Sashe 20
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abu kamar wasa yau tsayin kwana biyu ba labari akan sace Zaiyan, Abdul ya yi binciken har ya gaji amma babu wata alama da zai gano inda yake, hakan yasa yau ya shirya ya tafi Unguwar su Baba dan ya gana da shi. A mutumce ya tarbe shi suka gaisa sannan ya masa bayanin komai, ya kuma bukaci Baba da ya faÉ—a masa kalar motar da ta zo ta sace Zaiyan..
"Yaro motar nan ɓaka ce, ni kaina na sanar da 'yan sadan da ke kusa da mu amma da na koma washegari ba su saurareni ba ma." Nan dai Abdul ya dinga masa tambaya yana ba shi amsa daga ƙarshe ya masa sallama ya dawo gida..
Kuka da tunani a wannan karon shi ne abokin zaman Abir ta rame ta lalace ko abinci sai Abdul ya mata tsawa take ci, tunanin mahaifinta da Zaiyan kullum take yi ƙarshe rashin lafiya ta kwantar da ita har da karin ruwa leda uku aka mata saboda dama can ita mai yawan culuta ce bare yanzu da damuwa ta yi wa ƴar ƙaramar kwakwalwarta ƙawanya, sai ta rame ta kode da ƙyar take iya takawa...
"Hello! Alhaji wannan yaron fa ya sheƙa." Ɗaya daga cikin yaran Alhaji ya faɗa hankalinsa a tashi ya yi tsaye kan Zaiyan da yake cikin jini idanunsa sun kalli sama bakinsa a buɗe..
"What?" Alhaji ya faɗa a matuƙar razane yana miƙewa daga kan kujerar office ɗinsa, nan-da-nan zufa ta tsastsafo masa ya fito da sauri kamar sabon kamu har yana haɗawa da gudu, PA ɗinsa da ta ga yana buga sauri abin ya ba ta mamaki ta biyo shi tana faɗin "Sir! Lafiya dai?"
"Ba lafiya ba PA ki kula da komai zan je na dawo." Yana gama faÉ—in haka ya figi motar ya fita a guje......
_Muje zuwa dai _
_*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_
[10/25, 3:53 Yamma] My Addatyna: _*~A HAKA NAKE SON SHI~*_
_+966577675904_
*Arewabooks.com: Saratalkasum1897*
Shafi na (12)
Cikin minti 50 sai ga shi ya iso gidan wanda in a da ne sai ya yi awa da rabi yake zuwa in ya tafo daga cikin gari, a kiɗime duk yake hakan yasa ya danna hon da ƙarfi ɗiiii! A guje Maigadi ya fito daga banɗaki wandonsa a hannu ya nufi get ɗin ya leƙa ta ƙaramar kofa ya ga mai gidan ne sannan ya buɗe masa, jiki na rawa ya iso bakin motar ya buɗe yana faɗin "Barka da zuwa Alhaji."
A zafafe ya fito daga motar kafin Maigadi ya motsa ya zabga masa mari mai zafin gaske ya wuce fuu! Sake da baki Maigadi yake kallon hanyar da Alhaji ya bi yana jinjina rashin imani irin na Alhaji, so yake wataran ya bar gidan nan saboda zaluntar shi da Alhajin yake amma ko ya yi yunƙurin guduwa sai ya rasa hanya dole ya haƙura ya dawo gidan.
Yana shiga ciki ya dinga kiran yaran ɗaya bayan ɗaya suka fitowa jiki a sanyaye suna sadda kai ƙasa, a kufule ya kalle su ya ce "Me kuka ba shi ya ci?"
