Sashe 33
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani irin murmishi Alhaji ya yi yana kissima abubuwa kala-kala a zuciyarsa, É—ago da ita ya yi ya rungume ta yana shafa bayanta cikin iya bariki ya ce "In dai na ji yadda nake so za ki zama ajiyata ba zan kashe ki ba."
Jin abin da ya ce ta goge hawaye ta ce "Na gode." Tana kuka marar sauti jikinta na rawa jin yadda Alhaji yake yawo da hannunsa a cikin ƙirjinta..
Dariya Jarmai ya yi ya miƙe shi ma ya zabi ɗaya shi ma Alhaji Mustapha ya ɗauki ɗaya suka shige wani ɗaki..
Alhaji ya kamo hannun yarinyar ya bi wani lungu da ita sai ga su a cikin ɗaki ƙarami, ɗakin gado ɗaya ne a ciki mai mugun kyau har da drower a ciki, kwantar da ita ya yi ya shiga cire mata kayan jikinta yana wani lashe baki. Kuka take marar sauti ganin yau ita ce za a keta wa mutumci wanda tun da ta yi wayo take tattalin shi kar ya zube, sai ga shi yau Alhaji zai raba ta da shi. Wani kalar ƙara ta saki na wahala jin gabaɗaya ya danne ta yana mata kiss a duk inda ya ci ķaro na jikinta, shi kuwa Alhaji har wani lumshe yake yana faɗin "Yarinya za aje da ke."
Ihu ta dinga yi na azaba tana jin tamkar ba a duniya take ba, wani ƙara da ta kwalla har sai da jijiyar kanta ta fito daga nan ba ta sake motsa ko fa yatsar hannunta ba..
Farkawa ta yi kawai ta ganta an mata wanka an lullube ta da bargo, idanunta da suka yi luhu-luhu ta rufe ta sake bude su hawaye na zirya, rubutu ta gani a cikin ta ta soma dubawa cike da tsoro. Kasa karantawa ta yi dan ba ta gane me aka rubuta ba sai ta fashe da kuka tana faÉ—in "Waiyo Allah ka ceceni daga cikin wannan mugun gidan, Waiyo Mamana ko a wani hali kike ciki?"
Miƙewa ta yi a hankali tana tsoron taka ƙafarta ta lallaɓa ta miƙe tsaye tana jin wani irin zafi ya mamaye mata ko'ina na jikinta, jikinta ta duba ta ga babu kaya ta hangi madubi a jikin drower ta lallaɓa tana ɗigishi ta isa ta tsaya ta soma karanta rubutun da take da tabbacin Alhaji ne ya mata shi.
_"Sweet girl gaskiya kin haÉ—u, ki zauna a wannan É—akin zan sa ake miki duk abin da kike so, da zarar na zo gidan nan to ke ce abincin da zan fara karyawa."_
Ƙara ta kwalla tana nanata kalmar abinci, sai da ta gaji da tsayuwa sannan ta ga wata ƙofa ta nufi wajan, tana zuwa sai ta ga ƙofar ta buɗe sai ganin ta ta yi a cikin toilet mai mugun kyau kwamin wankan ta ma abin kallo ne,dogon numfashi ta ja ta kunna ruwa mai zafi ta cika kwamin ta shiga ta zauna. Ji take ina ma ace mutuwar ta ta gani da wannan ɓakar ranar da ta riska..
Kwanan ta shida tana fama da zazzabi kafin ta samu sauƙi, duk da a kwance take amma kullum duk dare sai ta kira Baba a waya tana tambayar shi ina Zaiyan ya jikin nashi? Shi kuma Baba zai ce mata lafiya lau yake, kuma yana samun sauƙi game da larurar tashi, hakan na faranta mata rai in ta ji ya faɗa mata haka..
Yau ma kamar kullum misalin karfe 9:00pm na dare, zaune take a gaban mirror tana tsane kanta da ɗan ƙaramin towel tana kallon kanta ta cikin madubi, masharci ta janyo ta jona ta kunna ta shiga taje kan cikin nutsuwa. Bayan ta gama ta ɗauko wani cream fari mai sanyin daɗin ƙamshin amma ƙamshin ba sosai ba ta shafe ko'ina na jikinta da shi, a nutse ta tashi tana jin cikinta na mata kukan yunwa ta shafa cikin da yake a lafa kamar babu yan hanji a cikin. Lumshe idanu ta yi tana jin kamar ta ci abinci babu, saurin buɗe idanunta ta yi ta isa ta buɗe drower ta , kayan baccin ta masu mugun kyau ne jere kala-kala ta miƙa hannu ta janyo wasu riga da wando masu sulɓi haɗi da hula kalar kayan, kayan ta ɗaga ta ga ba su mata ba ta mayar ta shiga dubawa saboda ruwan ido irin nata.. Sai da ta gaji da tsayuwa har idanunta sun cika taf da hawaye tana kumbura baki kamar wani ya mata laifi ta janyo wasu pink ta jefa su kan gado. Sai da ta zauna tana kallon kayan dan ita sam duk cikin kayan ta ji ba wanda ya mata ta saka a jikinta, haka dai ta haƙura ta cire towel ɗin jikinta ta saka kayan ta zauna a bakin gado, so take ta fita ta ci abinci amma saboda lalaci irin nata ta narke a gado tana lumshe idanu ƙarshe ma gadon ta kwanta..
Sai da ta ji yunwa na neman mata illa ta janyo wayarta ta nemo number Mommy ta kira ta, har ta katse ba ta ɗauka ba ta kuma kira a karo na biyu tukun ta ɗauka. A shagwaɓe ta ce "Mom ki ce Laraba ta kawo min abinci yunwa nake ji."
