← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 120

Sashe 26

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi ta sakar masa ta ce "Zan kawo ma ai yanzu, Yaya ya kamata fa a taimaka masa da wanka a ba shi wani kayan." Ta faɗa tana kallon Abdul.. To ya ce mata sannan ta sa aka kawo masa shinkafa da miya, haka ya barbaje ya dinga ci yana zubarwa har ya gama ta miƙa masa ruwa ya sha sannan ya shiga jaddada mata bredi da rawaninsa ba ta ba shi ba, so yake ya tafi fada..

Ammi ta gyaÉ—a kai tana kallon Zaiyan ta ce "Sannu ka ji bawan Allah."

Ko kallon ta bai yi ba, gabaÉ—aya kowa ya tashi ya rage daga Grandma sai Abir..

Bayan ya gama Abdul ya dawo da maza huÉ—u daga cikin masu tsaron gidan ya ce su É—auke Zaiyan su tafi da shi, Abir ta so in magana amma ganin fuskar Abdul ba wasa sai ta yi shuru da bakinta aka yi wa Zaiyan wayon cewar bredi za a ba shi suka É—auke shi...

*NIGER*

Masarautar Niamey.

Hon ake yi Maigadi ya tafi a guje ya buɗe get ɗin, motoci ne farare su takwas a jere suka dinga shigowa ɗaya bayan ɗaya, suna gama paka motocin Dogari ya fito da sauri motar kusa da wadda ya fito ya buɗe ya ɗauko wani jan capet ya shinfida daga bakin ɗaya daga cikin motocin har zuwa wata ƙofa ruwan gold. Saurin dawowa ya yi ya buɗe mota ta biyar yana faɗin "Gyara kimtsi da kyau sauka lafiya Yarima." Sai da aka sauƙi kusan minti uku sannan Yarima ya miƙo kyakyawar farar ƙafarsa waje, sai can ya miƙo ɗayar ya fito gabaɗaya, dogo ne sosai kyakyawa fari kamar Balaraben Saudiya, yana saje wanda ya kwanta luf sai ƙyalli yake haka ma sumar kansa a kwance take luf ga ta yi ɓaki luɓuk. Ƙafarsa sanya take da takalmi mai kama da na fata, jikinshi sanya yake da alkyabba kalar kayan da yake jikin Red color. Wani irin ƙamshi yake zubawa na musamman sai bin harabar gidan yake da kallo yana murmushin gefen baki wanda in ba lura ka yi ba za ka taɓa cewa ya yi ba. Tsadaddan ogogon da ke manne a hannunsa na hagu ya ɗago hannun ya kalla, inda ya nuna masa karfe 2:30pm ya lumshe idanuwansa ya shaƙi iska yana buɗe su akan hannun nasa.

WaÉ—anda suke wajan suka soma masa barka da zuwa yana É—aga musu hannu.

Capet ɗin da aka shinfida ya suma takawa a hankali ana ta masa kirari, duk wanda ya zo wucewa sai ya yi sauri ya zo ya kwashi gaisuwa, ganin sun kusa isa wata ƙofa sai ya ɗaga musu hannu suka ja da baya suka tsaya a bakin ƙofar.

Wani tamfatsetsan palo ne na alfarma wanda ya sha kayan ado capet ɗin kansa in kana takawa kamar kana tafiya akan kafita, ya shigo da sallama a nutse cikin takunsa na izza da mulki ya zauna. Ɗaya bayan ɗaya Hadiman sashen suka dinga zuwa suna masa barka da zuwa shi kuma yana ɗaga musu hannu, sai da ta ƙarshe ta zo yatsar dai ta, cikin girmamawa ta durƙusa tana yin ƙasa da kanta saboda tasan halin Yarima sarai baya son ake kallon shi, ajiyar zuciya ya sauke ita har ta ma cire rai da zai ce mata wani abu sai ta ji ya yi gyaran murya. Gyara zama ya yi yana wani ciccin magani kamar an masa lefi fuskar nan babu annori ya ce "Jakadiya Mamma fa?" Ƙara sunkuyar da kai ta yi cikin girmamawa ta ce "Ranka ya daɗe tana ciki yanzu na gama shirya ta." Bai ce komai ba ya mata alama da ta tafi, da hanzari ta tashi ta wuce. Sai na ya ɗauki kusan minti biyar a zaune yana shan ƙamshi sannan ya miƙe ya nufi ɗakin, a hankali ya shiga inda ya hango ta zaune ta ƙurawa waje ɗaya idanu, da ƙyar ya iso ya zauna a gabanta murya na rawa ya ce "Mamma.!!!..

_*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_
[6/20, 7:45 PM] Ummu Amjad: _*~A HAKA NAKE SON SHI~*_

_+966577675904_

*Arewabooks.com: Saratalkasum1897*

Shafi na (15)

Da ƙyar ya iso ya zauna a gaban ta murya na rawa ya ce "Mamma!!" A hankali ta juyo ta zuba masa idanu tana masa kallon irin ta ga baƙuwar fuska, sai da ta ɗauki lokaci tana kallon shi sannan ta sakar masa murmushi tare da miƙa hannu ta shafa fuskarsa, bakinta na motsawa kamar mai son yin magana. Wani kalar zazzafan numfashi ya fesar ya ɗaura nasa hannun akan nata cikin wani kalar yanayi wanda shi kansa ya kasa gane wani hali yake ciki, a sanyaye ya kuma cewa "Mamma sannu Allah ya ba ki lafiya."

