← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 120

Sashe 106

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi mai haÉ—e da hawaye take ganin wai yau ita ce Fatima ta rungume tana murnar ganin ta, janyo hannunta ta yi ita kuwa sai kallon su take dan so take ta yi tozali da Abdul. Shi kuwa bai ma san ta shigo ba saboda eapis ya saka saboda faÉ—an da suke, kalaman Fatima ne na karshe ya sa shi saurin É—agowa ai kuwa ya yi arba da ita, da wani irin sauri ya mike tsaye itama tana gano shi ta kwance hannunta ta nufe shi tare da sakin kuka, saurin taro ta ya yi ta faÉ—a jikinsa tana faÉ—in "Yayaaa."

Maman Nusaiba ce

[12/10, 11:36 Yamma] Anty Sarat (Mom Nusy 🌹): *A HAKA NAKE SON SHI*

Shafi na 52

Kuka take sosai tana faÉ—in "Yaya ashe akwai ranar da za ka iya shafe babina a rayuwarka? Ashe akwai ranar da za ka furta min kalmar tsana? Don Allah Yaya ka gafarceni in na yi maka wani lefi, wanda har ya sa ka yanke min wannan mummunan hukuncin."

Ɗago da ita ya yi yana share mata hawaye itama tana share masa, murya na rawa ya ce "Bab..Baby Wallahi babu abin da kika mini, hasalima ni ne zan nemi yafiyar abin da na aikata a gareki, ban san na aikata wannan abubuwan ba sai daga baya, ga muguwar da ta shiga tsakaninmu da ke nan azzaluma." Ya faɗa yana nuna mata Umma da ta yi baƙi wasu ƙuraje sun feso mata a jiki sai susa take tana kallon kowa na palon..

Ɗaya bayan ɗaya haka ta bi ta rungume su kowa na palon kuka yake, sai da ta zo kan Ammi sai ta tsaya tana kallon ta, tsoron isa gare ta take dan ba ta san ya za ta karɓe ta ba, gane hakan ya sa Ammi fashe wa da kuka ta miƙa wa Abir hannu tare da cewa "Zo nan 'yata Wallahi na yi nadamar abubuwan da nake miki, zo ki ji tsumin jikin mamanki."

Isa ta yi suka rungume juna suna kuka gwanin ban tausayi.. Bayan komai ya lafa ne Abdul ya É—ago ya kalli Abir ya ce "Baby ina Zaiyan É—in yake? Ko kin baro shi a gidan su Baba?"

Saurin tashi ta yi tsaye dan sai yanzu ma ta tuna da shi, ganin ahalinta ya mantar da ita komai, da hannu ta nuna musu shi tana narke fuska ta nufe shi. Dukkan su baki suka saki suna kallon wanda ta nuna musu a matsayin Zaiyan É—in, kowa gani yake kamar Suhal ne a tsaye. Grandma ta face majina ta ce "Ke Hauwa'u ba ma son shiririta fa, yanzu wannan É—in ne Zaiyanu? Wannan ai Suhal ne mijin Iman dan kin dauke mu makafi sai ki nuna mana shi ki ce shi ne Zaiyanu?"

Ƴar dariya Abir ta yi tana isa gare shi ta kamo hannunsa ba tare da ta ce matsa komai ba, amma da ido take masa alamar ya yi haƙuri, shi kuma ya yi shuru yana jin zafin rungumar ta da Abdul da Salim da suka yi. Zaunar da shi ta yi a gefen Abdul ta zauna a kusa da shi tana ƴar dariya, Abdul ya shafa kan Zaiyan ya ce "A'a, mutumin yau ba ko gaisuwa? Ko ka manta da Baba ne da ka masa dukan sakwara?" Ya faɗa yana tariyo dukan da ya ci a hannunsa. Sunkuyar da kai ya yi ya tuna da Abir ta sanar da shi Abdul ne yake kira da Baba, ɗago kai ya yi fuskarsa dauke da murmushi ya ce "Abba Dad sannun ku da gida, mun same ku lafiya? Kai kuma yanzu ai ba Babana ba ne sai dai na ce maka Yaya kamar yadda Baby ke kiran ka."

Sumar zaune Abdul ya yi sauran 'yan palon suka dinga kallon shi, Ammi ta kasa daurewa ta ce "Uwar masu gida ko dai mijin naki ya fara samun sauki ne?"

Kallon shi ta yi ta juyo da kallon ta ga Ammi ta ce "Ai ya jima da samu lafiya, yanzu yana cikin hankalinsa ras yake kamar kowa?" Ta faÉ—a cikin jin daÉ—i.

Baki suka haÉ—a wajan faÉ—in "Kai ma sha Allah! Mun taya ki murna har shi ma Zaiyan É—in."

Bayan an gama murnar samun lafiyar Zaiyan, Abba ya yi gyaran murya ya kalli kowa na palo sannan ya ce "Mamana ga dama maganar ki ce ake yi sai ga ki Allah ya kawo ki." Ya tsagaita sannan ya ɗaura "Ita ce silar duk wani abu da ya faru da wannan ahalin, har mahaifiyarki ita ta sa mota ta bige ta karshe ta rasa rayuwarta, ta cutar da ke cuta mai yawa." Ya ƙarashe maganar yana goge hawayen da suka gangaro daga kwarmin idanuwansa. Kallon Umma kawai Abir ke yi tana girgiza kai sai ta fashe da kuka tare da cewa "Kin cutar da ni Umma dayawa ba zan taɓa yafe miki ba ko wani irin hali za ki shiga, ke ce silar zamana marainiya gaba da baya me na miki Umma? Kin kashe min Uwa kin kashe min uba duk dan Abie ɗina yaƙi amincewa da buƙatarki? Wallahi na yi Allah wadai da kasancewar ki ɗaya daga cikin ahalina. " Kuka ne ya ci ƙarfinta har da shiɗewa take, saboda yau ɗin nan an fama mata ciwon da ke daskare a cikin zuciyarta.. Hannu ya sa ya kwanto da ita jikinsa yana bubbuga mata baya tare yi mata magana a saitin kunnenta ta yadda ba me jin abin da yake faɗa.

