Sashe 66
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Marmartaba na shigowa ya yi musu nasiha sosai ya ja hankalin su game da zamantakewar aure, sosai duk jikin su ya yi sanyi ita da Suhal sai zubar da hawaye take har ya gama musu nasiha. Bayan Maimartaba ya yi tasa su Kilishi suma suka dinga yi wa amarya da ango nasiha, mamaki fal ran Suhal amma ya yi ta murmushi jin wai Kilishi ce take cewa ya ji tsoron Allah ya riƙe amana kar ya zalunci ƴar mutane, sai da suka gama Maimartaba ya ce ya sallame su kowa ya tashi Mamma ta yi wa Mom Yasira alama da su biyo ta suka bi bayan ta. Sai da suka fito za su shiga sashen Mamma Iman ta ga an tsaya a gaban ta, tsayawa suka yi ganin hamshaƙiyar matashiyar budurwa tsaye a gaban su tana yi musu murmushi. Dam! Iman ta ji gaban ta ya faɗi ganin kallon da take mata amma ta dake ta ƙara jan alƙabba ta rufe fuskarta.
"Amarya ayi min afuwa ban zo da wuri ba ga shi har za ku shiga sashen Mamma, ina fatan za a riƙe min Yayana da amana." Ta faɗa tana sakin murmushin da ita kaɗai ta bar wa kanta sani. Jinjina kai kawai Iman ta yi Jakadiya ta ɗan rusuna ta ce. "Ranki ya daɗe muna so za mu kai Gimbiya ta samu ta huta ga Angonta can yana kallon mu kar mu yi lefi." Ta faɗa cikin jin tsoron Fauziya dan kar ta mata tijara a gaban su Mom Yasira..
GyaÉ—a kai ta yi zuciyarta na tafasa ganin wannan wannan Æ´ar kwailar ce matar Suhal, kwafa ta yi ta yadda ba za su gane ba ta ba su izinin wucewa suka yi gaba..
Daret gaban wajan Suhal ta nufa da yake gefe shi da wata hadimarsa wacce ba za ta wuce shekarun Abir ba suna magana, tana isowa ta yi gyaran murya ya yi banza da ita ya dubi hadimar ya ce "Ina Fatan kin gane bayanin duk da na miki ko?"
Rusunawa ta yi cikin girmamawa ta ce "Na fahimta ranka ya daÉ—e kuma ango."
Murmushin gefen baki ya yi abin da duk hadiman gidan ba sa samu sai ita kaɗai yake iya sakin wa fuska ya mata magana, wannan abu na ƙonawa sauran hadiman gidan rai ganin yadda komai nasa in ya tashi ita zai kira.
Ganin zai zubar mata da girma a gaban ƙaramar yarinya ta dan nisa ta ce "Yaya Suhal Ango wajan ka fa na zo."
Wani irin kallo ya mata wanda ya sa ta sha jinin jikinta, sallamar hadimar ya yi ta tafi ya dubi Fauziya murmushi ya mata wanda ya sa ta shagalta da kallon shi, tsaki ya ja sannan ya ce "Ba ni da lokaci sai na matata, idan kina da wata magana sai ki bari nan da wata uku sai ki yi maganar." Ya faÉ—a yana yin part É—in Mamma..
Wani irin turiri zuciyar Fauziya ke yi ganin yadda ya gasa mata magana, kwafa ta yi ta nufi part É—in Sarauniya Bilkisu tana jin kamar ta fasa ihu ko ta ji sassaucin kishin da ke cin mata zuciya...
_Maman Nusaiba ce_
[11/9, 11:01 Yamma] Anty Sarat (Mom Nusy 🌹): ~A HAKA NAKE SON SHI~
+966577675904
Shafi na (32)
Suna shiga part ɗin Mamma aka shigar da su masaukin su in da shi ma ne part babba wanda ya kasance na Iman ne, sosai suka yaba da tsarin palon komai na musamman ne a ciki Ammi sai gyaɗa kai take tana jin haushin da ba Fatima ko Yasmin ba ce ta samu wannan daular, ɗakin da ke kallon kitchen ta nufa ta murɗa ta shiga ciki. Waro idanu ta yi ganin wani makeken gado an masa shinfiɗa ta alfarma sai ƙamshi ɗakin yake, da kyar ta isa bakin gadon tana riƙe baki cike da jinjina lamarin gidan sarauta. Ko'ina na ɗakin sai da ta duba har wardrobe ta buɗe ta ga kayan Yarima Suhal ne kala-kala iri daban-daban ga su nan a goge wasu an rataye su ko buɗa su ma ba a yi ba, gyaɗa kai kawai Ammi take ta sake buɗe ɗayan gefen inda kuma ta ga set ɗin kayan mace ne wanda take kyautata zaton na Iman ne cike da wajan a jere tsaf sai ƙamshi suke, wata riga da wando ta gani 'yan kanti masu azabar kyau duk cikin kayan sun fi jan hankalinta, a hankali ta ta janyo ta buɗe tana riƙe baki mamaki ya ƙara kama ta ganin kuɗin kayan ya fi dubu 50k a naira. Cukuikuyawa ta yi ta cusa dan ta kasa linke su kamar yadda ta gani, dafe ƙirji ta yi tana zama a kan gadon ta ji wani irin laushi ta kasa jurewa sai da ta ce "Tabɗijam! Lalle yarinya kin samu tsuntsu daga sama gasasshe, yanzu wannan daular duk ke kaɗai za ki zauna a cikin ta? Lalle Abban Salim mugun munafiki ne da yaƙi aura wa Yarima Yasmin ya aura masa wannan shashashar da halin su ɗaya da Abir." Tashi ta yi tana ta nazari sai zagaya ɗakin take carpet ɗin da ke mamale a ƙasan ɗakin kan shi abin kallo ne, wani kalar laushi gareshi ko a iya kan shi za ka iya kwanciya ka yi bacci. Jin ana faɗin ina take ta yi saurin ɗaukan mayafinta da ta aje a bakin gadon ta yo palo. Da kallo Mom Yasira ta bi ta tana jinjina tsaurin ido irin na Ammi ganin daga inda ta fito, ganin kallon da Mom Yasira take mata sai ta waske tana wani kawar da kai ta saki murmushi tare da cewa "Ɗakin amarya na gani ba ko'ina na je ba."
