Sashe 91
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sallolin da suke kan ta ta gabatar ɗaya bayan ɗaya tana yi yana biye da ita duk abin da ta yi sai ya yi, bayan ta shafa fatiha ne ta soma tunanin abin da za ta dafa musu ga shi kuma kuɗin hannun nata ya yi ƙasa sosai, dubu goma kacal ya rage mata a cikin dubu ɗari da hamsin da ta zo da su garin kash a hannu, sai dollars guda biyu gareta wanda kyauta ce da Abdul ya mata ranar zayayowar haihuwar ta. Nisawa ta yi tana dafe jikin jin yadda ake mata rugugin da ya haifar da rage kuzarinta, lumshe idanu ta yi sai kuma ta tashi tsaye ta nufi wajan kayan abincin su, taliya leda biyar gare su sai sauran shinkafar su da ta yi ƙasa sosai a cikin buhun, leda ɗaya ta dauko ta haɗo kan kayan miya ta fito waje ta zauna a kusa da rishow ɗin ta. Ladidi da yake ƙoƙarin fidda abincin su na sayarwa ya dakata da fitar, kallon ƙarfin hali ya mata ya iso inda take zaune tana ƙoƙarin tayar da wuta, tsayawa ya yi a gefe yana tafa hannu kamar wanda ya ga abin da ya shallake tunaninsa, ya ce. "Haba ƴar shawalwala, yanzu kuma girkin meye za ki ɗaura?"
A matuƙar gajiye ta ɗago ta kalle shi, ita kan ta tasan ƙarfin hali ne take makaho da shiga rijiya, daina ɗaura abincin ta yi hango manyan kulolin kayan abincin su da zai fitar, ta ce "Ladidi tun da ka dafa abincin ka zuba mana wanda za mu ci ni da Zaiyan sai ka faɗa min nawa zan bayar." Ta faɗa tana sauke tukunyar da ta ɗaura. Ladidi bai ce mata komai ba ya nufi ɗakinsu da hanzari, wata yar madaidaiciyar kula ya dauko ya iso wajan abincin, sai da ya cika ta taf da shinka dafa-duka da naman ta ya kawo mata, ta amsa ta miƙe tare da cewa "To tsaya na dauko kuɗin nawa ne?"
Gyara zaman mafinsa ya yi tare da karkace kai ya ce "Kin ga ban ce ki ba ni ko sisin kwabo ba, ki je ku ci dan shi ma kan shi mijin naki tun da kika fita har kawo yanzu bai ci komai ba yana ambaton sunanki." Yana gama faÉ—in haka ya wuce ya dauke abincin ya wuce..
Murmushi ta yi tana bin bayan shi da kallo, tana kuma jinjina kirki irin na Ladidi matsalar shi ɗaya kawai Daudu, wanda ta ce masa ya dawo yadda yake ranar sai da ya wuni bai shiga sabgar ta ba yana fushi. Ɗakin ta shiga ta aje abincin ganin Zaiyan kwance yana rawar sanyi, da hanzari ta iso ta aje abincin tare da kamo shi ta ɗago da shi tana bin shi da kallo, wuyansa ta taɓa ta ji zafi rau ta shafea kansa kamar za ta fashe da kuka ta ce "Ka gani ko? Ban so ka yi wankan nan na Magariba ba ga shi yanzu zazzabi ya rufe ka, tashi ka ci abinci sai na sa a sayo ma magani ka sha." Ta gyara masa zama yadda zai ji daɗin cin abinci, budewa ta yi ta sa masa a gaba ya yi saurin kai hannu zai ci ta riƙe, da kallo ya bi hannun nasu sai kuma ya ƙura mata ido bai ce komai ba, ta harare shi ta ce "Ka ce Bismillah."
Æata fuska ya yi yana turo baki ya yi bismillah sannan ta sakar masa hannun ya soma ci.
Zuba masa na mujiya ta yi tare da rafka tagumi tana ƙara jin tsananin so da kaunar sa na ratsa kowanni ɓargo da jijiya na jikinta, sauke hannun ta yi ta kalli kular abincin ta ga ya cinye bai fi loma uku ba ya bari yana karkaɗe wanda ya zubar masa a jiki, mamaki sosai ta yi ganin yawan abincin ta miƙa hannu ta dauke da nufi ta cinye amma ta ga ya warce, hawaye suka cika mata idanu saboda yadda cikinta ke neman agaji gaggawa har wani zagawa kanta yake. Haƙura ta yi ta miƙa masa ya amsa ya dauko sai ta ga ya kai bakinta, da sauri ta amsa tamkar marayan da ya kwana bai ci ba, yana gama ba ta ta ga ya tashi ya nufi banɗaki , bin shi ta yi da kallo cike da ta'ajjibin abin da ya yi ta miƙe ta bi bayan sa..
Wanke hannu ta ga ya yi ya kurkure baki ya juyo ya kalle ta, mayar da kansa ya yi ya ci gaba da goge bakin ita kuma ta yi ƙiƙam kamar an dasa ta, tana wata duniyar ta ji ya yanyo hannunta yana wankewa, bayan sun gama suka fito...
Sai bayan Sallar Isha'i ta fito lokacin Ta Sakkwato ta fito waje tana waya sai sababi take, sai da ta gama ta É—an rusuna ta ce "Mama barka da dare, don Allah akwai maganin zazzabi a wajan ki?"
Sauke wayar ta yi ta kama hannunta suka zauna ta kalle ta da kyau, sannan ta ce "Jiddo amma dai ba ki ci abinci ba ko?"
