Sashe 68
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai wajan karfe goma aka shirya gagarumar walima a wani babban ɗakin taro da ke cikin masarautar, su Mom sun ga manyan mata hamshaƙai masu ji da izzar sarauta da kuɗi kowacce in ka gan ta sai ka rantse gasar kyau za ta je.. Bayan an tashi suka mata nasiha saboda gida za su dawo ai kuwa ta yi tsalle ta dire ta ce tare za su koma, da kyar da lallami aka samu ta kyale amma ta ce tafiya ba fashi babu wanda zai bar ta a wannan babbar masarautar da babu wanda ta sani, abin ya ishi su Mom Nabila ta kira Umma ta ba ta wayar ta rarrashe ta amma ta ce ita fa Wallahi ko ana muzuru ana shaho sai ta koma Nigeria ba mai barin ta a nan. Ƙarshe dai su Abba suka yi ta mata nasiha amma taƙi ji sai kuka take kamar ranta zai fita, dubara ta faɗo wa Umma ta sa aka kira Abir ta ce ta je ta mata magana ta ce sai ta dawo da su Ammi. Abir da sauri ta koma part ɗin su ta kira Mom Nabila ta ce a ba ta Iman, tana amsa ta fashe da kuka ta ce "Ni gaskiya Anty Baby ba zan zauna a nan ba zan bi su mu koma Nigeria, Wallahi ban san kowa ba ni dai ki ce wa Abba ya sa Yaya Suhal ya sakeni mu koma gida."
Dafe kai Abir ta yi saboda itama ba ta daÉ—e da gama kukan rashin masoyinta ba kanta ya mata nauyi sai sara mata yake, ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Ashe bakya sona Iman? Na dauka duk gidanmu ke ce wacce kika fi kowa so na ashe ba haka ba ne?"
Saurin tsayar da kukan Iman ta yi ta miƙe tsaye ta ce "Wallahi Anty ina son ki mana."
"To in dai har da gaske ki na so na me ya sa ba za ki Ƙaunaci wanda yake so na ba? Ki yi hakuri ki zauna da kin yi wata biyar ko shida zai kawo ki ganin gida. "
Fashewa da kuka ta yi har da dira ƙafa ta ce "Wata shida kuma Anty Baby? Ina lefin sati ɗaya ma." Ta faɗa tana zama kan kujera.
Dariyar yaƙe ta yi ta ce "Sati fa? To shi kenan zan masa magana da kin cika sati ya kawo ki ganin gida." Ta faɗa tana jinjina shirme irin na Iman. Wani sanyi Iman ta ji sai ta kyalkyace da dariya tana rufe fuska ta ce "To na yarda zan zauna."
Itama dariyar ganin ta shayo kan ta ta yi, nan suka yi sallama tana ƙara jadadda wa Abir daga sati fa ba za ta sake kwana a Niamey ba ta ce mata to sannan ta kashe wayar..
Riƙe baki Mom Yasira ta yi ta ce " 'Yan'uwa jini da hanta to mu za mu wuce." Rufe fuska ta yi tana dariya tana ɗaga musu hannu har suka fita daga palon, da sauri ta biyo su inda ta samu suna yi wa Mamma sallama suka wuce ita kuma ta shiga gaishe da Mamma, alama ta mata da ta zo ta zauna ba muso ta zauna a gefen Mamma suka kama hira ita da Ikilima...
_NIGERIA_
Tana aje wayar magani ta ɓalla ta sha ta fito palo ta zauna zaman jiran zuwan su Mom Yasira.. Sai La'asar sakaliya suka iso gida aka hau ba da labarin Iman da yadda ta birkice Abir nata murmushi, ko ba komai ta ji daɗi tun da Iman ta yarda ta zauna....
Bayan an yi biki da sati biyu Abir ta shirya ta tafi gidan Baba dan ganin Zaiyan. Kamar kullum a zaune ta same shi yana ta yin gidan ƙasa ya kwaɓa taɓo yana yaɓe ɗakunan da ya yi, ganin ita ce sai ya tsuke fuska ya ce "Na daina miki magana."
Lumshe idanu ta yi tana jin zafin zuciyarta na sauka, a hankali ta isa gaban ɗakunan ƙasar da ya yi ta aje handbag ɗinta ta ce "Ni ma zan yi wasan." Ta faɗa a shagaɓe tana turo baki kamar yadda ya yi..
Hannu ya kai ya yaɓa mata taɓon da ya gama kwaɓawa a kumatunta yana dariya, ɗayan kuncin ya kuma sa mata taɓon yana dariya tare da cewa "Wannan faudar za ta miki kyau Anty, cire ɗankwalin na miki wankin kai." Kafin ta yi magana tuni ya cire mata hular da ke kanta ya kwaso taɓon hannu bibiyu ya zuba mata a cikin lallausan gashinta da ya sha gyara baƙi siɗik sai sheƙi yake yi, sai da ya gama daddaɓa mata taɓon duk tana kallon shi kuma ta kasa tsayar da shi, miƙewa ya yi ya buɗe rigar shi zariyar wandonsa ya kunce ya zare zariyar ya ɗaura mata a kan yana murmushi. Ita dai Abir kamar an dasa ta haka ta yi kawai ji ta yi ba za ta iya ce masa komai ba, zama ya yi yana sake kwaɓa wani taɓon mai yawa, bayan ya kwaɓa ya dube ta da ta kafe shi da idanu sai ya ɓata rai ya ce "Kallon ki irin na Maman abokina ne sai na daure mata hannu ma in tana kallo na."
