← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 120

Sashe 63

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daret ɗaki ta nufa Mom Yasira ta bi bayan ta ita da Mom Nabila. A tsaye suka same ta ta cire ɗankwali da hijab tana tsaye ƙiƙam kamar wadda aka dasa, ganin su ya sa ta kawar da duk wata damuwa ta ƙirƙiro murmushi tana kallon su. Rarrashin ta sosai suka dinga yi tana kuka mai tsuma zuciya har ta yi shuru, sai da suka tabbas ta daina kuka sannan Mom Nabila ta fita ta kawo mata tea ta sha ta miƙa mata maganin ciwon kai ta sha sannan ta zauna a bakin gado, sosai suka kula da ita suna ƙara yi mata nasiha ta kuma ce ta yi imani da ƙaddara kar su damu da ita ma za aje kai Iman...

Suna fita ta rafka tagumi tana tuna irin yadda Suhal ke nuna mata tsananin so da Ƙauna, yana ba ta lokaci a kullum dan su ƙara samun kusanci da juna ashe dai ba rabon sun rayu a matsayin miji da mata. Ajiyar zuciya ta sauke jin an dafa ta, juyo wa ta yi ta ga Abdul ne ba ta san ba lokacin da wani irin kuka ya zo mata ta faɗa jikinsa ta fashe da kukan...

Bubbuga bayan ta yake yana jin wani iri kukan ta na taɓa masa zuciya, da yana da iko da ya hana wannan auren abar mata masoyinta. Ɗago da ita ya yi yana share mata hawaye cikin wani kalar yanayi ya ma kasa magana, da sauri ta koma jikinsa cikin kuka ta ce "Yaya me na yi wa Suhal haka da zafi har ya zaɓi ya kasheni kwanana bai ƙare ba? Ko wani abin aka ce masa ina yi marar kyau da har zai bar ni ya koma kan wata?"

Kanta ya shafa yana jin ciwon abin da aka mata amma ya zai yi da ikon Allah? Dole ne ya sa ta ta haƙura da Suhal tun da Allah bai ƙaddara shi ne mijin da za ta aura ba. Sake ɗago da ita ya yi ya yi gyaran murya tare da ruko hanayenta ya ce "Baby ke fa musulma ce me ya sa kike irin wannan kalaman? Ki yi haƙuri nasan dole za ki ji zafin abin, amma ki yi wa Suhal uziri kar ki ƙullace shi ko da na ɗaya rana ne, kar ki tuhume shi da cin amanarki ki yafe masa abin da ya aikata a gareki, ki gode wa Allah ma Iman ya ce yana so jininki ƴar'uwarki wadda duk family kowa ya sheda kun fi kusanci da juna. Ina so ki manta da Suhal a matsayin masoyi ki goge wannan a babin rayuwarki ki ci gaba da harkokin ki kamar yadda kika saba, ban da abin ki meye na tayar da hankali? kin fa san da cewa matar mutum kabarinsa wani ba zai taɓa auran matar wani ba dole kowa tashi zai aura, ki ƙaddara cewa ke naki mijin ne bai zo ba yana nan tafe. Tashi ki zauna nasa Laraba za ta kawo miki abinci ki ci ki nuna kamar ba ki ji ciwon abin da ya faru ba ki saki ranki ko da kuwa a zuciyarki ba hakan ba ne, idan har ki na kuka za ki ba wa maƙiyan ki damar yi miki dariya tun da dama ba son auren ki suke ba da shi. "

Shuru ta yi tana sauraron shi har ya gama yi mata jawabi, a hankali ta kai hannu ta goge hawayen murya a shaƙe ta soma magana.

"In sha Allah Yaya zan daure na rasa Mom ma na dangana bare wani Suhal, zan yi duk abin da ka ce Yaya in sha Allah ko na fita ba zan yi kuka ba." Ta faɗa tana kirkiro murmushi yaƙe.

"Yawwa my Baby dama nasan ai ke Jaruma ce."

Murmushi ta kuma yi suka ji an buɗe ƙofar an shigo, Labara ta iso ta aje farantin tana hura hanci ta zauna tare da kallon su. Abdul ya yi murmushi ya ce "To ke kuma fa wa ya taɓo ki?"

Kwafa ta yi sannan ta ce "Su Maman Yasmin ne wai dan naje kiran wannan tsohuwar shi ne har Yasmin ta mareni ban mata komai ba." Ta faÉ—a tana goge hawayen da suka zubo mata..

Waro idanu suka yi a tare Abir ta ce "Me kika mata har ta sa hannu ta mare ki?"

