← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 120

Sashe 75

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dafe Goshi ta yi ta masa dubara amma sam ya ce mata ba zai yarda ta shiga ta bar shi a bakin ƙofa ba sai dai su shiga tare, ba yadda ta iya haka suka shiga banɗakin duk jikinta rawa yake, haka ta juyar da shi gefen da ake alwala ta nuna masa madubin wajan ta ce masa ai abokinsa ne ya masa magana, shi kuwa murmushi ya yi ya miƙa hannu yana shafa jikin madubin da haka ta yi saurin tsugunnawa ta yi tsarki ta miƙe tana mayar da numfashi. Rigar jikinsa ta cire masa ta goge masa zufa shi kuma yana tsaye ƙiƙam yana kallon ta sai inda ta juya shi, ganin dai duk jikinsa ya yi baƙi ta janyo hannunsa suka iso wajan wanka ta kalle shi ganin ya ƙi yin gaba ta ce. "Ka tsaya mana jikinka zan wanke ma." Ta faɗa tana ƙarasa janyo shi ya tsaya a saitin da ruwa ke zuba ta kunna. Zabura ta yi lokacin da ruwan ya zubo ta yi saurin riƙe hannunsa tana ce masa ya tsaya, haka ta dinga fama da shi da ta dauko sabulu za ta goga masa sai ya ce shi fa ba ya so, da kyar da siɗin goshi ya yarda ta masa wankan da wandonsa bakin gwiwa haka ta masa wanka da shi a jikinsa. Ita kanta ta yi jigib da ruwa kayanta sun jiƙe haka dai ta janyo wani towel da ta gani a toilet din ta goge masa jiki sannan ta yi alwala shi ma ta masa suka fito. Sai da ta zo za ta canja kaya ta tuna ba ta ma shigo da kayan ba ta nufi palo cikin sanɗa, akwatunan ta janyo za ta shige ɗaki ta ji muryar Inna ta daki dodon kunnunta ta juyo da sauri. Cike da mamaki Inna ta iso tana kallon ta ganin yadda ta jiƙe da ruwa ta ce. "Hauwa'u waɗannan kayan duk naki ne?"

Gyaɗa kai kawai Abir ta yi ta juya ta shige ɗakin cikin saurin, riƙe baki Inna ta yi tana cewa "Iko sai Allah! To bari dai mu gani malam ya dawo." Juyawa ta yi ta nufi kitchen tana ta mamakin yadda ta ga kitchen ɗin ba haka ta fita ta bar shi ba..

Abir na shiga ɗakin ta zarge akwati mai kayanta ta fito da wata doguwar riga da mayafinta shi ma Zaiyan ta ɗauki nasa kayan da ta dauko masa ta ce ya zo ta sa masa, bai musa mata ba ya iso gabanta ta dauki jallabiyarsa baƙa ta sa masa a haka ta fidda masa na jikin ta nuna masa yadda zai sa ta ba shi ya saka yana dariya, jallabiyar ta cire ta sa masa rigar sannan ita ma ta koma jikin wardrobe ta buɗe kamar mai ɗaukan kaya ta kare da murfin ta yi saurin canja kaya. Salla ta tayar shi ma ya yi kamar yadda ya ga tana yi, duk abin da ta yi sai ya yi har suka gama Sallar ta juyo ta kalle shi tana murmushi. Matsowa ya yi kusan ta ya ce. "Kai kai kai! Anty."

Dariya ce ta so subce mata ta danne jin ana kwankwasa musu kofa, tashi ta yi yana biye da ita a baya ta buɗe ƙofar ta ga Inna ce tsaye. Murmushi ta yi ta ce "Inna Baba ya dawo ne?"

"E ya dawo shi ma ya ce a kira ki." Ta faÉ—a tana juyawa ta fice ;ita kuma ta juya ta dauko mayafin rigar da wayarta suka yo palo.

Tun da suka fito Baba ke kallon su yana jinjina lamarin da ya faru, suna isowa ta zauna ƙasa Zaiyan ya kwanta kansa a bayanta yana riƙe da hannunta sai kallon su Baba yake, riƙe baki Baba ya yi ya ce "Zaiyan yau kuma mu ka nuna kamar ba ka san mu ba?"

Ƙara komawa bayan Abir ya yi bai ce komai ba hakan ya sa Baba ya yi murmushi, Inna ta nisa ta ce "Malam wai me ke faruwa ne? Na ga Hauwa'u ta dauko kayan har akwati uku, sannan palon nan an kwashe kujeru sai wannan dayar aka bari a gidan ko dan itama a lungu take shi ya sa ba ku gan ta ba?" Ta faɗa tana kallon Baba.

Gyara zama Baba ya yi ya faÉ—a mata yadda suka tarar da palon har zuwa lokacin da suka kwashe komai na palon suka fitar, ya dan muskuta ya kalli Abir yana girgiza kai ya ce "Maganar Hauwa'u kuwa da yammar nan aka É—aura auren ta da Zaiyan, shi ya sa kika ga ta zo da akwatuna."

A zabure Inna ta kalli Baba baki na rawa ta ce "Ba...Ban gane me kake nufi ba Malam? Wai Zaiyan da Hauwa'u ne aka ɗaura wa aure?" Ta faɗa tana dafe ƙirji.

Jinjina mata kai ya yi alamar tabbatarwa ta rafka tagumi tana kallon Abir da ta nuna ko a jikinta sai ma danna waya da take, tafa hannu Inna ta shiga yi ta ce "Hauwa'u anya kina haiyacinki kuwa? Zaiyan ɗin ne aka aura miki matsayin miji? Anya dangin nan naki suna ƙaunar ki kuwa Hauwa'u." Ta faɗa cike da ta'ajjibin wannan lamari na Abir.