Murmushi kawai ta yi ya janyo kwanon da ya kwaɓa taɓon ya ce "Kawo ayi miki lalle irin na Inna ki yi kyau." Ya faɗa yana miƙa mata hannu tare da nuna mata ƙafarta.
Dariya ta yi kamar wacce aka yi wa wahayi ta miƙa masa ƙafarta da ta sha kunshi ja da baki na amarci, kama ƙafar ya yi har da gyara zama ya soma yi wa ƙafar wankan taɓo kamar yadda tsofaffi ke yi ya shirɓine mata ƙafar har ƙwafrin duk ya yayyaɓe su, ƙafar ɗaya ya kama ya mata irin na ɗayar har da huci yake irin na wanda ya daɗe a tsaye yana aiki. Bayan ya gama sai gani ta yi ya warci hannunta ya yaɓe shi duka, tashi ya yi zaune ya ɗaga kwanon taɓon ya ƙarasa kwarara mata a kai har da sa hannu ya goga a inda bai samu ba...
Kallon yadda ta yi wani iri kamar wata mai ciwon daji sai kawai ta fashe da dariya, shi ma dariyar ya yi yana zama a gaban ta ya ce "Anty ina son ki."
A wani kalar zabure ta kalle shi, duk da ta san ba wani abin mamaki ba ne jin Kalmar saboda ya saba faÉ—a mata, amma a wannan karon ji ta yi ta bambanta da sauran lokutan da yake sanar da ita yana son ta...
Baba da Inna ne suka fito suka gan su a haka ta kafe shi da kallo, dariya Inna ta yi ganin yadda aka mata wankan taɓo, shi ma kan shi Baba dariya ya yi hakan ya sa ta yi saurin kallon su, dariyar da suke mata ta sa ta ji kuka ya zo mata kawai ta ɓare baki ta fashe da kuka wiwi. A rude Zaiyan ya kalle ta yana ta cewa "Anty waye ya dake ki?"
Ganin taki ba shi amsa sai kawai shi ma ya zauna ya yi tashe-tashe ya shiga rero kuka, ai kuwa me su Baba za su yi in ba dariya ba Inna har da riƙe ciki....
_Maman Nusaiba ce_
[6/20, 8:43 PM] Ummu Amjad: ~A HAKA NAKE SON SHI~
*No editing*
Shafi na (33)
Tsayar da dariyar Inna ta yi ta nufo su ganin yadda suke kallon juna kowa sai kuka yake kamar wasu yaran goye, tana isowa Zaiyan ya kalle ta yana goge hawaye y ce "Inna kin gani ko Anty tana kuka, ko Baba ne ya ce zai sace ta irin na jiya?" Ya faɗa yana kallon Inna da take ƙoƙarin gumtse dariyarta.
Baba ne ya iso ya dubi Abir da zuwa yanzu ta daina kukan sai kallon su da take ya ce "Hauwa'u me ya faru kike kuka wai?"
Kallon jikinta ta yi ta dawo da kallon ta kan Zaiyan sai kawai ta sake rushewa da kuka jikinta ya yi sharkaf da zufa ga taɓon da ya yaɓe mata duk ta ji jikinta ya yi wani kalar, dariya Inna ta kuma yi tana cewa "Ke yanzu kuka ba ya miki wahala Abir? Yanzu Zaiyan ɗin n kike yi wa kuka sai ka ce kin samu wani nutsastse? To tashi ki je ki wanke jikin naki kar kayan jikin ki su lalace." Ta faɗa tana nuna mata famfon da ke can gefen su.
Girgiza kai Baba ya yi ya ce. "Æata jiki kuma na nawa? Ba ki ga har kanta ya wanke mata da taÉ“on ba? "
Sai lokacin Inna ta kalli kan da kyau ta ga shi ma an masa wankan, riƙe baki ta yi ta maka hannun Abir ta miƙar da ita tsaye, ita kuwa kallon Zaiyan ta yi da ya mike kamar an tsikare shi suka hada idanu ta harare shi tare da cewa "Mun ɓata da kai." Tana faɗin haka ta yi gaba zuwa bakin fomfon. Turo baki ya yi yana kifkifta idanu irin na yaron da ya yi lefi ya bi bayan su, Baba ya koma ciki dan dama leƙo Zaiyan n suka yi su ga ko yana inda yake. Sai da ta fara wanke hannuwanta da ƙafafu sannan ta sunkuya Inna ta janyo maisar da ake ba wa shukokin wajan ruwa ta jona ta dinga duba mata ruwan ita kuma tana wankewa, sosai ta jigata saboda ƙasar ta daddaɓe a can ƙasar kanta sai da Inna ta dinga tayata sannan ya wanko. Ta jiƙa kayanta sai hararar Zaiyan take da matso kusa da ita hannunsa duk taɓo ne haka ma kayan jikinsa sabbi ne kar amma ya lalata su da taɓo, gashin ta kama ta matse ruwan yana zubewa ta ɗago ta kalle shi yana ta juye-juye kamar mai yin training. Inna ta ce "To yanzu ki shiga ciki ki yi wanka dan wannan kayan naki sai dai ki fidda sun jiƙe." Ta faɗa tare da wucewa ciki ta bar su a nan tsaye ita da shi.