Ɗaya daga cikin su ya ɗago tare da cewa "Babu abin da muka ba shi Alhaji, kai ka ce kar a ba shi komai in ba wannan ruwan da ke cikin ƙwarya ba. Muna zuwa duba shi muka ga baya motsi ƙarshe muka gano mutuwa ya yi ga... Kafin ya ƙara Alhaji ya zabga masa mari yana huci yana nuna su da hannu, takaici ya hana shi yin magana ji yake kamar ya yi hauka saboda sun gama ɓata masa rabin shirin da ya dauki tsayin shekaru yana yi, a tsawa ce ya ce "A ina yake!?" Wanda aka mara bai kuma yin magana ba ya sha kunu yaƙi ba wa Alhaji amsa, sosai ranshi ya sosu ya fice daga palon yana bin wata ƙofa, hakan yasa Alhaji ya ƙara kufula ya ce "Wato yanzu na gano duk laifin Wancan ne da har ya yi zuciya ya tafi, Wallahi in kuka ruguza min wannan aikin gabaɗaya sai na kashe ku har 'yan danginku kun ja musu." Yana gama faɗin haka ya wuce su.
A kwance ya same shi ya yi saurin isa ganin yadda idanunsa suke kallon sama sai ya ƙara ruɗewa, ya ɗauko wata laya a cikin aljihunsa ya matse a hannunsa tare da lumshe idanu sannan ya ce "Nadumbuza ina son ganin ka yanzun nan." Yana buɗe idanunsa iska ta mamaye ɗakin mai ƙarfi, a hankali iskar ta wuce sai ga Nadumbuza ya bayyana yana karkada gashin dokin da ke hannunsa ya dubi Alhaji ya ce "Ka yi kuskure Alhaji da ka bari wannan yaron ya mutu."
A ruÉ—e ya ce "Haba Nadumbuza ina da kai ai ba zan sha wahalar samun abin da nake so ba, ka duba min shi kasan dai ai yau ne ranar É—aukan jinin da za a ba wa Uwa Dudu ko ka manta ne?"
"Hahaha! Ban manta ba Alhaji ka yi kuskuren wani abu ne a cikin aikin shi ya sa hakan ta faru, dole yanzu sai ka yi abu É—aya kafin yaron nan ya tashi." Da sauri Alhaji ya ce "FaÉ—a min Nadumbuza ko me kake so na yi zan yi komin wahalar shi in dai yaron nan zai tashi."
Wata dariyar ya kuma yi yana kewaye Zaiyan yana karkada masa gashin dake hannunsa, sai da ya dawo bayan Alhaji sannan ya ce "Alhaji Uwa Dudu ta ce dole sai ka kwanta da budurwa sabon jini wadda babu namijin da ya taɓa sanin ta a 'ya mace, da jinin da ya fito daga al'aurarta za a ɗauka a haɗa magani a tashi wannan yaro. Ka sani idan har ka rasa yaron nan to kana cikin matsala, in hakan ta faru sai ka maye gurbinsa da ɗan cikinka mai irin shekarunsa ko ƙasa da shi." Ya faɗa yana firfito da jajajan idanunsa ma su firgitarwa. Alhaji ya jinjina kai cike da gamsuwa da maganar Nadumbuza ya ce "Ba ma zan bari na rasa yaron nan ba, maganar budurwa kuma ai ina da safayar 'yan mata dayawa a cikin gidan nan zan sa a kawo ɗaya daga cikin su sai a aiwatar da komai." Ya faɗa yana murmishin jin daɗi.
Nadumbuza ya kwarara ihu yana ɗaga hannu sama ya juya ya daɓi kan Alhaji, sai da zagaye shi yana wasu irin kalamai sannan ya ce "Wannan aikin ba fa kai ɗaya za ka yi ba, ni ma sai na yi amfani da yarinyar ta yadda za mu samu isashen jinin da za ayi komai."
"An gama ko nawa kake so ka kwanta da su zan kawo ma ballantana É—aya tal."
