← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 120

Sashe 72

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A zabure Kilishi ta yi tana zare idanu, da sauri ta isa bakin gadon baki na rawa ta ce "Maza ka tashi uwar gulmar gidan nan ta zo ga ta nan a palo, ka bi ta kofar baya." Ta faɗa tana janyo doguwar rigarta ta zura da sauri ta zari mayafin rigar ta sa. Da hanzari ya tashi ya bi kofar baya kaya jikinsa a hannu, gyara gadon ta yi da sauri ta cire zanin gadon ta ja bargon ta lullube ko'ina sannan ta nufi wajan mayukan shafawar ta. Sai da ta shafa mai ta saka turare mai ƙamshi sannan ta nufo palon rai a matuƙar bace. Tana isowa ta hade rai cikin masifa ta ce "Ke wacce irin dabba ce Jakadiya? Ba ki ga na sallami masu min hidima a wannan palon ba zan kwanta ke kuma kika kwaso kafafu kika shigo min har kusa da ɗakin bacci na? To meye ma ya kawo ki da daren nan?" Ta faɗa tana zama a kan kujera.

Rausayar da kai ta yi cike da jin haushin ta ce mata dabba, kasa daurewa ta yi ta ce "Ranki ya daɗe ki yi hakuri aikin da kika saka na yi miki ne yake neman lalacewa, shi ne na shigo na leƙa dakin sai na ga Yarima yana bacci a gadonki sai na dawo nan."

Dam! Gaban Kilishi ya faɗi ta yi saurin kallon Jakadiya da ta yi ƙasa da kai, ganin ba ta kallon ta sai ta kawar da tsoron da ta shiga ta ɗaure fuska ta ce "E Yarima ne yake bacci wai ya dawo ya gaji sosai muna magana ya yi bacci, amma ina me jan kunnenki Jakadiya kar ki sake leƙa min ɗaki, ke ko nan palon ban ba ki izini ki shigo min ba ko ma meye ki bari na fito palo na biyu ko na uku sai mu yi magana, ki kula bana son shigigi da shiga inda ban bayar da damar hakan ba. " Ta faɗa tana hamdala da Jakadiya ba ta gane komai ba.

" Tuba nake ranki ya daÉ—e zan kiyaye. "

"Me ya kawo ki ?" Ta faÉ—a tana yatsina fuska.

Gyara zama ta yi ta ce "Ranki aikin da muka yi duk ya tashi a banza, yau dai Yarima ya yi aika-aika ba ki ga ba yadda ya mata, ni ina tunanin ma sai an yi mata dinki." Ta faÉ—a tana dagowa ta kalli Kilishi da ta dafe kirji tana jin wannan gagarumin labari.

Kasa cewa komai Kilishi ta yi ta yi kamar mai sumar zaune sai da Jakadiya ta kira ta sannan ta dawo haiyacinta.

"Ki je Jakadiya zan neme ki ko zuwa jibi ne ni na san mai za ayi, wato Fulani so take ta cusa mana baƙin ciki ni kuma ba zan yarda wata can ta zo ake fifita ta biye da ni ƴar gidan sarauta."

Jakadiya ba ta ce komai ba ta tashi ta tafi tana son komawa part É—in Mamma amma in ta tuna yadda Suhal ya mata tsawa sai ta ji tsoro, haka dai ta nufi sashensu..

_NIGERIA_

Dukkan su Abba ya tattare 'yan gidan a palo gabaÉ—aya, bayan kowa ya zauna Abba ya ce "Wai Yaya Kabir ina Inna take ne? Na fa ce mata za mu tattauna."

Girgiza kai Daddy ya yi ya ce "Inna fa ta bar gidan ma wai ana biki a can rugar su sun tafi ita da Laraba sai nan da sati ko kwana goma za ta dawo, ni na dauka da Mamana za ta tafi amma ta ce sam ba za ta tafi da ita ba ta shaki hayaƙin ruga ta sa ta uku ba."

Sunkuyar da kai Abir ta yi ita dai ba ta ce komai ba, Abdul ya yi sallama ya shigo tare da Salim aka amsa musu, daure fuska ya yi ganin su Fatima zaune har da su Umma, cike da ba da umarni ya kalle su ba alamar wasa ya ce " Ku kuma wa ya ce ku zo taron manya? Ko har da ku za a tattauna ni da Salim mu koma inda muka fito?" Ya faɗa yana hura hanci ganin Abir ya ƙara ɓata masa rai ya daka mata tsawa ya ce "Tashi ki ba wa mutane waje duk kun wani zauna munafukai." Ya faɗa yana kallon Yasmin.

Tashi suka yi sim-sim suka wuce, Abir ma mikewa ta yi za ta tafi Abba ya ce "Dawo Mamana wannan taron dan ku ukun nan aka kira shi."

Dam! Ta ji gaban ta ya faÉ—i ta lallaba ta dawo ta zauna, gabadaya yau ji take kamar ta yi ta kurma ihu ko ta ji sanyi saboda yadda jikinta yake mata wani kalar yanayi wanda ta kasa gane na meye, ga kanta da yake juya mata da ta yi tafiya mai É—an tazara dole sai ta tsaya ta huta..

Gyaran murya Abba ya yi ya ce "Mamana dalilin kiran taron nan na kira shi ne dan ku ukun nan kamar yadda na faÉ—a, muna son haÉ—a ku aure ke da É—an'uwanki Abdul ko kuma Salim, amma dai ni na ga Abdul É—in ya fi dacewa da ke ba Salim ba."

