Sashe 56
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Ranar na yi farin ciki marar musaltuwa na yi ta yi wa Abban Abir godiya har da kuka ganin yadda ya inganta rayuwar yaran Baba Malam, ya saka su a makaranta boko da Islamiya ya saya musu gida É—an madaidaici, har shi kan sa Baba Malam É—in ya ba si jari ya dinga sayar da kayan abinci irin su shinkafa, taliya, kayan miya, da dai sauran su..
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya har Allah ya yi wa Abokin Abban Abir Alhaji Mustapha dawowa daga America, nan fa suka ɓarke da zuminci har ni da matarsa muna ziyartar juna. Samun ta a daidai wannan lokaci ya min daɗi saboda Hajiya Nafisa mace ce mai wayewa da girmama mutum, sosai muke zuminci har muka zama Aminan juna inda da an yi hutu za ta buƙaci na kai mata Abir na sa a kai ta da ƴarta Hafsat su yi ta wasa, hakan ya sa naji kamar Hajara ce ko Usaina a tare da ni babu abin da nake boye mata na rayuwata itama ba ta boye min komai nata..
Matsalar daya Abir ba ta son zuwa gidan su tun da ta kai shekaru 10 ta daina zuwa, ko Hafsat ta zo gidanmu sai ta yi ta share ta ita kuma ba ta zuciya da an sake hutu sai ta dawo.. Tun da kowa ya san Abir na da wannan ciwon ba damar ta fita cikin su Yasmin wasa sai su ja ta cikin gidan su, Farida ko Baraka da sun gan ta za su sa turaren wuta ya yi hayaƙi sosai sai su rufe kitchen ɗin su ce mata ta zo ta dauko musu ruwa ko cup, da ta shiga numfashinta zai sarƙe ta yi ta fama in sun ga tana neman mutuwa sai su dauko ta su kawo ta bakin kofa su koma da gudu, an yi haka ya fi sau biyar na gaji na je har part ɗin su na ci mutumcin su na kuma faɗa wa mazajensu komai, ranar sai da kowacce ta kwana a gidan su dan sun ce ba za su yarda suke wulaƙanta musu ɗiyar ɗan'uwa ba itama mutum ce mai gata fiye da kowa na gidan, hakan ya tada fitina suka kore su har sai da suka yi kwana biyu sannan aka dawo da su.. Tun daga ranar suka ƙara tsanar ta ni ma da na san da haka na hana ta zuwa inda suke, a lokacin kai kuma kana can wajan ƙanwar su Kabir Yasira da ke Gemerny. Sosai Allah ya buɗa wa Abban Abir dan kaf family Maitama babu wanda ya kama ƙafarsa a kuɗi har wanda suke ƙasar waje duk ba su kai shi kuɗi ba, hakan ya sa Hajiya ke ta shiga da fita wajan ganin ƴarta ta aure shi, shi kuma ya ce mata ba ya buƙatar wani aure ni kadai na ishe shi a rayuwa, ai kuwa ta dinga kukan markici ta ce na asirce shi dole ya ce ba zai min kishiya ba ya yi ruwan rogo da ita har ta gama sababin ta ta tafi..
Kwatsam wata rana aka turo min saƙo wai na faɗi inda mijina yake aje kuɗi ko a kashe shi da Abir, na tsorata da ganin wannan saƙon na kasa zaune na kasa tsaye har sai da ya dawo na ba shi ya karanta ya ce na share 'yan damfara ne, ban yi masa muso ba na share maganar amma kullum ina cikin zullumi a zuciyata. Haka aka ci gaba da turo min saƙon safe da yamma wani lokacin ma har da dare ake turo min, duk na tattara na watsar ko an turo bana bi ta kai karshe dai na kai number wajan ɗan gidan Baba Malam saboda ya karanci computer na ce ya min bincike a kan layi ana yawan kira na da shi, a take ya dauko kayan aikin shi ya shiga bincike inda ya ce min ai mai kiran nawa yana cikin daji ne. Hankali na ya tashi ina ta tsoro ko yan bindiga ne haka dai na dawo gida na sanar da Abban Abir komai ya ce kar na damu babu abin da zai same ni sai alkhairi..
Kwana biyu na ga Abban Abir na yawan tunani ba tambaye shi ko lafiya? Sai ya ce min ba komai wasu kaya yake tuna lissafin su, ranar kai ka tafi aiki ita kuma Abir tana gida Abban ta ya ce ta raka shi zai je sayan shanu rugar su Inna, tana murna ta raka dauko mayafi suka tafi, wannan rana ita ce ganina na karshe da shi sai gawar shi da aka kawo bayan sun kashe shi. Kuma har yau mai yi min barazanar nan bai daina bibiyata ba sai tambaya ta yake abin da ban sani, amma ni dai na san Abban Abir ya ba ni wasu takardu da kuma wata yar akwati ƙarama yar madaidaiciya ya ce na aje a wajena kar na bari kowa ya gani, tabbs in har hasashe na ya zama gaskiya akwai abin da yake cikin wannan akwatin wanda shi ne mai min barazanar nan yake son na ba shi, ban kawo shi ba ne sai da na tuna da ya ce kar na bari kowa ya sani..."
