Sashe 78
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Wani irin nauyi ya ji zuciyarsa ta masa, har ya miƙa hannu zai taɓa nata ya ji wani abu ya danne wannan yanayin da ya taso masa nan da nan ya janye hannun, tashi ya yi da kyar yana jan ƙafa ya isa bakin motarsa ta yi saurin tashi duk da tana jin ciwo ta daure ta runtse idanu ta take ƙafar ta nufi motar, ganin haka shi ma Zaiyan ya bi bayan ta ko ajikinsa sai ma saurin isa gefenta ya yi ya riƙe hannunsa. Yana ƙoƙarin tashin motar ta iso tana share hawaye ta ce "Don Allah Yaya kar ka ce za ka yi driving da kanka ka bari na kira ma Ali ya zo ya kaika."
Wani irin kallo ya watsa wanda ya sa ba shiri ta ja da baya tana sakin kuka, me yake damun Yayan nata? Ko dai shi É—in ma ya samu tabin hankali ne? Tsayar da kukan ta yi ba shiri ganin yadda Zaiyan ke tayata kamar wasu yaran goye.
Shi kuwa Abdul cikin zafin rai da na zuciya ya ja motar ya nufi Get ɗin gidan duk da rawar da ƙafarsa take, amma wutar ƙiyayyar ta da ke ruruwa a zuciyarta ta mantar da shi an dake shi, da sauri Maigadi ya matsa ganin zai buge shi, shi kan shi cike yake da tsananin mamaki da al'ajabin abin da ya faru a gaban idanuwansa, dan a iya saninsa yasan Abir dai ƙanwar Abdul ce wadda ba ya son ɓacin ranta duk abin da take so shi yake mata, sai ga shi yau shi ne har da dukan ta..
A wajan ta durƙushe ta kalli Zaiyan da yi tsaye yana turo baki, tashi ta yi ta faɗa jikinsa ta ci gaba da kuka tana faɗin "Rashin uwa babban ciwo ne a rayuwa, ya Allah ka dawo min da hankalin Yayana ya daina tsana ta abin na taɓa min zuciya, Waiyo Abie na nasan da kana raye ko da duk duniyar nan za su taro su tsaneni kai ba za ka tsaneni ba, ya Allah ka dubi marainiyarka ka kawo mata mafita. "
Shi kuwa ƙara rungume ta ya yi ya ci gaba da nasa kukan, sai da ya ji ta tsayar da kukan shi ma ya tsayar da nasa ta ɗago daga jikinsa tana share hawaye. Fuskarta ya ɗago ya sa hannu yana share mata hawayen itama ta shiga share masa nasa, sosai zuciyarta ke ƙara karaya da lamarin Yayan nata ta sake komawa jikinsa ta sa sabon kuka.. Wannan karon Zaiyan bai yi kuka ba sai ma ƙoƙarin raba ta da jikinsa da yake yana fadin "Anty Baba mugu ne sai na kashe shi tun da ya dakeki."
Sai da ta yi mai isar ta har Maigadi ya ga abin ba na ƙarewa ba ne ya iso wajan su, runsunawa ya yi ya ce. "Ranki da daɗe wai lafiya Oga ya miki wannan ɗanyan aikin?" Girgiza kai kawai ta yi zuciyarta na zafi ta kama hannun Zaiyan suka nufi ciki, riƙe baki Maigadi ya yi yana ƙara jinjina girman abin da har zai sa Abdul ya daketa, haka dai ya juya ya koma bakin aikinsa yana jiran dawowar su Baba..
Suna shiga dakinsu daret toilet suka nufa dan zuwa lokacin ta daina kunyar cire kaya a gaban Zaiyan tun da ba wani hankali yake da shi ba da zai gane daidai da rashin daidai, cire masa nasa kayan ta yi ta tara musu ruwa mai ɗumi ta dauko sabulu ta kama hannunsa suka shige cikin bahon wankan. Lumshe idanu ta yi gabadaya kanta ya yi nauyi ƙwaƙwalwarta ta cunkushe, ajiyar zuciya ta sauke tana yin hamdala da wannan lamari ya faru su Baba ba sa gidan.. Sai da suka yi ta wasa da kumfa ita da shi sannan ta cuɗa shi shi ma ganin yadda ta masa ya dauki sabulun ya cuɗa ta, bayan sun gama ta sa masa towel sai dariya yake ya iso bakin madubi sai ya waro idanu yana dariya ya kama hannun Abir ya janyo ta iso kusa da shi ya nuna mata da hannu ya ce "Anty kalli shi ma Abokina ya sa irin wannan abin da kika sa mini." Sake kallon madubin ya yi sai ya ga Abir ai kuwa ya ɗaga hannu zai kurma ihu ta yi saurin rufe masa baki ya kwashe yana nuna mata ya ce "Shege Abokina ashe shi ma har yana da mama ga ta nan irin Anty."
