← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 120

Sashe 92

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sunkuyar da kai ta yi ta ce "Ai ku yan gida ne ba sai kun biya ba."

Ta Sakkwato da ta fito daga É—aki ta yi caraf ta ce "Babu maccen da za ki yi wa kitso a sadaka, dan kowacce mijinta yana ba ta kuÉ—i in za ta yi, in kina so a miki wannan kitson irin na manyan Hajiyoyi da lalle dubu biyu za ki ba da."

Waro idanu Maman Amal ta yi ta ce "Haba Ta Sakkwato dubu biyu kuma? Gaskiya a rage min ni fa Æ´ar gida ce, duka ma kuÉ—in da aka bani dubu É—aya ne na kashe É—ari uku a ciki sai É—ari bakwai ya rage."

Ta Sakkwato ta kada kai ta ce. "To kin ga Kuwa dole ayi miki na daidai kuÉ—inki ba irin nawa ba, ko ni biya zan yi dubu uku ma ni zan ba ta cif."

Ita dai Abir ba ta ce ba komai sai murmushi take da an jima ta leka Zaiyan da yake ta bacci tun na dare bai tashi ba..

Bayan ta gama yi mata lalle suka dinga yabawa Ta Sakkwato na sababi ta ce dole su ce ma sha Allah kar bakinsu ya faÉ—a Æ´ar mutane, suka ce to..

Washegari da rana ta yi wa Maman Amal kitso da ƙunshi, sosai lallen ya birge Maman Amal ta dauko waya ta ce ayi mata photo ta turawa Baban Amal ya gani kafin ma ya iso, ganin wayar ba za ta fito da kyan ƙunshin ba Abir ta ce "Jira bari na dauko wayata na miki da ita za ta fi haskawa."

ÆŠaki ta shiga ta dauko iPhone É—in ta suka dinga bin wayar da kallo, sai yanzu suka sake tabbatar da cewa lalle fa duk inda Abir ta fito É—iyar masu hannu da shuni ce.

Photo ta yi har da ɗan short video ta yi wa kitson ƙunshin ta yi iya photo, Ta Sakkwato ta ce ta dauki nata ƙunshi da kitson ta buɗe account take tallata sana'arta, ta amsa da to..

Bayan ta gama mata da yamma ta shiga Tiktok ɗin ta ta goge sunan da aka san ta ta sanya *Zaijiddatu* ta canja email da komai nata wanda aka sani, karshe ma ta goge duk wani post da ta yi a Tiktok wanda aka san ta da sunanta *Princess Abir* ya dawo *ZaiJiddatu*, ta poster ƙunshi da kitson ta kuma yi rubutun cewa tana ƙunshi da kitso ga duk mai so ya mata DM sannan ta sauka. Haka ta koma Istagram ta canja suna kamar yadda ta sa a Tiktok ta canja komai, WhatsApp ɗin ta da aka san ta da number ta canja ta sa special number ta wadda iya mutum hudu ne yake da ita Suhal, Abdul, Mommy, Iman, number Abdul ta shiga ta yi blocking ɗin shi ta goge number shi. Number Mommy ta shiga inda ta ga last message ɗin da ta mata wanda a ranar ta rasu, hannu ta kai ta shafa rubutu tana goge hawaye cikin tsananin kewa ta ce "Allah ya jiƙan ki da rahama Mom, nasan da kina raye rayuwata ba za ta zama haka ba duk da nasan idan Allah ya dauro wa bawansa ƙaddara a rayuwa babu wanda zai yaye ma sai shi, amma duk da haka nasan da ace kina duniyar ko da magana mai daɗi ce za ki min dan naji sanyi a raina. " Kwanciya ta yi tana kuka marar sauti....

_NIGER_

Suhal na shirin fita fada Iman ta tsare shi da rigimar sai ya sanar da ita dalilin zaɓar ta ya bar yayarta. Zama ya yi yana ɗaura agogo cike da gajiyawa da wannan tambayar, yau dai ya ƙudurta a ransa zai sanar da ita dan ya huta da tambaya, turo baki ta yi ta matso kusa da shi ta ce "Ni Wallahi sai ka faɗa min dalilinka in ba haka ba na gudu."

Murmushi gefen baki ya yi ya kamo ta ya zaunar tare da zuba mata idanu, tsumkon shi ta yi a wuya ya runtse idanu yana jinjina ƙeta irin ta Iman, a nutse ya buɗe idanuwansa ya sauke su a kan ta ya kama hannayenta ya ce "Kin shirya jin dalilina? Sannan idan na faɗa miki ba za ki shiga ɗumuwa ba?"

Saurin gyaÉ—a masa kai ta yi tana gyara zama, kawar da kai ya yi yana tuna abubuwa da dama da suka shuÉ—e amma ya kasa manta su, idanuwansa ne suka ciko da kwalla amma ya yi saurin shanye su ya juyo da kansa gareta, ta tsorata da ganin yadda idanuwansa suka yi jajur, amma saboda ta matsu ta ji me zai ce mata ta marairaice ta ce "Ya Suhalll.."

