Sashe 115
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ko da ta kawo nan a maganarta ta fashe da kuka, ni kaina jarumta na nuna ina mai ƙara jin tausayin Zaiyan, ƙarshe muka haɗa rukuni na sayi gida a Kano da kuma Yola na sa duk wasu matakan tsaro akan su Alhaji Mustapha, a nan ne na gano su suka sa wannan babbar motar ta kaɗe ka, to da suka samu labarin kana raye shi ne suka sa aka haukatar da kai ta yadda ba mai cewa sihiri aka yi ma.. Hakan ya sa na ci gaba da aikin da ka tsaya, duk zuwan da zan yi sai sun sa a kasheni amma ba sa sanin inda na sauka bare su cimma burinsu, wani zuwa da na yi ne na samu labarin an sace kanwar Jk na shiga bincike har na gano su Alhaji Mustapha ne ke sawa a sato musu 'yan mata a Jahohin Nigeria, Ƙarshe su fitar da su kasashen waje a mayar da su kasuwai, abin ya tayar da hankalin JK matuƙa na yi ta kwantar mata da hankali tare da mata alƙawarin nemo mata ƙanwarta, haka muka ci gaba da yin aiki a sirrince tare da amincewar Ogan su Zaiyan. Tun daga lokacin na daina ganin Zaiyan ko na zo Asibiti ba na samun shi, har sai da Allah ya haɗa ni da Princess muka ƙulla abokata daga ƙarshe na gabatar mata da soyayyata, ranar da na zo gidansu ta kira ni da suna Zaiyan abin sai ya ba ni mamaki, da na tuna ina neman mai wannan suna sai na matsa da sai kun nuna min shi. Ko da na shigo gaishe da su Mommy na kaɗu sosai da ganin ta sak mahaifiyata, hakan ya sa a sace nake kallon ta har na baro gidan, da kuka haɗa ni da Zaiyan na tabbatar shi ne sai naji sanyi da na ga ana kula da shi. Bayan na koma gida na samu Mai maibarta ina tambayarsa wai Mamma ba ta 'yan'uwa ne? Sai ya ce min tana da su hasali ma ita Mamma yan biyu ce akwai Hassanarta da kuma kanwarsu, nan ya sanar da ni Sunayen su. Sai na ce masa mai zai hana mu nemo "yan'uwan Mamma dan su san tana raye ba ta mutu ba, nan ya nuna min ɓacin ransa ya ce shi da Nigeria har abada ba ya ma so na sake yi masa maganar Nigeria ya dinga faɗa karshe ma ya ce kar na sake zuwa Nigeria in ba ta kama dole ba. Ganin haka sai na ba shi haƙuri na dawo na ci gaba da bincike har na tabbatar da Mommy ita ce Twins sister ɗin Mamma, sosai na yi farin ciki na kuma yi baƙin cikin mutuwar ƙanwarsu, dan na ƙara sa ido akan rayuwar Mom da su Abdul ya sa na turo musu Jk ta zauna a gidan duk wani abu da yake wakana tana sanar da ni, ita ta gano irin cutarwar da Umma ke yi wa Mom na ce ta sa ido a kan ta sosai, ko lokacin da ta kai sunana wajan malaminta akan a sa na fasa auren Princess na auri Khairat Jk ce ta lalata shirin, maganin da aka ba ta ta yi amfani da shi dan na ci abincin ta yi nasarar canja abicin da aka kawo min. Bayan na gama muka haɗu ta sanar da ni komai ta ba ni shawara da na fasa auren Princess na auri Iman na yi kamar asiri ya kamani amma na ce Iman nake so, haka ba dan na so ba na hakura da Princess dan na tseratar da ita daga cutar da za ayi mata na auri Iman, duk da haka ba ta bar Princess ba ta sa aka yi mata asirin da kowa ya tsane ta karshe kuma ta ce Zaiyan za ta aura ko an ƙi ko an so duk dan ta ga ta wulaƙanta, lokacin na yi tafiya wayar Jk ta samu matsala ba na samun wani labari game da gidan nan, sai bayan auren na san komai har guduwar da suka yi. Ƙarasa ba su labarin yadda suka sa aka karya sihirin ya yi, da yadda suka samu nasarar kwato ƙanwar Jk.."
Saboda tsananin farin ciki Abir sai da ta yi sumar wucin gadi har sai da Zaiyan ya dan shafe ta sannan ta dawo haiyacinta, ta É—aga baki za ta yi magana suka ji an yo sallama. Kowa kofar ya zuba wa ido in da suka hango Laraba tsaye ta sha ado cikin shigar doguwar rigar atamfa ta mayafi haÉ—i da jaka, saurin tashi Abir ta yi ta iso gaban ta baki na rawa ta ce "La..Laraba ke ce nake gani haka ko mai kama da ke ce?"
Murmushi Laraba ta yi ta kamo hannun Abir suka iso ta zauna tana kallon Suhal, shi ma murmushi ya yi mata tare da cewa "Barka da zuwa Jk Æ´ar amana, yau dai mun kammala aikinmu."
Ƴar dariya ta yi ta ce "Kuma fa haka ne, mai guri ya zo mai tabarma sai ya naɗe mun gaishe da Damisa." Ta faɗa tana kallon Zaiyan..
Abdul ya share hawayen da ya zubo masa ya dubi Abir ya ce "Baby ashe dai mu ma da rabon za mu ga dangin uwayenmu? Alhamdu Lillah dama ni tun da na haÉ—u da Zaiyan nake jin shi har raina ashe jinjina ne shi."
