Sashe 104
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yau Abir watan ta É—aya cif da rabi a cikin wannan gida, duk yadda Big boy ya yi tsammanin abin zai zo masa da sauki ya wuce tunaninsa, yana tsaka da haka Daddynsa ya kira shi ya ce ya je ya dauko shi daga airport, ba dan ransa ya so ba ya fita tsabar sauri ko kofar palon bai kulle ba ya wuce...
Abir na ganin shi ta taga har ya fita, ta lallaɓa ta buɗe ɗakin ta fita waje, cikin sanɗa ta dinga tafiya ta leƙo ta ga Maigadi ba ya bakin kofa, cikin azama ta nufi kofar ta bude a hankali ta fita ta mayar ta rufe, tana ganin ta fito waje ta kwasa a guje ta karya kwanar layin..
Sai da ta ci gudu sosai sannan ta iso bakin hanya ta tsayar da wata mota ta shiga, sai da ya fara tafiya sannan ya tambaye ta ina zai kai ta? Ta sanar da shi suka ci gaba da tafiya. Allah-Allah take ta gan ta a gida sai waiwayen bayan su take, gabaÉ—aya ta galabaita da kyar take numfashi har suka iso gida..
Ta maza ta yi ta fito daga ciki da kyar ta ce "ÆŠan tsaya na kawo ma kuÉ—in."
To ya ce mata ta daddaure ta nufi cikin gidan, da kyar da iya yin sallama tana tafiya jiki a mace, Tasakkawato da ta fito daga É—aki ta hange ta ai da sauri ta nufo ta. Kafin ta iso ta yanke jiki ta faÉ—i sumammiya.
Ƙwalla kiran su Maman Amal ta yi suka fito duk suka yo kan ta hankali a tashe....
_Maman Nusaiba ce_
[6/20, 8:43 PM] Ummu Amjad: : *A HAKA NAKE SON SHI*
Shafi na 51
ÆŠaukan ta suka yi su uku suka nufo É—akin Tasakkawato, hankalin Tasakkawato a tashe take kiran sunanta tana kuka, Maman Amal ta É—auko ruwan sanyi aka shafa mata a fuska. Ajiyar zuciya ta sauke tana motsa idanuwanta amma a rufe suke, sannu suka dinga jero mata tare da kiran sunanta ta kasa motsawa, sai zuwa can ta soma buÉ—e idanuwanta har ta buÉ—e su tar a kan su. Taimaka mata suka yi ta tashi zaune suka jingina ta da jikin kujera sai bin su take da kallo, Tasakkawato ta rungume ta tana faÉ—in "Alhamdu Lillah Allah mun gode maka, sannu Jiddo ina yake miki ciwo yanzu?"
Girgiza mata kai ta yi da kyar ta iya cewa "Mama ruwa."
Da hanzari Tasakkawato ta kawo mata gorar ruwa mai sanyi ta kai mata baki, da sauri ta soma sha har da lumshe idanu suka zuba mata ido cike da alhini, sai da ta shanye tas sannan ta janye gorar tana sauke numfashi. Abinci Maman Samira ta kawo mata tuwon Masara fara da miyar taushe, sosai ta ci tuwon dan taushen ya mata daÉ—i sosai, bayan ta gama ta kawo mata ruwa ta wanke baki da hannu, sai a lokacin ta yi gyatsa ta kalli Tasakkawato ta ce "Mama ina Zaiyan yake?"
Zama ta yi a kusa da ita tare da dafa kafaÉ—arta, hakan ya sa ta É—ago ta kalle ta ita kuma ta nisa ta ce "Ki huta tukun sai na sanar da ke komai, yanzu ba surutu ya kamata ki yi ba ki kwanta ki huta zuwa an jima zan miki bayanin komai."
Gabanta ne ya faÉ—i ta yi raurau da idanu sai ga hawaye sun zubo sharr ta turo baki ta ce "Please ki sanar da ni yanzu."
Rarrashin ta da dinga ita kuma ta ci gaba da kuka tana faɗin ina Zaiyan yake, ƙarshe ma ta sarƙe da tari ta yunƙura za ta tashi Tasakkawato ta yi saurin ruko ta, tambayar ta take ina za ta je?
Dafe ƙirjinta ta yi da yake mata zafi da daure ta ce "Mama amai nake ji."
Jin haka ya sa Tasakkawato ta nufi toilet da ita, sai da ta amayar da abin ta ci sannan ta samu salama zuwa lokacin ta galabaita matuƙa. Bayan sun fito ta kwanta a kan kujera tana rawar sanyi Tasakkawato ta dauki bargo ta rufe ta da shi, nan da nan zazzaɓi mai zafi ya rufe ta ta ƙudundune a bargo. Haka suka saka ta a gaba Maman Amal ta dubi Tasakkawato ta ce. "Ni kuwa wai har yau Zaiyan bai sake dawowa ba?"
Girgiza mata kai Tasakkawato ta yi tare da cewa "Bai sake dawowa ba tun ranar da ya bar gidan nan,ni yanzu tsoro na É—aya kar Jiddo ta shiga damuwa na rashin ganin sa in ta farka."
Haka suka ci gaba da tattauna maganar kowa jiki a sanyaye..
