← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 120

Sashe 30

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hankalin Mamma ya tashi ganin hawayen ɗan nata, Ƙanwarsa Ikilima da ke kusa da Mamma ta ja tsaki tana cewa "Wallahi Yaya kar ka yarda a aura maka wannan guzumar matar, duk ai makircin Mama Bilkisu ne ta nace wai sai Papa ya ba ka umarni ka auri Ƙanwarta. Haka fa kwanaki ta shigo har nan ta yi wa Mamma rashin kunya ni kuma na ɗauke ta da mari, shi ne muka dinga faɗa har magana ta je wajan Papa, abin mamaki na ga an ɗaure mata hannu da kai wai na fitar mata sa jini na kuma karya mata hannu. Shi ne Mama Bilkisu ta dinga cewa wai dan ita ba gidan ba ce sai a kashe mata ƙanwa? Ta dinga kukan ƙarya Papa ya min faɗa a gaban su kuma ya ce daga yau ko harara na mata shi zai hukunta ni ya ķuma hana na masa bayanin abin da ya faru har aka yi faɗan." Ta ƙarashe maganar tana goge hawayen takaici kamar yanzu ne aka mata faɗan..

A zabure Yarima ya miƙe cikin wani kalar yanayi har jijiyoyin kansa sun tashi, dama ga shi mafaɗaci tuni zuciya shi ta dinga tafasa ya kalli Ikilima ya ce "Auta! Me ya sa ba ki sanar da ni a waya ba?"

Sake goge hawaye ta yi ta ce "To Yaya ta ina zan sanar da kai? Lokacin ɓakin ciki ya hanani yin magana ko École ban je ba washegari."

Kamo hannunsa Mamma ta yi ta zaunar, ganin yadda yake huci sai ta kwanto da shi kan cinyarta ta shiga shafa kansa a hankali, wani irin abu ne ya zo ya tsaye mata a saitin ma'adanar sirrinsa, yana son yin magana amma ya kasa. Sai sauke ajiyar zuciya yake, sai can Mamma ta ɗago da shi ta masa alama da ya kwantar da hankalinsa za ta yi wa Maimartaba magana. Rumgume ta ya yi ya ce "Merci beaucoup ma chérie."

Kallon Ikilima ta yi ta mata nuni da ta É—auko mata takarda, da sauri ta tashi ta shiga É—akin Mamma ta É—auko mata , amsa ta yi ta soma rubutu. Sai da tafi minti ashirin tana rubutun sannan ta gama ta lumke ta aje, Yarima ya yi murmushi ya tashi ya ce zai je ya É—an watsa ruwa..

Cikin ɗakinsa ya shiga wanda faɗar tsaruwar sa ma ɓata baki ne, kayan jikinsa ya cire ya ɗaura towel har ya nufi banɗaki sai ya fasa ya koma ya zauna a kan makeken gadonsa. Computer ya janyo ya buɗe tare da saka code ta buɗe tare da buɗe data ai kuwa sakonni suka dinga rige-rigen shigowa.

Murmushi ya yi ganin saƙon da yake son ya san dama sai ya tarar da shi, Instagram ya hau ya buɗe sakon wani account da aka sa *Princess A*, saƙonni ya gani sun fi goma ya bi ɗaya bayan ɗaya yana karantawa.

"Assalam alaikum Suhal ya kake ya kwana biyu?"

Murmushi ya yi ya ƙara yin ƙasa ya ga emoji ɗin kuka ya zaro idanu waje.

"Suhal shi ne kaki kulani ko? Ba komai ni ma daga yau na daina kula ka tun da ka manta da Ƙanwarka."

Dariya ya yi yana shafa kwantaccan sajansa ya ƙara duba ɗayan.

"Da gaske ne ka yada ni ko Suhal? Har sace ni aka yi na samu na tsira da raina amma duk ba ka sani ba, yanzu haka ma Abie na ya rasu yau an yi kwana huɗu ina fatan lafiya ce ta ɓoye ka ba wani abu marar daɗi ba."

Dafe kai ya yi cikin damuwa yana mai Allah wadai da halinsa na rashin kulata da ya yi, shi tun da ya aje Computer ma bai sake bi da kanta ba har ya je ya gama karatunsa a ƙasar Turkiyya ya dawo, lumshe idanu ɗinsa ya yi ya kuma buɗe ya janyo wayarsa.. Number ta ya ɗauka ya danna kira sai ya ji a kashe wayar take, fesar da numfashi mai zafi ya yi cikin tsananin son jin muryarta, sai ya ji wata irin kewar ta ta mamaye shi ya nisa tare da gyara zama ya soma rubuta mata saƙon ban haƙuri da uzirin da ya hana shi yi magana. Gaisuwa ya mata sannan ya ce mata number ta ba ta shiga in ta hau ta ba shi wadda zai same ta. Yana gama tura nlmata ya aje Computer ya shige banɗaki...

NIGERIA

Misalin ƙarfe 10:pm na dare tana zaune ta rafka tagumi hannu bibbiyu ta lula duniyar tunani hawaye na kwaranya kan kuncinta, ringing wayarta ne ya dawo da ita haiyacinta ta zabura ta sauke tagumin da ta yi ta ƙurawa wayar idanu, sabuwar number take gani na yawo kan screen ɗin wayarta ta shiga tunani waye yake kiran ta. Tana katsewa wani kiran na shigowa hakan yasa cikin jin tsoro ta ɗauki wayar hannu na rawa ta yin picking call ɗin, a hankali ta ce "Assalam alaikum."

