← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 120

Sashe 113

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Cikin dare Abdulwahid ya tashi ya haɗa kan kayansa kamar mai zuwa inda ya saba kasuwanci ya bi ta kofar da babu masu tsaro ya bar gidan, gari na wayewa aka nemi shi aka rasa aka yi ta neman sa amma ba a gan shi ba. Abu kamar wasa ya ɓata fat Sauraniya ta yi ta kuka ta ci gaba da addu'ar Allah ya bayyana mata yaronta, ita kuwa Fulani Abida dan murna ji ta yi kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha, haka aka shafe shekara ba ya nan karshe ma aka wayi gari companynsa ya ƙone ƙirmus babu abin da aka fitar, wannan abu ya ƙara tayar wa da Sarauniya hankali har ta kwanta ciwo karshe ya yi ajalinta. Gida ya dawo na Fulani Abida ta dinga zuba mulkinta son rai, karshe ma ta nemo wa Yarima Haris mata biyu ɗaya ɗiyar sarkin Maradi ce ɗaya kuma ɗiyar sarkin Dosso ce, aka yi biki aka kai su gidajensu. Rashin lafiya ta kama Mai martaba dole ya sauka ya ɗaura Haris akan karagar mulki, burin Fulani Abida ya cika ɗanta ya zama sarki sai abin da ta ce a tsartar a masarautar ake yi. Sarki na kwance sai an kwantar sai an tayar ba wanda yake kula da shi saboda gabaɗaya an sa kowa ya manta ma da shi, wazirinsa ne kaɗai ya garara mantawa da shi shi ke zuwa ɗakin da aka kai shi yake kula da komai, ganin haka ya sa Fulani ta sa Haris ya cire shi a matsayin Wazirinsa, shi kuma ya yi hamdala saboda dama ba ɗaukan shawararsa Haris ke yi ba...

Haka rayuwata ta ci gaba da tafiya da daɗi ba daɗi, sai da Abdulwahid ya shafe shekaru goma sha biyu cif kwatsam wata rana sai ga Abdulwahid ya bayyana tare da matarsa. Bayan an zauna aka sha zuwa ganinsa kowa na murna ya dawo, bayan an tashi ya tambayi ina mamansa? Fulani da yake makira ce ta fashe da kuka ta ce ai ɓacewar shi ce ta sa ta kamu da ciwo karshe ta rasu, ya sha kuka sosai tukun ya gabatar musu da matarsa Husna.. Bayan ya dawo sai ga Mai marbata ya miƙe tsam akan ƙafafuwansa, sosai Abdulwahid ya ji daɗi matuƙa ya ci gaba da kula da shi, Fulani na bin su ta ƙarƙashin ƙasa har sai da ta tabbatar ta kulle bakin Sarki dan kar ya ce zai sauke ɗanta ya maye gurbinsa da Abdulwahid, shi kuma a lokacin ta babansa yake bai damu da wata sarauta ba, amma hakan bai gamsar da ita ba sai ta kira shi suka zauna da Sarki da shi, nan take sanar da shi ai tun da ya dawo kuma shi ne babba ya amshi mulki daga hannun ƙanensa. Hankalinsa ya tashi ya ce shi fa ba zai taɓa hawa kan kujerar mulki ba ya bar wa Haris girman ya ci gaba da mulki, hakan ya mata daɗi amma a fili ta ce masa me ya sa bai dauke ta a matsayin uwa ba har zai bijire wa umarninta? Haƙuri ya yi ta ba ta ƙarshe ta ce ta haƙura tukun suka tashi, haka ta dinga sa Husna a jiki tana bugun cikin akan rayuwar da suka yi, inda ita kuma a ganin ta ai ta zame musu uwa ta faɗa mata komai da ya faru da su, in da ta ce mata bayan an sa musu wuta hayaƙi ya rufe su, ita ta fara farfaɗowa daga suma ta nufi mijinta da yake kwance cikin jini yana numfashi sama-sama. Ƙarshe dai ya tashi suka samu suka fita ta ƙofar baya, in da suka yi tafiya mai nisa duk da suna cikin jigata, sun galabaita matuƙa gara ma ita akan Abdulwahid da fita jigata, suna zuwa tafiya a hankali ba su san inda kan su yake ba har suka faɗa gefen hanya suka nufi daji, suna zuwa saitin wata bishiya suka kasa tafiya nan suka zube zuwa lokacin ba su da ƙarfin da za su iya taka kafafuwansu...