Tun da Zaiyan ya koma gidan su Abokinsa ya kasa nutsuwa, duk da abubuwan da suke gaban shi amma tunanin rashin matarsa ya fi komai tayar masa da hankali, idan abokinsa ya tambaye shi me yake yi wa zurfin tunani sai ya sanar da shi cewa kawai dai ba ya jin daÉ—in garin ne..
Yau ma kamar kullum da misalin ƙarfe 11:00pm na dare shi da Bashow suna zaune gaban computer, ɗago kai Bashow ya yi fuskarsa dauke da damuwa ya ce. "Aboki Wallahi ka ga na kasa kwato maka da account ɗinka, yanzu haka maganar da nake ma wanda ya yi maka hacking ɗin account ɗin ya yi posting."
Saurin janyo computer ya yi yana jin ranshi na ƙara ɓaci, rubutu ya ga gani an yi sak kamar shi ya yi, photon kan dp ya danna sai ya ga an canja wanda yake kai tun lokacin da yake cikin hankalinsa, ƙara zuƙo photon ya yi ya ga dai sak yadda yake dressing haka mai hacking ɗin ya yi nasa ya ɗaura. Ya cika da zallar mamaki ganin ikon Allah, sai da ya jima a haka sannan ya dauke idanuwansa daga kan photon, lumshe idanu ya yi yana jin yadda kansa ke mugun sara masa babu abin da yake gani in ya rufe idanu sai Abir da take masa gizo, ya ƙara kwantar da kansa a jikin kujerar yana tuna bakar ranar da ta raba shi da matarsa, gabaɗaya ya kasa nutsuwa tuna halin da take ta tashi ba lafiya sosai ga shi kuma an sace masa ita. Saurin buɗe idanu ya yi tare da janyo computer ya shiga Facebook, wani numbobi ya danna tare da yin ɗan rubutu ya tura, haka ya dinga wurgawa na Kusan minti biyar ya kafe computer da kallo sai gani ya yi ta nuna masa OK, saurin danna Ok ya yi sai ga shi ya kwato account ɗin sa. Hannu ya ɗaga sama ya ce "Alhamdu Lillah na kwato shi Bashow."
Murna suka yi sannan ya shiga Istagram nan ma ya kwato kayanshi har Tiktok sai da ya shiga ya kwato sannan ya janye computer yana fesar da numfashi, sai lokacin kuma ya dauki wayarsa ya lalibo number Abir ya danna kira, nan take aka ce masa wayar a kashe take..
Bashow da ya gaji da ganin yadda Abokin nasa ya zama sai ya matso kusa da shi yana daure fuska ya ce "Zaiyan!"
Kallon shi ya yi sai kuma ya kawar da kai yana jin idanuwansa sun cika da kwalla, hannu ya sa ya juyo da fuskarsa yana hura hanci ya ce "Yanzu Zaiyan ban kai matsayin da za ka faɗa min abin da yake damunka ba? Ko ka manta yadda muke tun muna yara? Ka sanar da ni duk abin da yake faruwa sai mu ga ta ina za mu ɓullo wa lamarin."
Hawayen da yake riƙewa ne suka samu damar zubowa, Bashow ya rude ganin hawayen abokin nasa ya shiga tambayar shi, "Don Allah ka sanar da ni abin da yake damunka Zaiyan? Ba ka dauki ni yadda na dauke ka ba kenan? Ai damuwarka damuwata ce ka faɗa min me ke faruwa?"
Ajiyar zuciya ya sauke yana jin yadda zuciyarsa ke masa zafi, bai taɓa sanin tsananin son da yake yi wa Abir har ya kai haka ba, Bashow ya takura sai ya sanar da shi hakan ya sa ya ɗago ya kalle shi yana goge hawaye ya ce "Bashow an sace matata."
"What? " Ya faɗa yana zaro idanu sannan ya ɗaura, "Wai kana nufin har aure ka yi amma ba ka taɓa sanar da ni ba? Haba Zaiyan me ya sa ka boye min auren da ka yi? Kuma ma ina ka baro Mama ka dawo Kano da zama?"
Ganin yadda ransa ya ɓaci Zaiyan ya ce "Bayan mun bar Kano na kamu da lalurar kwakwalwa."
Saurin kallon shi ya yi ya É—aga baki zai yi magana ya dakatar da shi, labarin komai ya sanar da shi har auren da kuma yadda suka dawo Kano. Kallon shi kawai Bashow ke yi yana sauraron wannan labari mai ban tausayi da takaici, nisawa ya yi ya ce "Yanzu haka ban san wani hali take ciki ba, ga shi ba ta da lafiya na bincika amma shuru."
Dafashi ya yi cikin tausayawa ya ce "In sha Allah za a gan ta, amma sai nake ganin ya kamata ka kuma koma wa gidan da kuke zama ko sun samu wani labari akan hakan. Tabbas na san Princess Abir a Tiktok ga ta da saukin kai, idan ka yi mata comment sai ta ma reply Wallahi na yi mamaki da ka ce ita ce ka aura É—iyar mashahurin mai kuÉ—in nan Alhaji Ibrahim Maitama, zan so na gan ta a fili saboda saukin kan ta. "
Jinjina kai ya yi ya ce "Wallahi ni sam na manta da haka saboda duk na É—imauce."
Haka dai suka ci gaba da tattaunawa inda Zaiyan ya yanke shawara bayan kwana biyu za su je su gani...
Bayan kwana biyun suka shirya shi da Bashow suka nufi gidan gaban Zaiyan na faduwa..