Sashe 82
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shi ma turo nasa bakin ya yi kamar yadda ta yi ya tashi daga kanta ya koma gefen ta ya kwanta yana taɓa gashin kanta, harara ta aika masa ya yi saurin janye hannun ya tashi zaune yana shafa inda ta mintsile shi kamar zai yi kuka, itama ta tashi ta zaune ta kama hannunsa ganin yadda ya yi kicin-kicin da fuska ta sakar masa murmushi ta ce "To yi haƙuri ba zan kuma yi ma ba."
Shi ma murmushin ya mata ta tashi riƙe da hannunsa yana biye da ita suka shiga toilet, wanka ta yi niyar yi sai ta tuna ko soso ba ta da shi bare sabulu, dafe kai ta yi suka yo alwala suka fito..
Bayan sun gabatar da raka'atainun fajur suka zauna ta ɗaga hannu tana ta kwararo musu addu'a shi ma yana maimaita abin da take faɗa, sai da ta ji ana tayar da iƙama sannan ta shafa ta tashi suka yi Sallar. Bayan sun gama Zaiyan ya saka ta a gaba yana kallo, gaban ta ne ya faɗi sosai ganin yadda yake kallon ta kamar mai nazartar wani abu, can dai ya matso kusa da ita ya zauna har suna jiyo numfashin juna ya marairace ya ce "Anty yunwa nake ji." Ya faɗa yana riƙe ciki.
Abicin su na jiya ta janyo ya yi sanyi sosai kasancewar sanyi ya fara shigowa ta tura masa, da sauri ya sa hannu ya jimƙa zai kai baki ta yi saurin riƙe hannun ta ce "Ka ce bismillah."
Dariya ya yi ya faɗi sannan ta sakar masa hannun ya soma cin abincin, tagumi ta yi tana kallon shi yadda yake cin abincin sai ya birge ta, dan haka ta janyo wayarta ta kunna ta dinga masa vidéo bai sani ba, sai da ya gama cin abincin ya haɗe hannayensa ya musu kamar shafa mai, maimakon ta ji haushin abin da ya yi sai kawai ta yi murmushi tana girgiza kai ta aje wayar, kafin ma ta yunkura tuni ya goge hannun nasa a jikin rigarsa, dafe kai ta yi ta kalle shi ganin yadda ya ɓata rigar, ba ta rabu da jimamin abin da ya yi ba sai gani ta yi ya sake mayar da hannu ya kwashe sauran abincin da ya bari ya cinye, wannan karon kuma a fuskarta ya goge hannunsa yana dariya. Takaici da ya mata yawa kawai sai ta fashe da kuka tana kallon shi, da sauri ya matso kusa da ita ya ce. "Anty wa ya sake ki."
Buge masa hannu ta yi tana tsayar da kukan jin hayaniya a tsakar gidan, tashi ta yi ta kama shi suka shiga banɗaki ta wanke masa hannu ya wanke bakin itama da wanke fuskarta sannan suka fito. Kwashe kayan ta yi ta zuba a ledar da aka sayo mata abincin ta aje gefe ta janyo gorar ruwa ta buɗe ta miƙa masa, amsa ya yi ya shanye tas har da lumshe idanu yake sai ta ji ya mugun ba ta tausayi, rabon da ya sha ruwa tun jiya da safe a hôtel, tuna abin da ya faru jiya ya sa ta yi tagumi tana hasaso komai da ya wakana a yammacin jiya. Kenan da Allah ya ba wa 'yan fashin nan rana da tuni sun yi mata faɗe ko ma ta mutu in kwanan ta ya ƙare? To amma ya aka yi suke kiran Zaiyan da Damisa? Shin ko dai dama can sun san shi ne? Tambayoyin da take juya su tana kallon shi yadda ya yi wata kalar murya a jiya shi ya fi matuƙar saka ta kokwanto da kuma al'ajabi, nisawa ta yi ta gyara kwanciyarta shi kuma yana zaune a kan dabarmar yana surutu shi kadai. Tashi shi ma ya yi ya kwanta a gaban ta yana matsa ta can baya ta kai masa duka a gadon baya, daina tura ta ya yi ya juyo suka yi facing ɗin juna ya ƙura mata idanu, saurin rufe idanu ta yi shi ma ganin haka ya rufe nashi...
Karfe 11:Pm na rana suka farka sakamakon kwankwasa ƙofar da ake yi, ɗankwalinta ta zara ta ɗaura ta bude ƙofar , Ta Sakkwato ta gani tsaye bakin ƙofar tana gyara zaman mayafi ganin ta ya sa ta saki murmushi ta ce "Haba Jiddo kwanan ai ya isa haka ki shirya muje na kaiki ki sayo abin da kike so, ko kuma Ladidi ya miki rakiya?" Ta faɗa tana kallon Ladidi da ya iso shi da ƙawar shi cikin shirin fita. Girgiza kai ta yi tana ɗan murmushi ta ce. "A'a Hajiya mu tafi da ke kin ga shi fa namiji ne ni kuma matar aure ce bai kamata ya rakani ba."
Riƙe baki Ladidi ya yi yana kallon Abir ya ce. "To sabon salo lalle a mazaunai, ni 'yasu ! Yanzu ke saboda rashin girmama ɗiya mace haka za ki dinga dangantani da namiji gatsal haka? Gaskiya Ta Sakkwato ki faɗa mata in tana so a gidan nan mu shirya da ita ta daina ce min namiji ehe, dan Wallahi ba ƙaramin aikina ba ne in yi ɗamara mu ba hamata iska." Ya faɗa yana turo ɗankwalli gaba..