A matuƙar razane suka ɗago suna kallon Abba dukkan su, shi Salim abin da dama yake so ya ji su ba shi Abir wadda yake tsananin so da ƙaunar ta fiye da misali, shi kuwa Abdul da Abir sun san da cewa babu a tsakanin su, Abir tana jin ko da ace akwai aure a tsakanin ta da Yayan nata to fa tabbas za ta dauki Salim ta bar shi, saboda yadda ya tsane ta yanzu ko ganin ta ya yi sai ya ci mata zarafi ya ga hawayenta sannan hankalin shi yake kwanciya, a yayinda shi ma Abdul ɗin yake jin ko da akwai aure tsakanin shi da Abir ba zai aure ta ba dan shi Hafsar shi ta isheshi..

"Kun yi shuru kun kyale, Mamana ke wa kike so a cikin su?"

Wani irin zafi ta ji kanta ya dauka ta runtse idanu, da kyar ta iya cewa "Ni Abba ban son ko ɗaya daga cikin su, Salim Ammi ta tsaneni ba ta sona har su Fatima, shi kuma Yaya gabaɗaya ma ba ya so ya daga idanu ya kalle ni ba zan iya auren wanda ba ya ƙauna ta ba, ballantana ma babu aure a tsakanina da Yaya har abada ina da wanda nake so yake so na."

Baki sake duk suke kallon ta Ammi ta yi murmushi ta ji daÉ—i da Abir ta ce ba ta son Salim dan ko da ta amince sai ta hana auren, ita kuwa Umma turo É—ankwalinta gaba ta yi tana kallon su tana gyada kai irin an faranta mata rai É—in nan. Abba ya ce "To me ya sa kika ce babu aure a tsakanin ki da Abdul Mamana?"

Kai tsaye ta ce "Saboda Mom ce ta shayar da shi har ya kai mawar yaye."

Salati Umma ta dauka kamar da gaske ta riƙe baki tana jinjina kai, kallon Abir ta yi ta ce "Wai kina nufin nono ɗaya kuka sha ke da Abdul?" Gyaɗa mata kai Abir ta yi tana sauke numfashi, tambayar Abdul Abba ya yi ya ƙara tabbatar musu babu aure a tsakanin shi da Abir sai dai Salim shi kuwa ta ce ba ta so.

"To in ba ki son Salim waye wanda kika fitar a matsayin miji? Kin ga su Yasmin sun samu mazajen aure ita da Khairat sauran Fatima ya rage."

Shuru ta yi tana wasa da yatsu hannunta hakan ya ɓata wa Abdul rai ya saka mata tsawa ya ce ta faɗi waye. Ji ta yi ta gaji da wannan ƙuncin na gidansu kai tsaye ta ce " Abba ni ku aura min Zaiyan sai na ci gaba da kulawa da shi. "

Kwalalo idanu waye suka yi suka hada baki wajan fadin "Zaiyan..."

_Maman Nusaiba ce_
[6/20, 8:43 PM] Ummu Amjad: ~A HAKA NAKE SON SHI~

Shafi na (35)

Ji ta yi sun ma ɓata mata rai da suka hada baki wajan kiran sunan Zaiyan, hura hanci ta yi tana jin gara ta ɗauki wannan kasadar da ta ci gaba da zama a gidan nan suna ƙunsa mata baƙin ciki. Ɗago kai ta yi kan ta tsaye ta dubi Abba ta ce "E shi fa Abba, ina son shi sosai kuma zan zauna da shi har karshen rayuwata, ko ba komai zan samu ladan kula da shi kuma in sha Allah ina sa ran nan gaba zai samu lafiya. Ina so zan nema masa magani ko da ba a ƙasar nan ba ne zan tafi kowacce ƙasa wajan ganin ya samu lafiya kamar kowa." Ta faɗa idanuwanta na zubar da hawaye ; ji take in dai ba a aura mata Zaiyan ba to tabbas za ta iya mutuwa.

Ƴar dariya Umma ta yi tana tafa hannu wannan abu yana yi mata suga wai Mahaukaci take so? Daure fuska ta yi ta ce "Haba Abir yanzu ki rasa wa za ki ce ki na so sai mahaukaci wanda bai ma san rayuwar duniya ba? Anya kuwa ki na cikin haiyacinki Abir?" Ta faɗa tana riƙe haɓa alamar mamaki.

Ammi da ta yi shuru tana jinjina lamarin sai kawai ta rafka tagumi, can dai ta nisa ta ce "Abir ke yanzu in aka ce ki auri Zaiyan sai ki aure shi dan kema ki na mahaukaciya irin shi? Ya za ayi mu yarda jininmu ta auri mahaukaci ki dai sake magana ba dai wannan ba, idan kin ce ba ki son Salim ba wani abu ba ne mu ba za mu bari ayi miki auren dole ba, sai ki kawo wani. "

Ran Abir ne ya ƙara ɓaci taya ma tana ce musu ga wanda take so amma a ce mata wai ba shi ba, a fusace ta ɗago ta kalli Ammi cikin tabbatar mata da maganar ta ce " E shi ɗin dai *A HAKA NAKE SON SHI* a haka zan zauna da shi, ina ce dai ni zan zauna ba wani ba ko? To ku aura min shi na bar muku gidan gabaɗaya tun da dama ai ba son gani na kuke ba." Ta faɗa tana huci gabaɗaya ma gani take so suke su hana su Abba yin magana..
Chapter 72 · 0% Book details