"My Wife please stop crying, kin Ga ba ki da cikakkiyar lafiya idan kina kukan nan zai haddasa miki ciwon kai, ƙarshe ki zo ki yi ta mai har ya kwantar da ke. Ba na son kukan nan kar Baby ya wahalar min da ke."

Tsayar da kukan ta yi ta janye jikinta daga nashi, sai da ta dauki lokaci cikin shuru duk suka zuba mata idanu.

"Na tsaneki daga ke har uwarki da ƴar'uwarta shi ya sa na sa aka kashe su, ke ma na so na aika ku daga ke har Abdul amma aka kasa yi min maganin ku, shi ya sa na bi wannan hanyar." Umma ce ke faɗa tana kallon Abir, sautin muryar Umma ya razana ta ta maƙale a jikin mijinta.

Daddy ya nuna ta da hannu ya ce "Wallahi kin taɓe duniya da lahira Baraka." Ya kalli Abir sannan ya ɗaura da cewa "Mamana kin ba mu magana a dunƙule, ki warware mana zare da abawa dama tana da sa hannu a lamarin Yaya Ibrahim?"

Dogon numfashi ta ja sannan ta ce "Duk abubuwan da na sanar da ku lokacin da na kuɓuta daga wajan wanda suka sace ni ƙarya na faɗa muku, hakan kuma ya samo asali ne sakamakon barazana da suke min da cewar idan har na nuna na san wani daga cikin su za su kashe kowa na familyn nan. To ni kuma tsoro ya shige ni shi ya sa na faɗi cewa wasu ne suka tare mu a hanya. "

Tagumi Abba ya yi ya ce "Muna jin ki ki sanar da mu komai da ya faru, kar ki ji tsoron kowa a cikin wanda suka miki barazana."

Jinjina kai ta yi sannan ta soma fadin "Ranar wata Sunday da safe naje zan gaishe da Abie sai na ji sautin muryarsa yana cewa, "Wallahi Baraka idan ba ki fita a harkata ba zan miki rashin mutumci, kuma yau ɗin nan ba gobe ba zan sanar da mijinki duk abin da kika min na rashin ɗa'a." Jin ya ambaci sunan Umma sai na yi ta mamaki, amma haka na ja ƙafa na shiga ɗakin na same shi tsaye yana safa da marwa, jin sautin murna Umma na yi ta cikin wayar tana cewa "Matuƙar ba ka amince da buƙatata ba za ka ga matakin da zan ɗauka a kan ka, kuma dole ma ka samar mana gidan da za muke haduwa muna kasancewa da juna, idan ba haka ba Billahil Azim zan nuna maka wace ce Baraka, na fi ka shu'umanci. Tun ina ƙarama nake dakon soyayyarka amma ka tashi ka je ka auro wata bare dangin matsiyata wadda asalinta ma ba a sani ba. " Tana fadin haka ta kashe kiran. Zama Abie ya yi cike da damuwa na iso na zauna kusa da shi, kallona ya yi na ce masa, "Abie wace ce wannan matar da take ce ma ka nema muku gida?"

Gyara zama ya yi ya dube ni sannan ya ce "Mamana duk da ƙananan shekarunki amma kin san ba na ɓoye miki komai ko?"

Na gyaɗa masa kai kamar wata ƙadangaruwa, ya ɗaura da cewa, "Wannan da kika ji a waya Baraka ce matar Daddynki."

Waro idanu na yi na rufe baki sannan ya daura, "Ban san me ya shiga kan Baraka ba ta takura min, yanzu kamar ni za ta nema da aikin fasadi? Ko ba komai ai ni yanzu Yayan mijinta ne bai kamata take nema mu aikata saɓon Allah ba, wai ni yau take kallon tsabar idona ta ce tana so na muke keɓewa muna cin amanar ɗan'uwa dan ta mayar da ni ɗan iska." Ya faɗa yana huci. Sosai maganar Abie ta girgiza ni sai ga Mom ta shigo ta zauna a ɗayan gefen Abie ta ce "Ai Abban Abir ka ba wa iska ajiyarta kawai, yo hauka ake yi ba ta san nasan duk tsiyar da take shukawa ba."

Kallon Mom na yi duk jikina ya yi La'asar gabaÉ—aya maganganunsu sun saka ni cikin kalar wani yanayi na jimami da al'ajabi, da kyar na iya cewa, "Mom dama Umma bayan cin mutumcin da take miki a gidan nan ashe akwai wani mugun abin da take aikatawa? Gaskiya Umma ta yi nisa ba ta jin kira."

Cike da takaicin Umma Mom ta nisa ta ce "Zan sanar da ke wannan maganar saboda halin rayuwa, sannan kar ki kuskura ki sanar da kowa har sai lokacin faÉ—ar maganar ya yi."

Gyara zama na yi cike da zabuwa na baza na zomo ina kallon Mom.

"Khairat da kike gani ba jinin wannan gida ba ce, É—iyar wani bokanta ce wanda yake mata aiki akan duk abin da take son aikatawa."
Chapter 106 · 0% Book details