Sashe 47
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bai ba ni ba amsa illa ƙoƙarin riƙe ni da yake na ja da baya ya biyo ni, na fasa ihu amma bai daina bi na ba, ganin haka ya sa na dinga kiran sunan Bishira ta zo ta ceceni duk da ba ni da tabbacin ta dawo gidan.. Dariya na ga ya yi yana shafa gemun shi ya ce "Ki daina ɓata bakinki ma, ke da ganin Bishira har abada dan ta bar gidan nan kenan, dama dan ta bamu guri ne ta tafi. Sannan ki daina kira na da Daddy dan ni ba ubanta ba ne nan gidan babu iyayen Bishira."
Faɗin irin tashin hankalin da na shiga ɓata baki ne, tuni jikina ya ɗauki rawa na rasa yadda zan yi da rayuwata, ganin haka sai na ga ya miƙa hannu ya dauko waya a gefen gadon wanda nake kyautata zaton tashi ce ya zo da ita, daddanawa ya yi ya kara a kunne can kuma ya bani tare da cewa "Ga Bishira nan."
Saurin amsa na yi na fashe da kuka ita kuma ta fashe da dariya ta ce "Ke dalla malama ki yi wa mutane shuru, dama ba ki sani ba tarko ne na haɗa miki, tun da Alhaji ya gan ki ya takura sai na kawo ki Kano yana son ki da harka kin masa. Ya ba ni maƙudan kuɗaɗe har da na gyaran jikin da aka yi miki duk shi ya biya dan ya samu abin da yake so, dan haka sai an jima ni na gama aikina. "
Tana gama faɗin haka ta kashe kiran. Ƙara na fasa ina yin wulli da wayar na diro daga kan gadon na zo ina ƙoƙarin bude ƙofa na ga a kulle take, juyowa na yi na ga ya taso ya biyo bayana, nan muka dinga zagaye ɗakin ina kuka ina rokon shi kar ya taɓa ni amma sam yaƙi daina bina ni kuma ban fasa guje masa ba, na yi nadamar sanin Bishira a rayuwata, ashe dama kawalcina ta yi ban sani ba? Shi ya sa ta dage sai na zo ta yi iyayen ƙarya duk dan ta cika burin ta a kaina ? Wani irin marayan kuka na saki na durkushe a bakin ƙofa na haɗe hannayena biyu ina ta rokon shi ya rabu da ni, in kuɗi yake so zan sa Mijina ya tura masa ya bar ni tafi gida amma ya yi ta min dariya, a taƙaice a wannan dare wannan azzalumin ya keta min mutumcina ya ci zarafina ya wulaƙantani.."
Kuka ne ya ci ƙarfin ta ta dinga yi har da majina idanunwanta suka yi jajur, shi kan shi Suhal wani irin ɗaci yake ji na ketawa matarsa ta sunna mutumcj da aka yi, numfashi ya fesar yana janyo ta ya rungume ta bai ji kunyar kowa ba suma ba su damu ba dan kowa tausaya wa Sajida yake, Abir mai ruwan ido a kusa ta yi sharkaf sai sharce hawaye take tana tuna abin da ya faru da ita lokacin da take hannun masu garkuwa da mutane. Sai da Sajida ta tsagaita da kukan sannan ta ci gaba..
"Washegari aka kira likita ta duba ni har da dinki ta min ta sa min ruwa, na fi sati a kwance ban san inda kaina yake ba abin da kawai yake aiki a jikina idanu da zuciya, bayan su babu abin da nake iya motsawa da na yi yunƙurin tashi sai na ji azababben zafi ya mamaye min ko'ina na jikina dole na koma na kwanta, kwana na 20 cif kafin na samu lafiya Alhaji na ta zirya a kaina a lokacin ina jin ina ma na samu damar kashe shi a rage iri, ranar da aka sallame ni da dare ina bacci na ji an shaƙa min wani abu a hanci, daga nan ban kuma sanin inda kaina yake ba sai da rana ta fito na tashi na ga Alhaji a gefena yana bacci hannayensa a kan ƙirjina na kwalla ƙara ya zabura ya tashi. Kuka na dinga yi ina faɗin "Waiyo Mamana Bishira ta sayar da ni an mayar da ni karuwa, da na bi umarnin Suhal da hakan ba za ta faru da ni ba, amma sharri ƙawa ya ja min ga shi yau wai ni ce ake aikata zina da ni waiyo rayuwata, Allah ka ɗauki raina na huta da ganin wannan ɓakin gidan. "
Yana jina har na gama ya ja tsaki ya tashi ya zo saitina ya dauke ni ina kurma ihu ina yagon shi amma bai aje ni ba sai da ya kaini banɗaki ya min wanka ya fito da ni.. Haka kullum sai ya yi zina da ni ko da rana ya zo gidan sai ya zo ya kwanta da ni, dan kar na masa gardama da ya zo yake fesa wani turare a ɗakin daga nan ba na sanin ina kaina yake har sai ya gama biyan buƙatar shi ya tafi na tashi na yi ta kuka ina tsine wa Bishira. Na rame na ƙanjame bana cin abinci ko an kawo min, hakan ya sa Alhaji sai ya zo ya zazzare min idanu sai na ci. Shekara ta ɗaya a gidan kwatsam na samu ciki. "
Da sauri Suhal ya kalle ta ta girgiza masa kai alamar kar ya katse ta gama ba su labari ya kawar da kai gefen, ita kuma ta ci gaba.