Daga cikin wayar aka amsa mata, "Wa alaikum salam! Baby ya kike ya daren?"

Saƙare ta yi da wayar a kunne jin muryar mai magana, sai da ya sake magana sannan ta ce "Lafiya lau nake, Uncle Aruf ba ka rabuwa da canja number? Wallahi har naji tsoro naƙi ɗagawa da farko ashe ma kaine." Ta ƙarashe maganar tana sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi har sai da ya ji.

Dariya ya yi jin yadda ta sauke ajiyar zuciya ya ce "Wallahi Baby kin cika tsoro."

Turo baki gaba ta yi kamar tana gaban shi ta ce " to ai tsoro halak ne."

Dariya ya yi ya ce "Baby gobe za muje company Abie na motoci tare da ke."

Waro idanu ta yi cikin Shagwaɓarta ta ce "Ni dai gaskiya Uncle ku je kai da Yaya har da Salim, ka ga ni mace ce."

Murmushi ya yi mata kawai ya mata sallama ganin taƙi ba shi damar da zai yi hira da ita mai tsayi ya kashe kiran. Tana zaune sai ta lalibo glass ɗinta a saka ta buɗe computer wadda rabon da ta buɗe tun ranar kwana huɗun Abie da rasuwa, saƙo ta gani ta Instagram hakan yasa ta hau. Cike da mamaki take kallon wanda ya turo saƙon hannu na rawa ta shiga ta soma karantawa.

_"My princess am so sorry, Wallahi wata tafiya ce ta taso min na tafi ƙasar Turkiyya, na yi kewar ki sosai da sosai, kuma ban samu na sanar da ke ba tafiyar tawa ina mai ƙara ba ki haƙuri kin ji Ƙanwata. Ya kuma haƙurin rashin Abie? Sannu Allah ya jiƙan shi da rahama yasa kwanciya hutu ce a gare shi, sannan na kira number ki ba ta shiga ki turo min da number da zan same ki ina so na ji daddadar muryar ƙanwata. Miss you so much my princess."_

Wani kalar murmushi ta yi sai kuma ta ɓata fuska kamar tana gaban shi, ba ta ba shi amsa ba sai number kawai da ta tura masa. Kafin ta ɗauke hannu ta ga ya buɗe sai ta riƙe baki ta ce "Ɗan nema ni za ka raina wa hankali?."

Kiran ne ya shigo wayarta ta dauka ba ta ce komai ba, tana jiyo yadda yake sauke numfashi daga cikin wayar shi ma ya yi shuru, sai da ta gaji da riƙe wayar ta turo baki ta ce "Ni in mutum ba zai yi ba magana sai na kashe wayata."

Dariya ya yi yana jin wani matsanancin farin ciki ya mamaye masa zuciya,kuncin da ya shiga na kwanaki ya sauka jin yadda zazzakar muryarta mai haɗe da shagwaɓa ta ƙarashe majiyarsa, lumshe idanu ya yi dan har ga Allah yana son mace mai shagwaɓa da nuna yarinta da surutu irin na yara, a nutsu ya ce "My princess ɗin yayanta."

Ƙara kumbura baki ta yi ta gyara zama ta ce "Ni ai yanzu na goge ka daga layin yayuna ehhe." Ta faɗa tana murguda baki.

Waro fararen idanunsa ya yi fuska cike da annori ya ce "Haba dai Ƙanwata sorry mana, ba fa ƙin kula ki na yi ba, da gaske bana ƙasar na yi tafiya ne."

Ji ta yi ba za ta iya muso da shi ba ta ce "To ya gajiya ina Mamma da Ikilima?"

"Suna nan lafiya lau shekaranjiya ma Auta ke cewa wai ina kike na ce kina nan."

Harara ta aika wa wayar ta ce "Hmm wai har da cewa ina nan kamar ya kula da lamarina." Ta faɗa a shagwaɓe.

Lumshe idanunsa ya yi yana jin wani yanayi na fisgar shi mai daɗi, a sanyaya ya ce "Princess kin cika neman rigima sai Shagwaɓa, wai ke ba ki san yanzu kin soma girma ba." Ya faɗa yana jin wata iriyar kasala na mamaye shi, iya sautin muryarta in ya ji saka shi yake a wani yanayin shauki na musamman..

Riƙe baki ta yi ta ce "Kai Yaya Suhal a rage mugun hali, yanzu ni ina na wani girma saboda Allah? Am 19years fa, ita ma ban cika ba sai nan da wata biyar. Ai har yanzu ni yarinya ce."

Dariya ya yi yana mai jan bargo ya Lulluba sannan ya ce "E kuma fa kina da gaskiya my princess, har yanzu ba ki gama girma ba." Ya faÉ—a yana dariya.

"To sai da safe ma tun da ba ka kawo min tsaraba daga inda ka je ba, wai wata ƙasa ka je?" Ta faɗa tana kwanciya.

Da sauri ya ce "No my princess dakata please karki kashe, naje Turkiyya ne na ƙarasa karatuna. Kuma na samu sakamako mai kyau ko tayani murna." Ya ƙarashe maganar yana tashi zaune..

"Allah ni sai da safe bacci nake ji gobe akwai School, congratulations Allah ya taimaka."

Amin ya ce mata ba dan ya so ba suka yi sallama ta kashe kiran ta kwanta...

Washegari bayan ta dawo daga makaranta ta samu palonsu an yi ɓaki, rabawa ta yi ta zauna a kusa da Grandma ta ce "Uncle sannun ku da zuwa, ya gida? Ina Hafsy?" Ta faɗa tana murmushi..
Chapter 30 · 0% Book details