Murmushi kawai ta yi, hakan ya ba ta damar ci gaba, "Wai ni tsaya ma shin ba kin ce min ki na da cutar asmah ba?"
Gyada mata kai ta yi ta ɗaura, "Kuma jiya na ga kin yi girki da gawayi amma ciwon naki bai tashi ba, shi ne nake ta mamaki saboda an ce masu irin cutar basa son hayaƙi ko su yi gudu hakan zai tasar da ciwon nasu, ke kuma jiya kin tari hayaƙi ba ki yi komai ba."
Murmushi ta yi ta ce. "Mama ni ma kaina na yi matuƙar mamakin hakan, saboda gas ɗi na ya ƙare na amshi gawayi a wajan Gamboliya ina jin tsoro haka na ɗaura, sai ga shi dai Alhamdu Lillah har na gama ban ji komai ba, gara ma ɗazu da ina sauri ina haɗawa da ɗan gudu naji kamar ciwon zai tashi amma yanzu Alhamdu Lillah bai tashi ba. Kila ko Ubangiji ne ya amshi Addu'ar da nake ba dare ba rana akan wannan ciwon nawa, saboda yadda na tsinci kaina a cikin jarrabawar rayuwa sosai hankalina ke tashi in zan yi girki, ina addu'a Allah ya sa karshen wahala ta ta zo akan wannan ciwo da nake fama da shi tun ina karama." Ta faɗa tana goge hawayen da suka zubo mata.
Dafata Ta Sakkwato ta yi tana girgiza mata kai, sannan ta ce "Jiddo ya kamata ace kin fara sana'ar da za ta riƙe ku da sauran kuɗin da ya rage hannunki, kin ga in kina biɗar wani abu ba sai kin wahala sosai ba tun da kina da abin yi, ina kuma fatan Allah ya sa hanyar warkewa ce Allah ya kawo miki a daidai lokacin da kike tsananin buƙatar hakan. Amma waye ya sace ki? Ki hwaɗa min komai kinjiya karki boye min wani abu dan ke kamar ɗiyata ta ce. "
Share wahaye ta yi ta ce " Mama na gode da irin yadda kike nuna damuwar ki a kanmu ni da mijina Allah ya biya ki, in sha Allah zan soma sana'a saboda kuɗin da ke hannuna sun kusa ƙarewa saura kaɗan, amma zan kai dollars a bani naira sai na ga me zan ke sayarwa. Wani mutum ne ya sa aka sato masa ni wai so na yake zai aure ni. "
Kwalalo Idanu Ta Sakkwato ta yi ta ce "Auren ki zai yi? To ba ki ce masa ke tun tuni an miki aure ba?"
Nisawa ta yi ta ce "Na sanar da shi Wallahi..Nan dai ta kwashe komai ta sanar mata."
Dafe ƙirji kawai ta Sakkwato ta yi tana zaro idanu, sai da ta jima tana juya lamarin a ranta sannan ta ce "In sha Allah babu abin da zai miki, kuma ba zai sake dauke ki ba, shi mahaukacin ina ne da zai ce yana son matar aure? Anya ma wagga yaro ya yi karatun addini kuwa? Ni yanzu ba wannan ba, kin iya irin sana'o'i na hannu?"
Gyada mata kai ta yi ta ce "Na iya kitso da ƙunshi, ina yi wa Iman wani lokacin har Laraba ina yi wa, ƙunshi kuma musamman aji na shiga aka koya min a lokacin na shiga da zummar nake yi wa kaina ba sai naje na biya kuɗi ba an yi mini, tun ban iya ba har na kware amma ba wanda nake wa sai ƙanwata Iman, dan duk gidanmu ita kaɗai ce take hulɗa da ni. "
Gyara zama Ta Sakkwato ta yi ta ce "Ma sha Allah, to ai kuwa zan samo miki customer sosai dan duk Layin nan mace É—aya ce take kitso, mai lallen kuwa sun tashi. In sha Allah zan sayo miki kayan lallen da kuma kayan kitson ki fara yi min har lalle sai na nunawa kawayena."
Wani sanyi ta ji ya ziyarci masarrafarta sosai ta ji daÉ—in wannan bayani, haka suka cigaba da hira....
Gari na wayewa Ta Sakkwato ta tsife kitson kanta ta zauna Abir ta yarfa mata kitso na gani na faÉ—a, su Maman Amal suka dinga yaba kitson yadda ta yi mai kyau sosai kowa sai yabawa yake, hakan ya sa Ta Sakkwato ta dube su fuska a É—an daure ta ce "Kun ga idan har idanuwanku sun ga abin da zuciyarku ta yaba to yana da kyau ku ce ma sha Allah ko da ba a fili ba ne, ku daina hwaÉ—in magana kai tsaye ba tare da kun ce ma sha Allah ba."
Maman Samira ta rausayar da kai ta ce "Yi hakuri Ta Sakkwato in sha Allah ba za mu kuma zuzuta abin da ya birge mu ba tare da min ce ma sha Allah ba."
Hanci ta hura tana cewa "To ni dai na hwaÉ—a muku gaskiya ku gyara."
To suka ce mata Abir na ta murmushi duk suka zauna a gaban ta Maman Amal ta ce "Don Allah Jiddo za ki yi min irin kitson da kika yi wa Ta Sakkwato? Kuma nawa zan ba da? Dan gaskiya ya yi min matuƙa kin ga mijina gobe da dare zai dawo ki min har da lalle tun da Ta Sakkwato ta ce har shi ma kin iya, sai ki min lissafi naji nawa ne."