← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 120

Sashe 2

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita kuwa tuni sun yayyaga mata doguwar rigar dake jikinta, kaÉ—an ya rage su gama cire mata rigar ta ji muryarsa ai kuwa ta daddage ta kwarara ihu da É—an sauran kuzarin da ya rafe mata. Kafin ta rufe baki Dagus ya faÉ—o kanta, wani irin nauyi ta ji yayin da Dagus ya rikito bisa kanta ta dinga kiciniyar kwace kanta amma ina ta kasa, wata dabara ta zo mata ta juya da fuskarta ta samu daidai ta ci kuncinsa ta gatsa masa cizo, ihu yasa ba shiri ya kai mata mari ita kuma taki sakin kuncin nasa har sai da ta ji ya kawo jini sannan ta sake masa kunci..

Cikin magagin zafin cizon da ta masa ya tashi daga kan ta ya kai hannu zai damko ta ya ji saukar duka a gadon bayansa. Cikin kiɗima ya juyo dan ya ga waye ya dake shi a cikin abokan aikin nasu, sai dai kuma ya ga saɓanin hakan, dan kuwa Mahaukacin nan ya gani tsaye a bakin ƙofar yana wurga idanunsa ko'ina ya ga inda take.

Tana ganin shi ta miƙe da ƙyar ta nufi inda yake, hakan yasa Dagus ya kuma kai hannu da niyar dawo da ita ta yi saurin yin ƙasa da rarrafe ta dawo bayan Mahaukacin. Ganin jini a bakinta yasa ya zazzaro idanu ya kalli Dagus fuskarsa na nuna tsananin ɓacin rai ya ce "Ka daki Anty ko?" Yana gama faɗin haka ya nufe shi da rabin taɓaryar dake hannunsa.

Duk da Dagus a tsorace yake amma ya tsaya yana jiran Mahaukacin ya iso gareshi, shi kuma yana zuwa ya wurgo masa rabin taɓaryar dake hannunsa ji kake Tim! Ta same shi a ruwan ciki. Bai tsaya yin komai ba ya hau kansa ya dinga kai masa naushii ta ko'ina, abokan tafiyar Dagus su dama tuni ya sumar da su, dan haka Dagus ya rasa me ceton shi a hannun wannan Mahaukacin.

Sai da ya ga baya motsi sannan ya dakata da dukan shi, huci yake yana faÉ—in " Ka fito mata da jini sai na kashe ka."

Ita kuwa tana gefe tana kallon shi zuciyarta cike da mamakin wannan Mahaukaci da ya cece ta a hannun mugaye. Dawowa ya yi wajan ta yana kallon ta bai ce da ita komai ba, sai da ya sauke numfashi sannan ya koma kan Dagus ya ja ƙafarsa ya fitar da shi daga cikin kangon ya dawo ya fitar da sauran wanda a lokacin suka dawo daga sumar da suka yi, yana fito da su suka lallaɓa suka miƙe suna ƙoƙarin gudu. Yana tsaye yana kallon su har sun soma tafiya suna waiwayen shi, shi kuma ganin haka yasa ya koma ciki da sauri ya ɗauko makaminsa ya biyo su a guje..

Ganin mutuwa na tunkaro su yasa suka kwasa a guje sai ga su a bakin hanya, shi ma ya iso yana nuna su da taɓarya ai kuwa suka ƙara wa gudunsu mai tuni suka bar wajan. Kaiwa da komowa ya dinga yi a bakin hanyar kamar mai yin pareti, sai da ya jima a haka sannan ya juya ya koma..

Tana ganin shi ta miƙe tsaye tana kallon shi har ya iso ya zauna a kan wani kwali mai faɗi, wata leda ya buɗe sai ga masa da miya har ta soma tsami sai tashi take. Da sauri ta done hancinta ganin ya sa hannu ya ɗauko guda ɗaya yana murmushi ya kai bakinsa, kakarin amai ta dinga yi shi kuma ya kwashe da dariya ya janyo kwalin ya matso kusa da ita ya tura mata masar yana dariya..

"Anty za ki ci ko?" Ya faÉ—a yana É—aukar masar ya nufi bakinta da ita. Da sauri ta janye fuskarta ta ce "A a na koshi ka ci abinka."

Dariya ya kuma yi ya ci gaba da ci har ya cinye tas ya suɗe ledar, bayan ya gama ya janyo wata ledar ya bude ya ɗauko ruwa ya sha. Duk tana kallon shi har ya gama sannan ya ce mata "Anty yunwa nake ji." Ya faɗa yana ɓata fuska. Ita abin sai ya ba ta dariya ma dan haka ta yi murmushi abin da yake ba ta mamaki ma da yake ce mata Anty bayan kuma bai taɓa ganin ta ba sai yau, lokaci ɗaya taji zuciyarta ta yi rauni tausayin shi ya tsarga mata zuciya. "Yanzu kila iyayensa suna can suna neman shi, ko kuma sun gaji sun haƙura da nema, ko kuwa dai daga gidan mahaukata ya gudo yake zama a wannan waje mai mugun ƙazanta da wari?" Ta yi magana a sanyaye kafin ta sauke ajiyar zuciya ta dube shi ta ce " Ya sunan ka."

Dariya ya mata yana goge sandarsa da wani ɓakin tsumma, sai da ta kuma maimaitawa sannan ya dakata da abin yake ya ce " Ya sunanka?" Ya mayar mata da tambayar da ta masa. Waigawa gefe ta yi ta hango ɗankwalinta da isa wajan ta ɗauko, warware shi ta yi ta kalle shi ganin yadda jini ya ɓata masa jiki sai ta matsa a hankali cike da tsaro ta ce "Kawo na ɗaure ma wajan ciwon."

