← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 120

Sashe 46

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata ɗaya aka saka dan an ce Suhal zai yi tafiya zuwa ƙasar Turkiyya in an yi biki sai mu wuce tare, naji daɗi sosai dan dama ni ina son na ga naje ƙasashen waye...

Saura sati biyu bikinmu sai Maman Bishira ta ce a kawo ni Nigeria tana so za ta min gyara na musamman, da farko Mama taƙi yarda ta ce ai indai maganar gyara ne a nan Niamey ba za a nuna musu ba ta bari ayi min à nan, amma sai Bishira ta kafe har da kuka wai ita fa ta nemo mai yin gyara tun daga Maiduguri kar na watsa mata ƙasa a ido, jin haka ya sa na ce Mama ta bari naje in ya so ana saura sati biki sai mu tafi har Bishira. Ba dan Mama ta so ba ta amince amma ta ce na bari Baba ya dawo aji mai zai faɗa, yana zuwa na sanar da shi shi ma da farko yaƙi maganar na yi ta kuka ina roƙon shi da ya bari naje kwana biyar kawai zan yi, da kyar ya bari ya ce Halima ta rakani duk da garin kakanni na ne na saba zuwa. Da dare na samu Suhal na faɗa masa ya ce bai yarda na fita ko kofar gida ba, raina ya mugun ɓaci amma haka na haƙura ina ta lallaɓa shi amma fir ya nuna bai amince ba..

Da na faɗa wa Bishira yadda muka yi da Suhal sai ta hau sababi tana cewa ai shi ba ubana ba ne yanzu ba ya da ikoa kaina tun da ba a ɗaura mana aure ba, haka ta yi ta zuge ni tun bana ɗauka har na ɗauka na zo ina ta yi masa mita ya hana ni tafiya ga shi lokaci tafiya yake yi. Ganin na takura masa har na yi fushi bana daukan kiran sa ya ce indai har ina so na tafi to fa lalle sai dai a ɗaura mana aure in yaso da na dawo shagali kawai za ayi a kaini gidansa, na ce na amince na kashe wayar dan lokacin haushi nake ji na jan mini rai da yake na aje wayar, Mama na faɗawa komai ba ta ce komai ba sai da Baba ya zo ta sanar da shi, nan shi ma yake sanar da ita sun yi waya da Maimartaba ya sanar da shi kuma ya amince da hakan.. Haka kuwa aka yi washegari da safe aka ɗaura aurena da Suhal a Masallacin Unguwar mu akan sadaki jika hamsin saifa, da yamma na shirya ya cire min ticket na ce Halima ba za ta bi ni ba ni kaɗai zan tafi. Dama tun da dare Halima ta sheda mini ba za ta bini ba, haka ya kaini filin girgi wanda zai dauke ni zuwa Kano ta dabo dimbin giwa. A ranar sai ya yi ta kallo na kamar ya ga sabuwar halitta, abin ya dameni na ce masa "Ma shéri wai lafiya kake kallo na haka?"

BuÉ—ar bakinsa sai cewa ya yi "Ma famme kawai bana son tafiyar nan taki, sai naji kamar karki tafi mu tafi gida daga nan mu yi zaman mu ba sai an yi wani taron biki ba."

Murmushi na masa kawai dan yadda na ci buri akan bikin nan nawa taya ma zan yarda a yi min haka? Muna tattaunawa girji ya sauka aka soma kiran fasinjoji muka tashi ni da shi muka nufi jirgin, yana tsaye na shiga girjin yana ɗaga min hannu, da na zo bakin ƙofa na juyo na ɗaga masa hannu sannan na shige. Ana gama shiga jirgi ya tashi ina ta murna yau zan haɗu da Bishira ƙawata wadda kullum take min ƙorafin yaushe zan zo musu visit...

Jirgin mu na sauka É—an kanwar Mama ya zo ya É—auke ni muka tafi gidan kakanni na, bayan mun isa na yi wanka na huta muka gaisa da 'yan gidan na sanar da kakata dalilin zuwan nawa duk da Mama ta fada musu..

Ƙarfe 8:30 ina kan darduma na gama Sallar isha'i sai ga kiran Bishira ya shigo wayata, dauka na yi ko gaisawa ba mu yi ba ta hau yin masifa wai me ya sa na sauka a gidan kakanni na bayan zuwan da na yi dan ita na zo? Ni dai haƙuri na ba ta dan Bishira irin masifaffun mutanen nan ne masu saurin fusata, nan ta sheda min ga ta a ƙofar gidan kakanni na na fito mu tafi mai gyaran jiki tun da safe ta zo tana jiran zuwana. To na ce na kashe kiran ina son na tambaye ta wa ya mata kwatancen Unguwar Kakanni na amma ina tsoron ta rufe ni da masifa, haka na saka hijabi na dauki jakata ƴar goye na goya na bar wasu kayan a ɗakin kakata na fito na sheda mata Bishira ta zo, fatan alkhairi ta min na amsa da amin na wuce da sauri ganin kiran Bishira ya sake shigowa a karo na biyu...