Salim da ya yi shuru yana kallon su ya nisa ya ce "Wai dama Yarima Larabar ce Jk?"
Gyada masa kai ya yi ya ce "Tabbas Laraba ita ce Jk wadda na turo gidan nan a matsayin Æ´ar aikin Mom."
Gabaɗaya suka kamu da farin ciki matuƙa amma Zaiyan bai ce komai ba, sai da Abir ta taɓa shi ya ɗago ya kalle ta yana haɗe rai ya ce "Ni fa har yanzu ina kokwanto a maganar ka, amma bari na nuna ma photon nawa iyayen ka gani." Ya faɗa yana fito da photon da ya dauka a cikin walit ɗin da ya gani a jakar nan, nuna masa ya yi Abdul ya yi saurin amsa yana kallon photon ya ƙara tabbatar da cewa su ɗin yan'uwa ne, Suhal ya ce "Tabbas wannan su ne iyayena kuma kaima naka, idan kana son tabbatarwa za mu iya tafiya har Niger su da kan su za su yarda kai ɗansu ne."
Haka suka ci gaba da tattaunawa sosai Abir ta kamu da murnar za ta ga Twins sister É—in Mom, suna tashi Abdul ya kira su Abba ya sanar da su komai, sun yi farin cikin jin Hussainar Mom na raye kuma Suhal da Zaiyan yaranta ne.. Ko da Grandma ta samu labari ta sha kukan farin ciki dan ta san yadda Mom ke yawan maganar Æ´ar'uwarta, ranar Abir da Abdul da Zaiyan ba wanda ya runtsa saboda tsabar farin ciki...
Kwanan su biyu suka tattara zuwa Niger in da jirgin su ya yi tashin safe karfe 7:30am. Ko da suka sauka Suhal ya yi wa Zaiyan rawani irin na buzaye ya rufe masa fuska yana ta murmushi yau zai yi wa iyayensa bazata, haka aka zo É—aukan su suka nufi masarauta. Suna sauka a part É—in Mamma suka yada zango in da Suhal ya bukaci Mai martaba da su Kilishi duk su zo part É—in Mamma, sun sha mamakin wannan kira na Suhal haka dai suka tafo dan ba dama su ce ba su zo part Mamma ba..
Sai da kowa ya zauna Mamma ta fito daga ɗaki ta sha ado tana zuba murmushi ta nufo su, zabura Abir ta yi tana kallon Mamma sak Mom take gani tana nufo in da take, Abdul ya yi saurin riƙe hannunta tare da girgiza mata kai. Sai da Mamma ta zauna ta dube su ta ce "Sannun ku da zuwa."
Salim ne kadai ya yi karfin halin amsa mata dan shi ma ya ruÉ—e, Suhal ya warware rawanin Zaiyan ya ce "Mamma da Papa shin kun san wannan fuskar?"
A tare suka kalle shi idanu waje Mamma ta ƙura masa idanu, kasa daurewa ta yi ta ce "Subhanallah! Wannan bawan Allah ina kallon shi na ji ya shiga raina, Yarima a ina ka samo mai kama da kai?"
Jakar ya janyo daga bayan Zaiyan ya aje a gaban su ya fito da wayoyin su har da photonsu, Mamma ta ruÉ—e sosai baki na rawa ta ce "A.. A. Ina ka samo wannan jakar da kuma photunan?"
Bai ba ta masa ba sai photon Inna Asabe ya ciro a aljihunsa ya nuna musu ya ce "Nasan ke da Papa Kun san wannan matar."
A tare suka amsa da "E.. E mun san ta."
"To wannan da kuke gani shi ne É—an da kuka haifa."
Da wani irin saurin Mamma ta zabura sai ga ta gaban Zaiyan, kallon juna suka yi ta fashe da kuka tana rungume shi.....
Maman Nusaiba ce
[6/20, 8:43 PM] Ummu Amjad: *A HAKA NAKE SON SHI*
Shafi na 55
Shafa bayansa take tana faÉ—in "Ashe da rabon zan sake saka ka a idanuna yarona? Idan mafarki nake don Allah ka da ku tayar da ni ina so na ci gaba da ganin sanyin idaniyata."
Shi ma Zaiyan kukan yake yana ƙara ƙanƙame mahaifiyarsa cikin tsananin so da ƙauna, a hankali ya ɗago daga jikinta suka kalli juna ya juyo ya kalli Abir da take kuka wiwi, janyo ta ya yi ta matso kusa da shi ya damƙa hannunta a na Mamma yana murmushi mai haɗe da hawaye, Mamma ta kalli Abir gabanta ya faɗi ta rufe idanuwanta ta sake buɗe su a kan ta. Ajiyar zuciya ta sauke ta kai hannu ta taɓa fuskar Abir tana kallon Suhal ta ce "Yarima wannan kamar ita ce ka taɓa nuna min wadda za ka aura Allah bai yi ba?"
Jinjina mata kai ya yi idanuwansa sun cika taf da hawaye ya gyara zama yana murmushi, Mamma idanuwanta akan Abir sosai ta ga kamannin Mom a fuskarta, Suhal ya kalli su Mai martaba ya ce "Papa wannan ita ce matar Zaiyan, ita ce wadda na so aura Allah bai nufa ba ashe ma za ta zama matar Yayana."