Aje wayar ta yi da ɗago ta kalli Inna kafin ta yi magana idanuwanta suka cika da hawaye sai ga su sun zubo shar, da kyar ta saita kanta ta ce " Inna kenan, ki bar maganar dangina ba ta ni suke ba kowa ta kan shi yake da 'ya'yansa, ni kuma da ba ni da wanda zai kula da ni sai Allah wanda a kullum da shi na dogara shi ya sa ma na saɓi na bar musu gidan su daina ganina." Hawayen da suka sake zubo mata da goge Inna ta ruko hannunta ta ce "Ke fa daɗina da ke arhar ruwan ido kuka ba ya miki wahala."

Kamar jira take ta fashe da kuka tana rufe fuskarta da tafin hannu, sai da ta yi kuka sosai Inna na rarrashin ta sannan ta tsagaita ta shiga ba wa su Baba labarin abin da yake faruwa a gidansu da sauyawar da kowa na gidan ya mata, har labarin abubuwan da Abdul yake mata duk ta sanar da su tana yi tana sharce hawaye har da majina. Salati Inna da Baba suka ɗauka cike da tausayin ta, ba su taɓa tunanin Abdul zai yi wa Abir tsana har haka ba, Inna ta jinjina kai ta ce "Ki yi haƙuri Hauwa'u in sha Allah wata rana za ki yi farin ciki marar yankewa, amma hukuncin da kika yanke na wannan auren sam bai yi ba taya ma da hankalinki za ki auri mai allurar hauka? Gaskiya ɗabi'unki sun canja Hauwa'u ban san ki da taurin kai ba." Ta faɗa tana sauke numfashi..

Murmushi mai ciwo Abir ta yi ta ɗan motsa ta ji ya riƙe ta gam ga duk ya sakar mata nauyinsa, hannunsa ta taɓa tana kiran sunansa ta ji shuru sai da Baba ya leƙa ya ga ya yi bacci. Jin ana kiran Sallar Isha'i Baba ya ce su kai shi ɗaki kafin ya tafi masallaci, yunƙurin tashi ta yi a hankali sai gani suka yi shi ma ya miƙe tsaye yana ƙara riƙe Abir, ganin hakan sai ta ce Baba ya je ita za ta shigar da shi ɗakin ya amsa da to..

Inna ta nufi kitchen ta ɗaura abinci, ita kuma ta lallaɓa ta ja shi suka nufi ɗakinsu. A kan gado ta zauna shi ma ya zauna ya kwanta a kafaɗarta yana lumshe idanu, nuna masa ta yi ya kwanta amma sam yaƙi ya kwanta yana manne da ita ta dafe kai tana kallon shi, haka ta haƙura ta haye tsakiyar gadon shi ma ya hau ta kwanta tana kallon shi, ganin ta kwanta ya matso bayanta ya kwanta tare da zagaye cikinta da hannunsa yana sauke mata numfashi a kanta saboda ya fita tsayi sosai. Lumshe idanu ta yi tana jin gaban ta na faɗuwa, shi kuwa ya yi luf sai jan numfashi yake da ta motsa zai buɗe idanu hakan ya sa ta haƙura ta yi kamar tana bacci. Sai da karfe 9:30pm ta ga Inna ta shigo da kayan abinci ta aje ta fita ba ta ce musu komai ba, kunya ce ta mamaye Abir saboda yadda Inna ta gan su manne da ita da shi ta tashi zaune za ta sauko ta ji shi ma ya tashi zaunen. Haka ta janyo abincin ta dinga ba shi a baki yana ci yana mata surutu ita kuma tana bin shi da e ko a'a har ya koshi, bayan ya gama ya ce itama ta ɗaga bakinta zai ba ta, tana murmushi ta ɗaga baki ya dinga cusa mata kafin ta cinye wani ya sa mata wani, da kyar ta janye tana ce masa ta koshi shi kuwa sai ya ɓata fuska ya ce ta cinye duka dan ta zama ƙatuwa kamar abokinsa Suhal. Bayan sun gama suka nufi toilet ta wanke masa hannu itama ta wanke ta ɗauro alwala ta masa suka fito. Sallar Isha'i ta gabatar haɗi da shafa'i da wutiri duk abin da ta yi shi ma Zaiyan sai ya yi har ta shafa addu'a, tashi ta yi ta hau gadon shi ma ya yau ta yi musu addu'a suka kwanta. Kasa bacci ta yi sai juyi take gabaɗaya jin ta take a takure saboda ba ta saba kwana da kowa ba, waya ta dauka ta ga sakon Iman ya shigo ta share ta ci gaba da tunanin da ya zame mata jiki...

Karfe 11:00pm na dare Alhaji Mustapha ya kira Abdul ya zo ya same shi a gida ya ce ga shi nan zuwa..

Yana zuwa ya tarar da Alhaji Mustapha da Jarmai suna zaman jiransa, guri ya samu ya zauna tare da gaishe su suka amsa fuska sake suna ƴar ido. Zuwa can Abdul ya ce. "Dad gani ka ce na zo za mu yi wata magana mai muhimmanci, ina so mu yi mu gama na baro Hafsat a gida ta ce min kar na wuce awa ban dawo ba ni kuma ba na son na ɓata mata rai ta yi fushi." Ya faɗa yana ɗan ɗaure fuska..
Chapter 75 · 0% Book details