyan ta dinga sharara gudu a tsakiyar titi, tun suna gararanba a titina har suka fita daga garin suka kama hanya ɗoɗar. Shi kuwa Zaiyan tun da suka jefa shi a mota ya dinga kiciniyar kwatar kan shi yana ƙoƙarin ɗaukan makaminsa amma da yake sarkin yawa ya fi sakin ƙarfi sai suka danne shi, hannu da ƙafa suka ɗaure masa da ƙyar da suɗin goshi shi ma sai da suka shaƙa masa faudar gusar da hankali. Ko minti goma cikakke bai yi ba faudar ta sake shi ya dinga kwarara ihu yana faɗin "Ina za mu je? Za ku kaini wajan Anty ne?"
Jin abin da ya faÉ—a yasa É—aya daga cikin su ya ce "E can za mu kaika ka ganta ai kana so ko?" Ya faÉ—a a tsorace saboda kafin su É—aure shi ya mangare shi a gefen wuya. Dariya ya yi ya ce "Wallahi kun birge ni."
Ba su sake kula shi ba ya yi ta surutansa har ya gaji ya yi shuru yana kallon gefen hanya ta glass É—in motar ai kuwa ya ga bishiyoyi na gilmawa ya zabura ya ce "Kai ku tsaya ga Anty nan tana bin mu da gudu ku tsaya ta hayo." Ya faÉ—a yana nuna musu bishiyoyin. Su kuma msuka yi banza da shi ya dinga surutu har suka yi tafiya mai nisan gaske, dan sai bayan Magariba suka isa wani gida da ke cikin tsakiyar daji. Hon suka yi aka buÉ—e musu get suka shiga suka yi packing tare da fitowa suka fito da Zaiyan , wanda tun kafin su iso suka rufe masa idanu, ana fito da shi Maigadin Gidan ya kalle shi cikin tausayawa har aka shige da shi ciki..
Palo ne babban wanda yake shaƙe da kujeru irin na taron wajan dinner aure, suna isowa wata murya daga jikin bango ta shiga yin magana.
"Sannun ku da zuwa Jarumai, dama dai ogan ku ya faÉ—a min cewa za ku yi aiki kamar yadda nake so ku shigo ciki da shi."
Jin yadda aka yaba musu kowanne ya shiga hura hanci yana jin kansa shi fitaccacen jarumi ne, suka yi kama-kama biyu suka kama hannuwa biyu suka kama ƙafafuwa suka shige wani ɗaki da shi haske kamar ba Magariba ba. Wani girgegen mutum ne zaune da jajan kaya kansa ɗaure da ɓakin ƙyalle yana ganin su ya kwashe da dariya.
"Hahaha! Wannan ya haɗa duk abin da muke buƙata, amma duk da haka sai an kira Alhaji, ku kira min shi ya zo a gaban shi za ayi komai." Mutumin ya faɗa yana tsoma wani gashin doki dake hannunsa a cikin wani ɓakin ruwa ya zazzaga gashin a fuskar Zaiyan, nan-da-nan Zaiyan ya birkice yana kururuwa saboda tsananin azabar da ta shige shi. Dariya suka yi a tare suna sake matso da shi gaban Mutumin.. Ɗaya daga cikin su ya ɗauki waya ya kira Alhaji yana ɗauka ya koro masa jawabi ya ce ai ga shi a bakin ƙofar gidan zai shigo ciki, bayan ya kashe ya sanar da Mutumin Alhaji ya iso sai suka koma gefe suka ƙame kamar wasu mutanen arziki. Cikin dakakkiyar shadda Alhaji ya shigo yana washe baki na ganin an cika masa aiķinsa ya shiga yi wa Mutumin kirari.
"Nadumbuza mai abin mamaki, yau dai ga shi an cika aiki ba tare da samun wata tangarda ba."