Ina fita na ganta a wata dalleliyar mota fara sol sai sheƙin sabuntaka take, na isa cike da farin cikin ganin ta na kwankwasa glas ɗin motar kasancewar shi baƙi bana ganin ta ina daga waje. Fitowa ta yi cikin shigar ta ta alfarmar kamar yadda nake ganin ta a waya ta washe baki ta rungume ni kamar ba ita ba ce ta rufe ni da masifa ɗazu. Murna muka yi da ganin juna sannan ta amshi jakata ta sa a baya na zagaya na shiga gaba kujerar mai zaman banza ta ja muka tafi.. Sai da muka yi tafiya ta awa daya sannan muka zo wani tantsameman gida a Nassarawa J R. A, Ina ta santin gidan yadda ya tsaru tun kafin ma na shiga ciki, hon ta yi aka bude mata get ta ja muka shiga ciki ta yi packing a inda aka tanada dan aje mota... Dam! Naji gabana ya faɗi ganin wani hamshaƙin mutum ya fito cikin shiga ta alfarma ya nufo motar da muke, da kan shi ya bude min ƙofa na fito cikin girmamawa na rusuna dan da ganin sa na aiyana a raina mahaifin Bishira ne, a nutse na ce masa "Daddy barka da gida, mun same ku lafiya?"

Washe baki ya yi tare da cewa "Haba dai 'yata tashi maza kar ki sa ƙura a kayanki muje ciki."

Murmushi na yi in jin daɗin tarbar da na samu a wajan mahaifin Bishira, ta zagayo da jakata ta kama min hannu har da shi na biye da mu muka bi wata hanya,. A wani babban palo muka tsinci kanmu sosai na nuna kauyenci duk da ba yau na saba ganin palo irin wannan ba dan ko na gidan da Suhal ya min ya fi shi ado da komai, amma dai sai na ga wannan ɗin ya fi nawa tsaruwa. Zama muka yi aka kira wata hamshaƙiyar mata ta iso ta sha ado ta min barka da zuwa na amsa ina sunkuyar da kai, Bishira ta ja ni ta kaini wani ɗaki mai kyau da komai a ciki na bukata ta ce min tana zuwa na yi wanka..

Bayan na fito daga wanka na ci abinci Bishira ta fito da ni harabar gidan tare iyayenta kamar ba dare ba ne dan ko'ina tar haske ne ya mamaye, haka muka zauna har na soma jin bacci sannan ya ce mu je mu kwanta..

Washegari mai gyaran jiki ta soma ta dinga gyara ni ta ko'ina, duk inda na wuce sai na bar kamshi hatta kayan sakawata ƙamshin ya zauna a jiki. Ranar kwana na uku ne na Bishira ta ce na ba ta wayata tana son yin waya da saurayinta ba ta caji a wayarta, ban mata muso ba na ba ta dan ni ma a lokacin mun gama hira ni da masoyina.. Wasa-wasa har dare ban sake jin ɗuriyar Bishira ba sai na fito palon gidan inda a nan na ga Iyayen Bishira suna hira na iso ina sunkuyar da kai ga ƙamshi na tashi a jikina, baban Bishira ya tashi da kan shi ya nuna min inda ya zauna ya ce na zauna a gefen shi, kunya na ji sai ya yi dariya ya ce ai shi kamar uba yake a gareni jin hakan ya sa ina ɗari-ɗari na zauna a kusa da shi, sai da na gaishe su na ce "Daddy dama Bishira ce ta ari wayata tun safe ban sake ganin ta ba, ko ina ta tafi haka?"

Ƴar dariya na ga ya yi ya kamo hannayena ya ce "My Daughter kwantar da hankalinki ai ta tafi wajan party sai gobe za ki gan ta." Baki na saki ina kallon shi ina nanata kalmar party a raina, ban sake cewa komai ba na tashi na koma ɗakin da aka sauke ni. Haka kawai naji hanalina bai kwanta da gidan nan ba, amma na haƙura in Bishira ta dawo gobe zan koma gidan kakata daga can sai na koma Niger. Washegari na tashi ban ga Bishira ma nan hankalina ya tashi, da na fito sai na ga wasu 'yan mata su biyar waɗanda ba za su fini à shekaru ba, dan a lokacin shekaruna 20 cif, Maman Bishira ta ce na zo mu zauna na iso na yi wa sauran barka da zuwa, daga kayan jikin su za ka gane yaran ɗiyar masu ƙaramin ƙarfi ne..

Haka ranar na wuni ina saƙa da warwara na rasa a inda zan samu waya na kira Bishira na mata tatas dan ta kaini bango, shuru kamar an aiki bawan garin uwarsa ba ta dawo ba. Da dare ina kwance ina bacci na ji ana zuge min zip ɗin riga, kasancewar ina da nauyin bacci ban damu ba sai na gyara kwanciyata na ci gaba da bacci, kamar wasa na ji ana min yawo a jiki har ana neman cire min rigar tawa na farka a firgice in zare idanu, wa zan gani? Baban Bishira na gani zaune kan gadon da nake daga shi sai gajeran wando yana ƙoƙarin damƙo ni, a zabure na matsa ina zaro idanu cikin tashin hankali na ce "Daddy lafiya?"
Chapter 46 · 0% Book details