Dogon numfashi Abdul ya sauke yana murza hannun Mom ganin yadda bakin ta ya bushe ƙamas, cikin muryar da ke nuna tsananin damuwar da yake ciki ya ce "Mom yanzu ina wannan akwati da takardun suke?"
Fisgar numfashi ta yi ta runtse idanu tana juya kai irin na wanda yake cikin tsananin azaba, sai da ta ɗan jima sannan ta ce "Idan ka shiga ɗakina ka buɗe inda nake saka kayana can ƙarshe ka laliba za ka ji wata leda, in ka ɗauko to ita ce akwatin takardun kuma na bai wa Abir ta aje a wajan ta dan ta ce min Abban ta ya ba ta wata takarda ba ta ma duba ba ta ɓoye ta, kuma na ga...." Tari ne ya sarƙe ta ta dinga aman jini, hankali a tashe Abdul ya fita suka yi kiciɓus da Doctor Hashim a bakin ƙofa, da sauri su Grandma suka shigo ita da Hafsat da Iman Ammi kuwa tuni ta gaji da jira ta yi tafiyar ta. Duba ta ya soma yi bakinta na mutsawa jikinta na ƙyarma ta ɗamko hannun Abdul ta ɗaura a na Abir tana kallon su hawaye na gangarowa kan kuncinta zuwa cikin kunnenta, kuka sosai Abir ke yi tana faɗin "Mom don Allah ki tashi kar ki min haka, ki tashi Mom kar na zama marainiya gaba da baya."
Jikin ta ne ya saki idanuwanta suka rufe ruf kamar mai bacci, Doctor Hashim ya cire mata garin jini da ruwan da ake mata ya fidda mata robar da aka sa mata a hanci ya janyo zanin ya rufe mata fuska. A kiÉ—ime Abdul ya kalli Doctor Hashim ya ce "Ba... Ban gane ba na ga ka rufe mata fuska?"
Zagayowa ya yi ya dafe kafaÉ—arsa ya ce "Am so sorry Abokina Mom ta amsa kiran Mahalicci."
Wata irin zabura Abir ta yi ta fasa kuka É—if kukan ya É—auke sakamakon numfashinta da ya dauke, da sauri Abdul ya dauke ta suka nufi waje shi da Doctor Hashim yana kiran nurses..
Inna da su Iman kuka suke har wata nurse ta zo ta ce su fito waje, a bakin kofa suka tsaya Abdul ya fito daga ɗakin da aka kwantar da Abir ya rasa me zai yi kuka zai yi ko kawai ya yi ta buga kamshi da jikin bango ko zai ji sauki? Hannun Grandma ya kama ya zaunar da ita ya ce zai kira su Abba a waya ya sanar da su, Inna ta riƙe kai ta ce "Bar ni in yi kuka Abdullahi, Allah sarki Sadiya baiwar Allah."
Kiran Abba ya yi yana ɗagawa ya ji kuka ya zo masa ya danne murya na rawa ya ce "Ab.. Abba please ku zo Asibitin Hashim Mom ce.." Kasa ƙarasawa ya yi saboda kukan da ya hana shi yin maganar har karshe.
Zabura Abba ya yi ya tashi daga kan kujerar da zaman sa kenan ya dawo daga office, a ruÉ—e yake magana. "Abdul me ya faru da matar Yaya?".
Da ƙyar ya daure ya iya faɗa masa mutuwa ta yi, nan Abba ya dinga maimaita Inna lillahi wa inna laihin raji'un! Ya ce ga su nan zuwa. Aje wayar ya yi ya jingina a jikin bangon Asibiti yana zubar da wahaye na rashin Mom.
Suna nan sai ga Abba da Salim da Daddyn Aruf sun iso hankali tashe, dakin ya nuna musu aka fito da gawar Mom suka wuce da ita gida, Abir kuma Iman da Hafsat suka tsaya a wajan ta kafin ta farfado daga suma da ta yi..
Haka aka yi wa Mom wanka aka kai ta gidan ta na gaskiya, sai a lokacin Abdul ya ji wani irin kewar Mom ta rufe shi ya shiga É—aki ya rufe kan shi ya dinga kuka mai tsuma zuciya.."
Taku har kullum Maman Nusaiba
[11/1, 10:19 Yamma] Anty Sarat (Mom Nusy 🌹): ~A HAKA NAKE SON SHI~
ðŸ¥+966577675904
Shafi na (28)