Tsaki ta ja ta ce "Wai dan sun ganni suke cewa dama ai Suhal ba da ke ya dace ba da ɗaya daga cikin su ya dace, to shi ne fa ina isa ni kuma ban ce komai ba na ce ana kiran Hajiya shi kenan na yi lefi tsohuwar nan ta dinga zagar min iyaye tana cewa ko Mom da ta ja da su sun kai ta ƙasa bare ni ƴar aikin ta, ni ma in munafurci ya kawo ni rahoto zan dauka na kawo muku sai su min abin da zai sa ko sunan familyn gidan nan aka ambata sai na suma. Shi ne na ce ta daina zagina ni ai ba ƴar familynsu ba ce kawai fa daga haka Yasmin ta mare ni za ta sake min Iman ta fito daga ɗaki ta kareni ta ce na tafi ba su da mutumci. "

Jinjina kai Abdul ya yi ransa na ƙara ɓaci, ya zama dole ya saita wa Yasmin hanya a gidan nan, Abir itama ji ta yi wannan karon ba za ta yi haƙuri ba dole ta ɗauki mataki, idan har ita suna mata tana kyale su a matsayin su na 'yan'uwanta to ba fa za ta kyale suke cin zarafin ƴar aikin su ba kuma amanar da Mom ta bar musu. Tashi ta yi tsaye tana huci ta kalli Laraba ta ce "Laraba tashi muje yau sai na ga uban wa yake daure musu gindi suke wulaƙanta ki."

Sake da baki suke kallon ta jin abin da ta faɗa, shi kan shi Abdul ya yi mamakin kalamanta saboda bai taɓa gani tana zagi irin haka ba bare yin rigima. Ɗagowa ya yi da niyar mata magana ya ga wayam, da sauri ya miƙe ya nufi palo...

Suna zaune ana tattaunawa akan wanda za su raka amarya gidanta, tana isowa ta duba su da kyau ta hango Yasmin a gefen Hajiya tana mata kallon ya haƙuri, kwafa ta yi ta ƙaraso har inda suke ta tsaya a kan Yasmin cikin fusata ta ce "Uban wa ya ba ki umarnin ki mari Laraba? Ƙanwar Ammi ce ko ta Daddy? Kun haɗa jini da ita ne da kika mare ta?"

Gabaɗaya palon dauki wuta suka yi ganin yadda Abir ke masifa ba ji ba gani, Hajiya ta riƙe baki ta ce "Yo mu ai tun da aka hada mu da irin masifa ai mun shiga uku, yarinya kin haifu kin dauki gadon mai dattin ɗankwali duk wani baƙaƙen halayenta ga su nan kin soma fito da su za ki daura daga inda ta tsaya n...."

Ba ta ƙarasa ba Abir ta katse ta tare da cewa "Hajiya ya ishe ki haka!" Ta faɗa a fusace sannan ta daura "Shin wai me Mom ta tsare muku ne da kuka tsane ta har haka? Lefin ta ne ɗan ta zama matar Abie? Ko wani yana auran matar wani ne? To Wallahi daga yau na daina jin karar kowa a familyn nan ko min tsufan mutum ya ƙara zagar min uwa ko ya ci mutumcin ta a gabana kotu ce za ta rabani da shi, haba wannan wacce irin rayuwa ce wai?" Ta faɗa tana yin numfashi fat! Fat! Kamar wacce tsananin zazzabi ya rufe ta...

Tsoro ne ya kama Hajiya ganin yau wai Abir ce take faÉ—a mata magana son ranta, Mom Yasira kuwa murmushi ta yi ita kan ta abin na damun ta akan tsanar da su Hajiya suka yi wa Mom, Abdul kuwa sumar tsaye ya yi a bakin kofar É—akinta, mamaki ya hana shi takowa bare ya zo ya janye ta daga gaban su. Ita kan ta Ammi ta girgiza da jin kalaman Abir tana tunanin yaushe ta zama marar kunya?

Yasmin ta miƙe ta daga hannu za ta mare ta ta yi saurin damƙe hannun, cikin tsananin ɓacin rai Abir ta ce "Kar ki kuskura ki aika babban kuskuren da zai sa har ki mutu kina da na sanin shi marar amfani."

A kufule Yasmin ta ce "In an mare ki wani abin za ki.. Kafin ta ƙarasa ta ji saukar mata tass! Tass!..

A kiɗime ta ɗago ta ga Abir na nuna ta da tsaya ta ce "Ki riƙe girman kafin na sa ƙafa na take na murje shi a ƙasa." Tana gama fadin haka ta sake mata hannu ta dawo gefen Mom Yasira ta kwanta akan cinyarta, sosai zuciyarta ke tafasa ta lumshe idanu tana jin ruwan ashar ɗin da Yasmin ke mata ana rike ta sai ta zo ta dake ce..

Mom Yasira ta ɗago ta ta miƙar da ita suka wuce dakin Grandma.

Hajiya ta kalli Gradma ta ce "Lalle Hauwa'u, ki na gani wannan yarinyar ta mari Yasmin amma kika yi shuru?"

Kawar da kai Gradma ta yi ta ce "To me kike so na ce? Kun ga ku tashi ku tafi ku shirya amarya dangin Ango suna son a wuce bana son damuwa ni." Ta faɗa tana kaɗa ƙafa. Kwafa Hajiya ta yi ta tashi ta kama hannun Yasmin da take jin takaicin marin da Abir ta mata duk suka wuce...

Bayan an gama shirya amarya aka fito da ita harabar gidan za a saka ta a mota amma fir ta ce ba za ta shiga ba sai ta ga Abir, dole Mom Nabila ta kama hannunta suka zo ɗakin Gradma suka gan ta a zaune tana shan tea, ganin Iman ya sa ta miƙe tana murmushi ta ce "To ƴar'uwata Allah ya ba da zaman lafiya sai mun yi waya."
Chapter 63 · 0% Book details