Yasmin da ke tsaye tana kallon palon ta kalli Ammi ta ce "Ammi yana da kyau ko? Amma kuma ya aka yi ba ku mata jere ba na ga komai na ciki sabo ne?" Kwafa Ammi ta yi tana wayancewa ta ce "To ai dama tun da aka sa auren Abir da Yarima ya ce ba ya son su Abbanku su kawo ta komai ita kaÉ—ai yake so, a matsayin ta na marainiya kuma wadda yake da burin zama da ita zai mata komai dan faranta mata rai, ashe ma ba ita ba ce matar tasa." Ta faÉ—a tana yin murmushi dan ta ga me su Mom Yasira za su ce. Banza suka mata sai matar Daddyn Aruf ce ta rausayar da kai ta ce " Allah sarki mai sunan Inna ko a wani hali take yanzu? "
Sallama suka ji an yi suka amsa tare da kallon kofar, Ikilima ce ta shigo cikin shigar ta ta alfarma da ka gan ta sak Suhal sai dai shi ya fi ta fari. Fuska ba yabo ba fallasa ta iso tare da dan rusunawa ta ce "Sannun ku da zuwa baƙi, ina wadda ta yi wa Anty Princess kwacen Yayana?" Ta faɗa tana murmushi.
Dam! Ƙirjin Iman ya buga ta runtse idanu tana karanto addu'ar samun nutsuwa, abin da take gudu kenan ta san dama ba lalle dangin Suhal su ƙaunace ta ba kamar yadda suke son Abir, saboda ita Abir in dai ka yi mu'amala da ita to tabbas dole ne ka ji ta shiga ranka saboda sanyin halin ta ga tausayi da girmama mutane. Tun da ta ga yadda su Kilishi ke mata kallon daga ina ta tsure ta shiga damuwa, ko ba a faɗa mata ba tasan ba za su taɓa zama lafiya da kishiyoyin surukar ta ba. Dogon numfashi ta ja tana ɗan ɗago kai ta kalli Ikilima ba ta ce komai ba.
Murmushi Ikilima ta sakar mata tare da isa inda take ta kama hannunta, buÉ—e mayafin nata ta yi tare da cewa "Ki tashi muje Yaya ne yake son ganin ki, ya ce da kaina zan kaiki inda yake."
Zazzaro idanu ta yi tana jin kamar ta kurma ihu ta tashi aljannun ƙarya dan kar ta je, amma ganin yadda Mom Nabila ke hararar ta ya sa ta saki fuska ta miƙe tsaye tare da gyara lulluɓin ta ta kalli Ikilima ta ce "To muje."
Su dai su Ammi kallon su suke ba wanda ya ce musu ƙala har suka shige ɗakin da Ammi ta shiga. Da mamaki Ammi ke kallon inda suka shiga ta dafe ƙirji tana tunanin dama Yarima yana cikin ɗakin ta shiga? Ras ! Ta ji gabanta ya faɗi tuna kalmar da ta faɗa a ɗakin ta yi ƙasa da kai jin Jakadiya ta shigo tana nuna musu inda aka tanadar musu abinci na musamman..
Suna shiga ɗakin Iman ta yi ta mamakin ganin komai na ɗakin kalar na ɗakin Abir ne, kenan ta faɗa masa kalar yadda take so ɗakinta ya zama? Hawaye ta ji sun cika mata kwarmin idanu ta yi saurin mayar da su tana sauke numfashi. Wani waje Ikilima ta buɗe wanda a iya ganin mutum zai ce wardrobe ne, ƙofa ce a ciki ta kunna hasken wajan ko'ina ya gauraye da haske, ita dai Iman wani mugun tsoro ne ta ji ya sake shigar ta tana tunanin anya kuwa Suhal ba ɗan shan jini ba ne? Jiki na rawa Ikilima ta riƙe hannunta suka soma taka matakalar tana cewa "Ya sunan Antyn nawa."
Baki na rawa ta ce "I.. Iman suna na."
Riƙe baki Ikilima ta yi tana ta mamaki dama wannan ita ce Iman ɗin da suka taɓa gaisawa a wayar Abir? Ba Ta ce mata komai ba suk ci gaba da tafiya sai ga su a wani makeken palo mai ɗauke da dakuna uku har da kitchen, baki Iman ta saki tana kallon ko'ina har ba ta san ba lokacin da Ikilima ta yi wucewar ta ta bar ta tsaye a tsakiyar palon. Photon Suhal ne manne a jikin bangon palon ya sha ƙananan kaya ya hakimce a kan kujera fuskarsa ɗauke da murmushi abin da ya dauke mata hankali kenan ta shagala. A hankali ya iso cikin sanɗa ya biyo ta baya ya rufe mata idanu, a firgice ta soma ƙoƙarin kwacewa amma yaƙi ba ta damar hakan sai kawai ta fashe da kuka tare da cewa "Waiyo Allah Anty Baby ashe nan gidan masu shan jini ne aka kawoni?"