"Rashin lafiya ta same ni inda aka sheda wa Alhaji ina da cikin wata uku a gun ya ce a zubar da shi, lokacin na dinga kuka dan ba ni da bakin magana tsoron Alhaji nake ji kamar rai da ajali, haka aka min allura aka ba ni magani ya tsare ni ya ce sai na sha jiki na rawa na shanye maganin. Ban daɗe da hakan ba cikina ya dinga murɗawa, karshe dai cikin ya zube suka kuma min allura ta bacci, sai da na yi kwana biyu na farfaɗo ya mayar da ni wani ɗaki. Haka na dinga rayuwa kamar wata karuwa a gidan, a cikin shekaru huɗu sai da na samu ciki sau huɗu yana sawa ana zubar min, a shekara ta biyar ne ya ce za mu tafo Yola tare, zuwa lokacin na sallama komai na rayuwata ga tsoron shi da nake ji, na yi yunƙurin guduwa amma da na fito sai na ga gabana ruwa ne kamar kogi dole na koma na zauna, haka muka biyo jirgi daga Kano muka zo Yola a nan ne ya kaini gidan shi ya ce wa matarsa ni ƴar aiki ce ya kawo mata, kuma ta riƙe ni da amana kamar ƴar da ta haifa ta amsa da to ta tarbeni da fara'a. Ni kuwa a lokacin naji ɗan sanyi ina ƙissima wata rana zan gudu a gidan.. Ashe ba haka abin ya ke ba, lulluɓin biri ne akuya da fatar kura. A wajan matarsa nuna wa yake kamar ƴar da ya haifa, amma da dare ya yi zai je ya far mini na yi kukana na gani, dan kar ma matarsa ta ji a ƙasa ya sa aka bani ɗaki su kuma suna sama in dare ya yi yake zuwar min ɗaki, ko na kulle na kwanta sai dai na ji shi a bayana. Haka na ɗauki wata 11 a gidan kullum burina wata rana na fita daga gidan nan kar na mutu a cikinsa, kwatsam yau da sati ɗaya na dinga rashin lafiya matarsa a lokacin ta tafi London ba kowa daga ni sai shi a gidan dan yaransa ban taɓa ganin su ba matarsa ta ce suna Ameria karatu suke. Ganin ba yadda nake ya kira aka duba ni nan suka ce masa ciki ne da ni na wata hudu hayin na biyar, kallo na ya dinga yi ya ce me ya sa ban faɗa masa ba tun cikin yana wata ɗaya? Ni kuma naki ce masa komai na koma na kwanta, washegari ya dauke ni ya kaini Asibiti ya ce a zubar a cikin. Nan Likitan yake sheda masa matsawar aka ce za a zubar da cikin jikina mafaita ba za ta sake daukan ciki ba, kuma ba lalle na rayu ba. Jin haka sai ya ce indai zan daina daukan ciki a zubar babu abin da zai faru, ni kuma a lokacin kamar kurma haka na zama a gaban su ina ji ina aka kaini wani ɗaki ya ce sai gobe da safe za a min aikin. Washegari da Ƙarfe 11:am na rana yau kenan aka min allura, ban ji ciwo ba har sai bayan bayan Sallar Azuhur ciwo ya hana ni zama na dinga murƙususu a ɗakin ni kadai. Da ciwon ya kwanta ne na lallaɓa na iso bakin ƙofa na murɗa naji ta bude sai kawai na rike ɗankwalina a hannu na fito ina sauri, har zan bar Asibitin sai na yanke shawarar na samu wani wajan na laɓe in suka gaji da nemana ya tafi sai na fito na gudu, shi ne na faɗo ɗakin da kuke har Allah ya sa na ga mijina." Ta sharce majina ta ɗago kai ta kalle su kamar yadda suma ita suke kallo ta ce "Wannan shi ne abin da ya faru bayan na baro Niger, yanzu ban sani ba iyayena suna da rai ko sun mutu ban sani ba."
Tashi Abir ta yi jikinta na rawa kamar mazari, ta soma takowa ta yo wajan Sajida sai ta yi baya luu ta zube a ƙasa....
Hmm. Yanzu ma aka fara 🙃
*Taku har kullum Maman Nusy.*
[10/27, 6:31 Yamma] Anty Sarat (Mom Nusy 🌹): ~A HAKA NAKE SON SHI~
Na: Maman Nusaiba
*BONUS FAGE💃ðŸ¼ðŸ’ƒðŸ¼*
Albishir ku masoya littafin *A HAKA NAKE SON SHI* ganin mutane na ta maganar kud'in da na sa wato N500 ya yi yawa, hakan ta sa zan yi promo yau din za ku iya biya N300 a maimakon N500. Daga yau ranar Juma'a zuwa wata Juma'ar mai zuwa, kwana 7 cif idan kika wuce sati daya ba ki biya ba to zai dawo kudin sa n da N500. Za ku iya tura kudin ku ta wannan account din👇ðŸ»
Account number 0003187186
Name account, Khadija Salisu
Name bank, Ja'iz bank
WhatsApp number +966577675904
Shafi na 24