Ta ja sunan hakan ya sa ya saki murmushin da bai shirya wa zuwan sa ba, nisawa ya yi ya ce "Iman a yanzu babu wanda ya fiki kusanci da ni, gado ɗaya muke kwana mu ci abinci a tare duk wani ɗabi'una kaɗan ne ba ki sani ba, wannan maganar ma tana daya daga cikin ɗabi'una da ba ki taɓa jin su ba. Ba na son hankalinki ya tashi da jin wannan maganar amma babu yadda na iya tun da kin takura sai kin ji zan sanar da ke yanzu. " Ya tsagaita yana kallon ta, ita kuma ta kafe shi da kallo, hannunta da ke cikin nasa ya murza a hankali yana lumshe idanu sannan ya ci gaba "Na sadaukar da soyayyata ne dan na ceci rayuwar Princes a sakamakon mugun ƙullin da aka ɗauri niyar yi mata dan a raba mu, an yi niyar cutar da ita dan tun farko kasheta aka ce ayi amma abin ya gagare su."

Kwalalo idanu waje Iman ta yi tana kallon shi, baki na rawa ta ce "M.. Me ta tsare musu a rayuwa ne?"

Girgiza kai ya yi ya ci gaba "Tsanar da aka yi wa mahaifiyarta ne ya shafe ta, ganin ta taso kowa na familynku na son ta, ki yi haƙuri da jin abin da zan faɗa Iman, ba kowa ba ne ya mata wannan cutarwar sai Umma."

A mugun zabure ta miƙe tsaye baki na rawa, kamo ta ya yi ya zaunar da ita jikinta sai rawa yake, gabaɗaya hankalinta ya bala'in tashi ƙarshe ma ta fashe da kuka ta soma magana cikin fitar haiyaci, "Wallahi da ana canja uwa ni dai da na canja tawa uwar, ashe tsanar da Umma ta yi Anty Baby har ta kai ta hana ta yin aure? Ya Allah ka kare min Anty Baby a duk inda take, Wallahi ni dai ban yi sa'ar uwa ba n...

Saurin rufe mata baki ya yi jin za ta yi saɓo, rungume ta ya yi yana bubbuga bayan ta cikin kwantar da hankali ya ce "Ki daina kuka kawai ki yi wa Umma addu'ar shiriya, labarin yadda Umma ta je gidan Malam ya sanar da ita shi kuma da yake bibiyar duk wani motsi nata hankalina ya tashi, ya ƙara da cewa "Ni kuma na ga Khairat ba ta cikin tsarin matan da nake so da aka zo ɗaurin aure na ce ke nake so duk dan na kubutar da Princess daga sharrin Umma."

Tsayar da kukan ta yi ta ce "Amma kai ya aka yi to asirin bai kama ka ba?"

Murmushi kawai ya mata bai ce komai ba ya mayar da ita jikinsa ya ci gaba da rarrashin ta, sai da ya ga ta saki ranta sannan ya ce kar ta kuskura ta nuna wa Umma ta san wani abu game da abin da take ƙullawa a gidan, to ta ce masa ta kuma ƙudurta a ransa duk daren Allah za ta tashi tsaye ta yi ta nafila tana nema wa ƴar'uwarta kariya daga sharrin mahaifiyarta....

Sai da ya ga ta yi bacci sannan ya wuce ya bar ɗakin, bayan ya gaishe da Mamma ya nufi ƙofar fita ya buɗe zai fita, wani abu baƙi ya gani kamar gawayi an barbaɗe ƙofar da shi sai wani irin wari yake, girgiza kai ya yi yana murmushi ya ce "Hmmm rai dai."

Wata Hadima ya gani za ta wuce ya kira ta, jiki na ɓari ta iso ta durƙusa tana gaishe shi ya amsa ba yabo ba fallasa, nuna mata wajan ya yi ya ce yanzu ta share ta goge tas ta amsa da to. Dawowa palo ya yi ta share komai ta goge sannan ta ɗan leƙo da kai ta sanar da shi ta gama, da hannu ya mata nuni da ya gode sannan ta wuce tana ta mamakin abin da ta share. Sai da ya karanta ayatul kursuyi da falaƙi da naasi sannan ya yi bismillah ya fito, gabaɗaya masarautar ta isheshi da duk abin da ke cikin ta, ba dan yana tuna Mamma da Ikilima ba da babu abin da zai dawo da shi Niger zai yi zamansa a Germany ya amshi tayin aikin da suka masa na likitanci, yana ta saƙa da warwara har ya isa fada....

Duk abin da aka yi a kan idanun Jakadiya ta yi kwafa ta wuce fuu..

_NIGERIA_

abubuwa sun kankama na siyasa su Alhaji Mustapha babu zama ba su da lokaci, duk inda suka ji wani gidan marayu sai sun je sun kai taimako tare da yan jarida su dauki video suna yaɗawa a kafafen sadarwa, suna nuna irin taimakon da Alhaji Mustapha yake yiwa mabuƙata, hakan kuwa ya ƙara kankaro masa mutumci da ƙima a idanun al'umma duk inda ka yi a Jahar Yola maganar shi ake, hakan na faranta ran Alhaji Mustapha da abokan nasa matuƙa. Kacokan suka dauki nauyin gidan talabijin na jaridar *zo ka sha kallo* wannan gidan radio ya yi hura a jahar Yola dan haka duk abin da aka yi suka watsa a media sai ya bazu gari, su kan su masu aiki a gidan redio suna ta yabon Alhaji Mustapha saboda yadda yake musu ɓarin kuɗi in ya zo aka tattauna da shi...

Yau ma sun tashi daga wani taro sai ga kiran Abdul ya shigo wayarsa, saurin É—auka ya yi ya koma can gefe inda ba hayaniya ya yi picking call É—in. A hanzarce ya ce "Hello Abdul ya aka yi ne.?"

Daga can ɓangaren Abdul ya ce "Dad lamari yana neman ya ɓaci fa."
Chapter 92 · 0% Book details