Ganin abin nashi ba na karewa ba ne ta kama shi suka fito, mai ta shafa masa ta miƙa masa kayansa ya yi tsaye yana bin kayan da kallo yana taɓe baki, girgiza kai ta yi ta shirya shi da kanta saboda tasan hali indai yaƙi amsa to ba zai sa ba sai dai ita ta shirya shi. Fuska ta hɗe alamar ta yi fushi da shi, ganin ta yi fushi sai ya sa iso gaban gadon ya zauna a ƙasa irin na ɗa da uwa. Kallon shi ta yi ganin yadda ya rausayar da kai sai ta ji ya ba ta tausayi sosai, hannu ta miƙa masa ya yi saurin tashi ya hayo gadon ya yi zaune yana kallon ta, murmushi ta yi ta ja da baya ta jingina da jikin gadon ta buɗe masa hannu ya yi saurin zuwa ya lafe a jikinta yana sauke ajiyar zuciya.
Kamar wani yaro ta shiga bubbuga bayansa cikin ɗan lokaci sai jin saukar numfashinsa ta yi alamar ya yi bacci, a hankali ta lallaɓa ta kwantar da shi ya motsa ya ƙara riƙe ta sai ta kwanta har sai da bacci ya kama shi gadan-gadan ta raba shi da jikinta ta sauka a gadon ta rufe shi da bargo ta fita. Wajan Maigadi ta isa ta ce masa kar ya sake ko da su Baba sun dawo ya sanar da su zuwan Abdul da abin da ya faru a tsakanin su, to ya ce mata ba dan ya so ba sai dan ganin yadda ta marairaice sai ta ba shi tausayi. Godiya ta masa ta dawo ciki ta dinga safa da marwa a palon ta rasa ta inda za ta ɓullowa lamarin familyn nata, ganin dai lokaci na tafiya ta shiga kitchen ta ɗaura musu shinkafa da wake da miya, bayan ta gama ta gyara ko'ina ta rufe abincin ta dawo ɗaki ta samu har zuwa lokacin Zaiyan bacci yake hakan ya mata daɗi. Kayan jikinta ta canja ta ɗauro alwala jin ana kiran Sallar Azuhar, bayan ta gama Sallah ta ji sallamar Inna da Baba hakan ya sa ta cire hijab ta nufo palon.
Murmushi ta yi tana isa ta amshi ledar hannun Baba ta ce "Baba sannun ku da zuwa ya hanya?"
Murmushi ya yi ya ce "Alhamdu Lillah Hauwa'u ya gidan? Ina shi mutumin yake?"
Tashi ta yi tsaye tana ce musu ai bacci yake ta wucewa kitchen, ruwa ta kawo musu mai sanyi suka sha. Bayan Baba ya dawo daga Masallaci ta gabatar musu da abinci, har sun fara ci sai ga Zaiyan ya fito yana sosa kai ya iso inda take ya zauna,riƙe baki Inna ta yi ta ce "Zaiyan ko ka mana sannu da zuwa ma?"
Turo baki ya yi ya ce "Inna Baba ya zo ya daki Anty ni kuma na rama mata." Ya faɗa yana jumƙar shinkafar ya kai baki.
Aje cokali Baba da Inna suka yi suna kallon Abir da ta tauna abinci ta kasa haÉ—iyewa sakamakon maganar Zaiyan, Baba ya ce "Hauwa'u shin da gaske ne abin da Zaiyan ya faÉ—a?"
Murmushin yaƙe ta yi wanda ya fi kuka ciwo tana danne kukan da ke shirin kwace mata, hadiye abincin ta yi da kyar ta ƙara sunkuyar da kai tana boye hannunta da zuwa lokacin ya kumbura sai azabar ciwo yake mata daurewa kawai take, a hankali ta ce "A'a Baba ba haka ba ne, a ina ma ya ga Yaya a gidan nan." Ta faɗa cikin ƙarfin hali ta ci gaba da cusa abincin ba dan yana mata daɗi ba.
Kallon juna Inna da Baba suka yi kowanne yana juya maganar a ransa, idanuwan Inna ne ya kai kan hannun Abir na hagu da ya kumbura sai ɓoyewa take, da sauri Inna ta kama hannun wanda sanadin hakan ya sa Abir ta zabure tana salati sakamakon ciwon da ya ziyarce ta, Inna ta ruɗe ta sakar mata hannun tana mai kare mata kallo cike da tuhuma ta ce. "Tabbas Hauwa'u akwai abin da ya faru bayan mun fita, kuma da akwai ƙamshin gaskiya a maganar Zaiyan." Ta faɗa tana aje cokalin da ke hannunta ta janye abincin daga gaban ta. Kallon Zaiyan Baba ya yi da yake ta cin abinci duk ya zubar da abincin, girgiza kai ya yi ya nisa ya ce "Lalle da gaske ne Abdullahi ya zo gidan nan, me kika masa haka har ya cutar da ke haka?"