Sai da gari ya waye suka tashi in da suka gan su cikin wata Bukka ta Fulani, sosai Husna ta yi mamaki shi Abdulwahid sun sa masa magani a inda aka harbe shi sun daure wajan. Sai da suka yi sati sannan Husna ta warware shi kuma Abdulwahid bai ƙarasa warkewa ba ana ci gaba da masa magani, haka suka ci gaba da zama da fulanin nan da ke bayan gari har ya warke tas. Sai a lokacin ɗan Fulani ya zauna ya sanar da su cewar sun tafo su dayawa za su dawo gida daga cikin gari nan suka gan su jikin wata bisjiya, da farko sun ki ɗaukan su dan tsoro suka ji ko sun mutu sai daga baya suka duba suka ga baccin wahala ne suke, sai suka ɗauke su suka tafo da su Ruga suka yi musu magani. Godiya sosai su Husna suka yi musu inda Abdulwahid ya nemi da su musu alfarma su ci gaba da zama da su, suka ce ba matsala. Haka suke rayuwa a cikin Ruga har sai da suka yi shekara sannan hankalin Abdulwahid ya karkata kan gida, haka suka shirya suka bar Rugar in da suka dawo gari suka yo shigar Fulani Baffa ya kai su tasha suka shiga mota suka bar Nigeria. Bayan sun sha tafiya ta kwana hudu suka iso Niamey inda daret suka yo gidan Sarauta. Ko da Husna ta zo nan a labarin Fulani Abida ta sa kukan ƙarya tana cewa ai yanzu komai ya wuce. Kin ji ta yadda aka yi suka dawo Niamey. " Ya faɗa yana sauke numfashi tare da kallon Abir da ta yi tagumi. Jin sun yi shuru ya sai ya ci gaba da cewa "Rayuwa na tafiya in da Abdulwahid ya koma kan kasuwancinsa ya kuma samu albarka, mahaifinsa ya ba shi kudade masu yawa ya ce ya ja jari, wannan abu ya ƙona zuciyar Fulani sai ta sa a ƙara durkusar da shi amma sam abin ya garara, dan ko da Jakadiya ta je wajan bokan da ya mata magani ta tarar ya mutu har ya kumbura ya soma tsami, haka ta dawo hankali tashe ta sanar da Fulani. Tun da ta samu labarin mutuwar boka sai ta bi ta wata hanyar, da makirci irin nasu na mata da nuna tana son Abdulwahid da matarsa ta sa Mai martaba ya umarci Abdulwahid ya ƙaro mata biyu tun da shi ne babba a gidan, da farko bai Mai martaba bai amince ba haka ta dinga bi ta hanyoyi da dama har ta samu ta shayo kan shi, washegari ya kira Abdulwahid ya sanar da shi abin da yake so in da shi kuma bai yi muso ba ya yi biyayya ya auri ɗiyan abokan mahaifinsa. Bayan an yi auren ta ƙara samun dama tana jan kishiyoyin Husna a jiki duk dan ta kuntata mata, ita kuma ta nuna ba ta san tana yi ba. Ta samu labarin wani boka nan da nan ta tura Jakadiya ta amso mata magani dan a saka wa Husna ta ci ta kamu da ciwo wanda ba za ta mutu kai tsaye ba sai ta yi azabtuwa, ana kawo mata maganin ta shirya musu cin abinci a part ɗinta ta sa wannan magani a cikin abincin da ta ware wa Husna. Zumuɗin da take ya sa ta manta abincin da ta zuba wa magani shi ne ta ci, da dare ta dinga kurma ihu saboda mugun zafin da take ji a cikin naman jikinta.
Chapter 113 · 0% Book details