Dariya Nadumbuza ya kuma yi sannan ya ce aje a kawo yarinyar, Alhaji ya fita daga ɗakin yana kiran yaran gidan. Suna zuwa ya ce "Mutum biyu su biyoni su ɗauko min yarinya ɗaya. " da to suka amsa sannan suka bi bayan shi har suka isa wata ƙofa a dandan ƙasa, sai ka rantse rijiya ce a wajan amma suna buɗewa sai ga hanya mai matakala ta yi cikin ƙasa, Alhaji ya fara shiga kana suka bi bayan shi suka shige ciki..
Ɗakuna ne guda uku da babban palo sai toile dake gefen ɗakunan, ɗaya daga ciki ɗakin ya buɗe ya shiga tare da kunna hasken fitilar ɗakin sai ga haske tau. 'Yan mata ne sun fi ashirin a cikin ɗakin kowacce ta takure a waje ɗaya, Daga jikinsu in ka gansu sai ka rantse babu abin da yake damun su kowacce ta yi frech abin ta, amma da ka kalli fuskokinsu za ka ga damuwa ƙarara ta bayyana.
Suna ganin Alhaji a tsaye kowacce ta yi saurin tashi suka zubo masa idanu, da kallo ya dinga bin su har ya hango wata farar yarinya wadda ba za ta wuce shekara 19 ba kayan jikinta duk ya yayyage, tana ɗago kai ta ga ita yake kallo ta zabura tana ɓoyewa a bayan wadda take kusa da ita ta fashe da kuka ta ce "Yaya don Allah kar ki bari ya ɗauke ni ya yanka, ki ɓoyeni Yaya." Ta ƙarashe maganar tana rufe bakinta da hannu..
Wani irin yawu Alhaji ya haɗiye shedan na ƙara ƙawata masa surar jikin yarinyar kasancewar ta fara sol yar duma-duma, duk da halin da suke ciki amma ita har wani sheƙi take sai in ka mata kallon nutsuwa za ka gano matsananciyar damuwa da tashin hankalin da take ciki.
Da hannu ya nuna musu ita suka isa wajan ta tana kuka tana kurma ihu suka ɓamɓareta daga jikin ƴar'uwar ta tana faɗin "Yaya ki taimakeni karki bari su tafi da ni Yayaaa! Ta ja sunan da ƙarfi ganin sun fita daga ɗakin. Kuka duk suke yi ba kamar wadda aka ɗauke Ƙanwarta kamar ta yi hauka sai cewa take "Don Allah ku dawo da ita ni na yarda ku kashe ni a madadin ta." Haka suka dinga kuka suna ji aka rufe ƙofar da aka shigo..
Suna tasa ƙeyarta da haka suka fito da ita waje suka buɗe mata ƙofa ta shiga sai ga ta a ɗakin da Zaiyan ke kwance, ganin Zaiyan baki buɗe idanu sun kalli sama yasa ta zaro idanu tana aiyanawa a ranta cewar yau fa ta yi bankwana da duniya. Dariya Nadumbuza ya yi yana lashe baki yana kallon ta ya ce "Yarinya matso nan ki ji." Ƙin zuwa ta yi sai da suka tura ta gaban shi ta runtse idanu jin wani kalar wani na ziyartar ta, Nadumbuza ya ce su ɗauke Zaiyan su fitar da shi daga ɗakin su kai shi ɗayan, shi kuma Alhaji ya tsaya su kuma kar su dawo, to suka ce sannan suka kama Zaiyan suka fitar da shi.
Nadumbuza ganin tana kuka ya É—auki wani ruwa mai kama da farau-farau ya É—an É—iba ya yayyafa mata a fuska, ajiyar zuciya ta sauke sannan ta kalle su ta ce "Kar ku cutar da shi ku mayar da ni wajan yayata."
Mamaki ne ya kama Nadumbuza jin maganin da ya yayyafa mata bai kama ta ba, ganin za ta ɓata musu lokaci ya sa ya ɗauko wani ɗan ƙyalle ya rufa mata a fuska nan-da-nan ta ji kanta yana juyawa ta durƙusa a wajan tana fitar da wani kalar numfashi na fitar haiyaci.