Mommy dake shirin shiga ɗaki ta dakata da shiga ɗakin, kwafa Mommy ta yi ta ce "Allah ya shirya ki kawai zan ce, yanzu rabon da ki ci abinci tun da safe kin shige daki kin rufe kamar wata baƙuwar boka." Ta faɗa tana dawowa palo ta kira Laraba.
Tana isowa ta ce "Laraba sauran abincin nan da na ce ki É—auke shi É—azu, to ki fiddo ki dumama wa Mamana wai yunwa take ji."
Sosa kai Laraba ta yi tana mutsitsike idanu saboda baccin da ya mamaye ta, sai da ta ƙara sosa kai sannan ta ce "To Mommy bari na dumama mata." Ta faɗa tana wucewa.
Jin abin da Mommy ta faÉ—a Abir ta gyara kwanciya ta ce "Mom ta yi min shayi ta haÉ—o da madara mai sanyi a cikin freeze da na ce ta saka a ciki."
"Hmmm ba za ki canja ba Mamana, ga shi zan sa ta kawo miki sai da safe." Ta faÉ—a tana kashe kiran.
Tana nan kwance Laraba ta shigo ɗakin ɗauke da trey, a bakin gadon ta aje mata ta shaƙi iska ta ce "Alkur'anin Allah Anty Baby ɗakinki akwai daɗin zama." Ta lumshe idanu tana washe baki.
Murmushi Abir ta yi ta sauko daga kan gadon ta zauna a kan capet ɗin dake malale a ƙasan ɗakin, buɗe abincin ta yi ta ga shinkafa ce dafa-duka, ɗagowa ta yi tana ɓata fuska ta kalli Laraba da itama ita ɗin take kallo ta ce "Laraba babu wani abincin sai wannan?" Ta faɗa tana nuna mata abincin da hannu.
ÆŠaga kai ta yi sama kamar mai tunani sai kuma ta kalli Abir ta ce "Anty Baby ai wannan mugun yayan naki ne ya cinye macaroni mai hegen daÉ—i da na yi É—azu."
Murmushi kawai ta yi dan ta san Labara da Abdul take, madarar ta zuba a cup sai da ta cika shi taf ta yi sanyi ƙarai, wani irin yawu ta haɗiya ta kai baki ta dinga sha tana lumshe idanu tana buɗe shi a hankali daɗi da gardin madarar na zagaya mata kwanya. Bayan ta gama sha ta ce ta ƙoshi da shayin ta mayar har abincin, riƙe baki Laraba ta yi ta ce "Kai Anty Baby to iya madara fa kika sha."
Runtse idanu ta yi dan ba ta son Laraba ta addabe ta da surutu, a hankali ta ce "E na ƙoshi ɗauke sai da safe."
To ta ce ta É—auke kayan tana jin kamar kar ta fita daga É—akin jin yadda wani irin sanyi ke ratsa ta duk da itama a nata É—akin akwai AC ..
Washegari ta shirya cikin black É—in Abaya É—aya daga cikin wadda Uncle Aruf ya kawo mata, jaka da takalmi ta É—auko ta saka ta yi rolin da mayafin abayar tare da É—aukan wayarta ta fito.. A zaune ta samu Abdul yana daddana waya ta tako cikin nutsuwarta tana murmushi ta iso gaban shi ta tsaya..
Tun daga kan kyakyawar ƙafarta ya soma kallon ta har zuwa kan fuskarta wadda take ƙyallin, duk da ita ba ma'abociyar kwalliya ba ce amma kwallin da ta saka ta yi ɗigo a tsakanin ƙirar ta ya ƙara mata wani irin kyau na musamman, hannu ya miƙa mata ta kama ya zaunar da ita a gefen shi har yanzu bai daina kallon ta ba, ji yake kamar ya cinye ta saboda tsananin ƙaunar da yake mata. In kuwa ya ga tana yi wa wani murmushi ji yake kamar ana hura masa wuta a cikin zuciyarsa. Hura masa iska ta yi ya yi saurin ɗauke idanunsa ta turo baki ta ce "Yaya wai canja halitta na yi ne da kake kallo na kamar ba ka sanni ba?"
Murmushi ya yi ya ce " Baby Wallahi kin yi kyau sosai, sai ina haka ba sanarwa?" Ya faɗa yana kafe ta da dara-daran Idanuwansa masu ƙara masa ƙwarjini..
"Yaya zan je wajan su Baba ne." Ta faÉ—a tana cuno baki dan kar ma ya ce mata ba yau ba..
Kamar ya karanci me take tunani ya kamo hannayenta ya ce "Baby ba zan hana ki zuwa ba, amma bari na kira Ali ya kaiki."
Murmushi ta yi cikin farinciki ta ce "Thank you."
Bai kuma ce mata komai ba ya É—auki waya ya kira Ali tare da sanar da shi ya zo ya kai ta ya amsa da to sannan ya kashe kiran..
Ba su fi minti biyar ba sai ga kiran shi ya shigo wayar Abdul ya sheda masa yana harabar gidan, kallon ta ya yi ya ga yadda take cikin farin ciki sai ya ji wani sanyi na ratsa shi ya ce "Baby ya zo."
Miƙewa ta yi ta ce ya sanar da Mommy ta fita duk da ta faɗa mata da safe, shi kuwa ko uffan bai ce mata ba ya bi ta da kallo, yau kawai ji ya yi baya son ta je wajan su Baba, amma ba yadda ya iya idan ya ce zai hana ta zuwa to fa yau duk gidan nan sai kowa yasan halin da ake ciki...