Maƙale kafaɗa ya yi yana turo baki sai kuma ya ce "Ni fa sarki ne a faɗar nan."

Sakato ya yi tana kallon shi, ta yi juyin duniyar nan amma fir ya ce shi sarki ne ba za a taɓa masa rawani ba, ita kuma tausayin shi ya cika mata zuciya sai kawai ta rabu da shi ta ce " Zan fita waje dan na koma gida." Ta yi magana tana bin hanyar fita..

Shi ma bayan ta ya bi suka fito a tare har bakin hanya, sai da ta juya ta ga ya biyo ta ta yi fuskar tausayi ta ce "To na gode ka koma."

Shi ma fuskar tausayin ya yi ya ce "To na gode ka koma."

Murmushi ta kuma yi a karo na biyu.

Duk wanda ya zo wucewa sai ya kalle su kallo irin na mamakin yadda ta tsaya a kusan mahaukaci ga shi kuma riƙe da makami amma bai ce mata komai ba, wasu kuma in sun ɗan yi gaba sai su ce mata 'Baiwar Allah wannan mahaukacin zai iya miki illa.' Murmushi kawai take musu ba ta cewa komai tana kuma mamakin yadda in mutane sun zo wucewa sai ya kare ta ya shiga gabanta yana muzurai.

Wani Dattijo ne ya zo wucewa ya yi shigar shi ta zuwa Masallaci ta yi saurin tarar shi sai ya tsaya. "Baiwar Allah lafiya?" Ya faÉ—a yana kallon ta.

"Baba ba lafiya ba don Allah ka taimaka min da waya zan kira Mamana su zo su dauke ni." Ta faÉ—a tana durkusawa, shi ma ganin ta durkusa ya durkusa a gefen ta ya ce "Baba ba lafiya ba don Allah ka taimaka min da waya zan kira Mamana su zo su dauke ni."

Dattijon nan ya dubi Mahaukacin ya ce "To amma mai ya haÉ—a ki da wannan Mahaukacin?"

Labari ta ba shi na ceton ta da ya yi ta kuma ce masa sace ta aka yi shi ne ta gudo har ya ceceta, jin haka yasa Dattijo ya cika da mamakin Mahaukacin ya dinga kallon shi ganin yadda ya durƙusa kamar yadda za yi, girgiza kai kawai ya yi fuskarsa na nuna tsananin damuwa ya fito da wayarsa Nokia ya ba ta. Amsa ta yi ta sa wata number ta danna kira, sai da ta kusa yankewa sannan aka ɗauka tare da yin sallama.

"Mommy!" Ta faÉ—a tare da sa kuka wani irin farin ciki na lullube ji na jin muryar mahaifiyarta da ta yi.

Daga cikin wayar matar ta dinga salati ta ce "Abir ke ce? Ina kuka shiga muke ta neman ku hankalinmu duk a tashe?"

Sai da ta goge hawaye ta ce "Mommy don Allah ki zo ki É—auke ni Wallahi in suka kama ni kashe ni za su yi."

"Su waye za su kashe ki?"

Ganin za su ja magana yasa Abir ta ce "Mommy ki bari sai na zo gida, ni dai ku yi sauri tsoro nake ji Mom."

"Ok Mamana yanzu a ina kike?" Mommy ta faÉ—a murya na rawa.

Tambayar Dattijon ta yi ya faɗa mata inda take, tana jin mai suke faɗa dan haka ta roƙi tsohon da ya tsaya a wajan ba ta da nisa sosai da wajan za ta iso. Ba dan ya so ba ya ce ya amince..

Kamar an tsikare shi ya buga sanda a ƙasa ya juya ya shiga kewaye su yana dariya, da ido kawai suke bin shi tsoro ya cika musu zuciyoyi kar ya ce zai kai musu duka. Yana gama zagaye su ya wuce ya bar wajan yana faɗin " Anty bari na kawo miki kaya."

Suna kallon shi ya tsallake bolar ya shige cikin kangon nan sai ga wata dalleliyar mota ɓaka ta yi packing a gaban su, a razane Abir ta ja da baya ta koma bayan Dattijon nan..

_Littafin nan na kuɗi ne ƴar uwa nomal ~N~ 300, vip ~N~ 500 ne. Ina kuma sanar da ku ga masu buƙatar Littafin ABBA NE complete ayi min magana ta WhatsApp number na 👉🏻🥏+966577675904_

*Kada ku bari a ba ku labarin wannan littafi*

_Maman Nusaiba ce🫶🏻_
[6/20, 7:15 PM] Ummu Amjad: ~_*A HAKA NAKE SON SHI*_~

Daga Alƙalamin

_*Sarat Alƙasum ~(Maman Nusaiba)~*_

_🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_

Littafin A HAKA NAKE SON SHI na kuÉ—i ne nomal ~N~ 300 vip ~N~ 500.

_🥏 WhatsApp Number +966577675904_

*بسم الله الرحمن الرحيم*

Shafi na biyu (2)

Da mamaki Dattijo ke kallon Abir ganin yadda nan-da-nan jikinta ya É—auki rawa, dawo da kallonsa ya yi kan motar yana jiran ya ga waye zai fito wanda kafin ya fito É—in ma yarinya ta tsorata?. Direba ya fito cikin sauri ya zagayo baya ya buÉ—e tare da rusunawa ya ce "Oga mun iso wajan."
Chapter 2 · 0% Book details