Murmushi ta kuma sakar masa hawaye sun cika mata idanu sai kallon ɗan nata take cike da tsabanin so da ƙauna, zare hannunta ta yi ta janyo abincin da aka jera mata da kayan marmari, wanda ko kallon abincin ba ta yi bare ma ta ci, buɗe wata ƙatuwar kula ta soma yi ya yi saurin tashi daga inda yake ya iso gefen ta ya amsa ya buɗe kular. Shinkafa ce fara a ciki ya buɗe ɗayar inda ya ga miyar ta sha isashen nama da kayan haɗi sai zuba ƙamshi take, lumshe idanu ya yi yana ɗan murmushi ya buɗe su akan Mamma ya ce "Za ki ci wannan na zuba mana?" Ya faɗa yana rausayar da kai, ita kuma ta gyaɗa masa kai hakan yasa ya zuba musu ya aje a gaban su. Haka ta dinga ɗauka tana ba shi a baki fuskarta ɗauke murmushi shi ma haka. Bayan sun gama ya janyo ruwan da aka zuba a cikin wani golden ɗin ɗan ƙarami kofi ya tsiyaya cikin wata roba, hannunta ya janyo ya wanke itama ta wanke masa nasa, ya yunƙura zai tashi ya ji ana buga ƙofa. Kallon Mamma ya yi ita ɗin ma ƙofar ta kalla, gyara zama ya yi tukun ya bada izini aka shigo.

Jakadiya ta shigo tare da rusunawa ta ce "Ranka ya daɗe Maibartaba ya ce a sanar da kai yana kiran ka a can ɓangarensa."

Annorin fuskar Yarima ne ya ɗauke ya kalli Jakadiya ya mata alama da kwashe kayan abinci, sannan ya kama Mamma ya miƙar da ita tsaye suka nufi wata ƙofa.. Taɓe baki Jakadiya ta yi tana jinjina izza da girman kai irin na Yarima, ta kira hadimai suka kwashe kayan wasu suka gyara wajan tare da kunna turaren wuta aka aje a wajan.

Suna shiga Yarima ya buɗe wani wuri a ɗakin sai ga Alkyabba kala-kala a jere, ya ɗauki kalar wadda ta zo daidai da kayan jikin Mamma ya sanya mata tare da fesa turare mai daɗin ƙamshi sannan ya zaunar da ita ya fita a ɗakin. Bai jima sosai ba sai ga shi ya buɗe ƙofar ɗakin Mamma, sanya yake da wata blue ɗin jallabiya ƴar Dubai ya ɗaura hula kalar rigar, ga wani fitinannan ƙamshi da yake yi yana taku ɗaiɗai har ya iso cikin ɗakin ya samu Mammi a zaune a inda ya barta. Sunkuyawa ya yi ya kama ƙafarta ya sanya mata wani lallausan takalmi mai kyau, ya ɗago ya ce "Mamma wai ina Auta take ne?" Ya faɗa yana murmishi duk da ya san ba amsa za ta iya ba shi ba. Girgiza maza kai ta yi tana masa nuni da ta tafi makaranta hakan yasa ya sauke ajiyar zuciya sannan suka bar ɗakin.

A tsaye suka samu Jakadiya tana jiran fitowar su tana ganin su ta rusuna ta ce "Barka da fitowa Fulani."

Gyaɗa mata kai kawai Mamma ta yi suka wuce yana gaba suna biye da shi a baya ita da Jakadiya da wasu Hadimai biyu , suna isa bakin wata ƙofa wani Hadimi ya zo da sauri ya buɗe musu yana faɗin "Barka da sauka Yarima Allah ya ja da kwanan ka, barka da zuwa ranki ya daɗe ." Ya faɗa yana yin murmushi.

Shi ma Yarima murmushin ya yi wanda ya sa Hadimi sakin baki, saboda bai taɓa ganin Yarima ya saki fuska ba har ya yi murmushi sai yau. Goya hannayensa baya ya yi ya kalli Hadimin tare miƙa masa hannu ya ce "Halil ya kake?"

Sunkuyar da kai ya yi yana ƙara shiga al'ajabin Yarima, sai da Yarima ya yi gyaran murya sannan ya ɗago ya ga ya sake miƙa masa hannu, ya yi saurin amsa yana washe baki tare da cewa "Ina nan lafiya ranka daɗe, fatan an dawo lafiya?"

Bai sake ce masa komai ba ya yi gaba ya shige su Mamma na biye da shi.

Halil ya ɗan matsa daga bakin ƙofar yana jin daɗi yau ya taɓa hannun Yarima, wani da ke kusa da shi ya ja tsaki ya ce "Uban neman guri har wani wage baki kake yau Yarima ya kula ka." Halil ya ɗage masa gira ɗaya ya ce "To ya son ranka ɗan hassada da bakin ciki? Ai duk wanda Yarima ya kula to shi mai matuƙar sa'a ne a cikin masarautar nan, ni kuma dama masoyin shi ne dan haka ina ƙaunar shi." Yana gama faɗin haka ya wuce abin sa..

Suna shiga babban palon suka samu Maimartaba tare da Kilishi da Sarauniya Bilkisu sun hakimce a gefen Maimartaba kowacce sai zuba izzarta take, Yarima ya ƙara ɗaure fuska ya ruƙo hannun Mamma suka ƙaraso. Murmushi shinfide kan fuskar Maimartaba yana kallon ɗan nashi, hannu ya miƙa wa Mamma ta ɗaura nata a kai ta zauna a daf da shi tsakanin Kilishi da Maimartaba a nan ya mata guri ta zauna, wani kallon banza Kilishi ta yi wa Mamma tana ɗago kai suka haɗa idanu da Yarima da fuskar nan take tamke kamar bai taɓa yin dariya ba, saurin kawar da kai ta yi tana yin kwafa.
Chapter 26 · 0% Book details