Murmushi Abir ta yi ta ce "Allah ya ba ki haƙuri Ladidi."
Farr ya yi da idanu ya gyara zaman handbag ɗinsa ya ce "Ba komai ai ke kin shigo da ƙafar dama."
Komawa ta yi ciki ta canja kaya ta canja wa Zaiyan suka fito tana riƙe da hannunsa, matan gidan duk suka bi da kallo ta kawar da kai tana kallon Ta Sakkwato da take fitowa daga ɗaki, Maman Amal ta kalli Maman Samira ta ce "Ke anya kuwa wannan sabuwar matar da aka kawo mana ba mai girman kai ba ce? Kalli fa yadda take wani daure fuska ko gaishe mu ba ta yi ba."
"Hmm na ga alama gaskiya Maman Amal amma dai kar mu yanke hukunci."
Ƙarasowa ta yi wajan su duk suna kallon ta ta ɗan nusuna ta ce. " kun tashi lafiya ya yara?"
Washe baki suka yi duk suka amsa da lafiya ta juya tana riƙe da hannunsa, wannan karon bai kwaikwaye ta gaisuwa ba sai ma shuru da ya yi yana kallon su.
Maman Samira ta kalli bayan su ta ce. "Kut! Lalle Allah mai halitta, ke Maman Amal kin ga wani santalelan matashi mai jini a jika, anya ma wannan ba balarabe ba ne?"
Itama Maman Amal shi take kallo har suka bar gidan...
Mai adaidaita suka tare suka shiga ta ce ya kai su Kwari, suna tafiya Ladidi na ta ba su labarin wata yarinya a Layin Unguwar tasu wai ta yi ciki, ita dai Abir na jin su suna ta hira Ladidi na shewa har suka iso Kwari..
Suna isa suka suka fara sayayya inda Abir ta sayo duk wani abu da tasan za su buƙata har da ƴar madaidaiciyar freezer ta sayo musu da babbar katifa. Bayan sun gama suka sa a mota suka yo gida. Suna isowa lokacin karfe 12: daidai na rana, zama ta yi tana tunanin yadda za ta dafa abinci ga shi Zaiyan nata korafin zai ci abici, jin haka sai Ta Sakkwato ta zubo masa tuwon shinkafa da miyar taushe amma sam ya ƙi kallo bare ma ya ci, riƙe baki ta yi tana cewa "Ikon Allah! To ba yanzu kake damun mutane da ɗumi ba yunwa kake ji shi ne na kawo ma abincin ka ce ba ka ci? To Wallahi sai ka ci." Ta faɗa tana aje masa abincin a gaban shi. Harɗe hannaye ya yi yana hararar abincin ya ɗago ya kalli Ta Sakkwato fuska daure, saurin tafiya ta yi ganin kalar kallon da ya mata abin ya ba ta tsoro dan ta yi tunanin zai tashi ya dake ta ne. Tana so ta yi girki amma tana tsoron ciwon nata ya tashi, ganin ba yadda ta iya sai ta ɗauki mayafin abaya ta nade hancinta da shi ta janyo rishow ɗin da ta sayo ta buɗe shi a kwallinsa ta fito da shi, mai ta zuba Ladidi yana gefe ta ce ya ba ta ashana ya shiga ɗakinsu ya kawo mata, wutar ta kunna tana ɗaura girkin..
Sai da ta kusa gama girkin ta ji babu abin da ta ji hakan ya sa ta buÉ—e hancinta, buÉ—e tukunyar ta yi tana kawar da kai ta ga ta tafu ta sauke. Ladidi ya taso yana wata kalar tafiya ya iso bakin rishow É—in ya ce "Sannu da aiki."
Gyaɗa masa kai kawai ta yi ta shige ɗaki, ba ta jima ba ta fito da babbar kula ta zuba musu abincin ta zuba wani ta miƙa wa su Ta Sakkwato tana murmushi ta ce "Hajiya ga abinci, don Allah kuma kar ki ce ba za ki ci ba."
Murmushi ta yi ta amsa ta mata godiya ta miƙe ta miƙa wa Ladidi ya amsa yana shewa tare fadin "Allah dai ya biya ƴar madara ai dole mu ci girkin da kika yi."
Girgiza kai ta yi ta koma ta sake dauko wata kular ta zuba ta nufi su Maman Amal, tun kafin ta isa hayaƙin da yake tashi a inda Maman Samira ke girki ya kawo mata ziyara, amma haka ta daure ta toshe hanci ta isa ta sunkuya ta aje musu kular, magana take son yi amma ta kasa saboda ta shaƙi hayaƙi ta yi baya tana riƙe ƙirji tana tari. Da kallo su Maman Amal suka bi ta ganin yadda ta done hanci, Maman Amal ta ce "Wannan yarinyar ƴar rainin hankali ce, diba ki ga yadda take done hanci dan ta zo inda muke." Maman Samira za ta yi magana suka ga ta durƙushe tana tari, da sauri duk suka yo kanta suna tambayar ta lafiya, kasa magana ta yi sai nuna musu ɗakinta take da hannu Ta Sakkwato da ta rikice ta ce "Ku taimaka mu kai ta ɗaka."