← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 120

Sashe 110

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Shi kan shi sai yanzu wannan dabarar ta zo kansa, tashin hankalin da yake cikin ya mantar da shi duk wata dabara, dan haka ya ja hannunta suka zagayo ta ƙofar get inda suka tarar da maigadi kwance cikin jini. Tsoro da firgici ya sa Husna ja da baya ya yi saurin janyo ta ya riƙe ta gam, cikin sanɗa suak nufi fita daga gidan sai Aisha ta tsaya jikinta na rawa ta ce "Maigida Inna Asabe na nan fa tun da sun shiga ciki ka yi sauri ka taso ta mu gudu."

A hanzarce ya nufi ɗakin maigadi inda ya samu Asabe ta maƙale a jikin gado, jin shigowa ya sa ta ɗauke numfashi cikin tashin hankali. Da sauri ya matso wajan gadon ya ce "Maza taso mu tafi Inna." Ya faɗa yana kallon ta da dan hasken fitilar da ke ɗakin..

Jin mai maganar yasa Asabe fitowa ta bi bayan shi suka fito, ganin mijinta cikin jini ya sa ta É—aura hannu a ka za ta kurma ihu Husna ta yi saurin rufe mata baki

"Karki kuskura ki yi kuka mai sauti za su ji mu su fito." Ba yadda ta iya ta hadiye kukan ta, tana kallon mijinta haka ta juya ta ƙaraso bakin ƙofar da nufin ta buɗe ƙofar suka ji an daka musu tsawa.

"Kai Alhaji!"

Hankali a tashe Alhaji ya yi saurin ɗamka hannun Husna a na Asabe ya ce "Maza ku fita kafin su iso." Ya faɗa tare ɗan tura su suka fita ya yi saurin juyowa ya danne ƙofar. Manyan garada su shida dauke da bindigu a hannayensu, dukkan su sun rufe fuskoki ba a ganin komai a fuskar sai iya idanu.

Zagaye shi suka yi wani ya É—aura wa Alhaji bindiga a ka ya ce "Kai ga ka mai wayo ko? Duk wayonka mun fika sanin kan tsiya Wallahi."

Alhaji dai bai ce da su komai ba ya yi shuru yana muzurai, É—aya daga cikin su ya ce "Ina matar taka take?"

Sai a sannan Alhaji ya iya magantuwa, "Ai ta yi tafiya ne?" Ya faɗa yana sunkuyar da kansa ƙasa cikin rashin sanin mafita..

"Mu za ka raina wa hankali? Muje ka fito mana da duk abin da yake cikin gidan nan." Wanda ya É—aura masa bindigar ya faÉ—a a fusace kamar zai kai masa duka.

Jiki na rawa ya miƙe suka saka shi a gaba har cikin ɗakinsa da yake aje duk wani abu da yake da muhimmanci, su kuma da kan su suka shiga birkice ɗakin inda suka fito da jikar kuɗi rafar 'yan dubu-dubu. Yana gani suka kwashe komai sannan suka ɗauko wani takardu suka ce sai ya sa hannu a ciki, shi kuma bai musu muso ba ya sa hannu da duka takardun. Bayan ya sa hannu suka dage lalle sai ya taso matarsa ta fito, ya ce da su ba ta dawo ba daga wajan biki, dalilin haka yabsa wani ya bugi kafadarsa da gindin bindiga. "Ka fito da ita ko kuma mu da kan mu mu fito da ita." Wanda ya dake shi ya faɗa yana huci.

Bai sake ce musu komai ba sai wani daga cikin ya zaburo tare da cewa, "Lokacin da muka nufo shi na ga kamar ya buɗe ƙofa, kai tabbas ita ya buɗe wa ƙofa ta gudu Oga."

A tare suka ce tabbas haka ne nan take suka yi masa harbi uku ko shurawa bai yi ba ya mutu a wajan, su kuma suka kasu biyu. Mutane uku suka fita nemo su Husna, uku suka shiga bincike gidan suna É—auke duk wani abu da suka san yana da daraja...

Husna da Asabe suna gudu inda suka bar layin gidan jini ya soma zuba a jikin Husna, Asabe ta rasa yadda za ta yi da ganin wannan tashin hankali suka samu gefen hanya suka tsaya. Ba ka jin komai sai kukan karnuka da kwari Asabe ta cire ɗankwalinta ta ɗaura wa Husna a a ƙasan marar tana faɗin, "ɗaure hajiya mu ɗan ƙarasa barin unguwar kar su zo su same mu a nan."

Runtse idanu Husna ta yi tana juya kanta saboda azabar ciwon da take ji, can kuma ciwon ya lafa suka ci gaba da tafiya inda Aisha ta daure ta yi ƙarfin hali ta soma gudun ceton rai jin ciwon ya lafa sosai..

Sun kusa fita daga Unguwar suka ji ƙarar tafiya ana bin bayan su, kafin su ankara har sun kusa cin musu sai sautin muryoyinsu suke ji suna faɗin, "Ga sawonsu nan ."

Hankalin Asabe ya tashi a daidai lokacin ciwon naƙuda gadan-gadan ya zo wa Husna ta durkushe Asabe ta yi saurin shiga kafadarta tana mata sannu cikin rada, ta lallaɓa suka bi gefen hanya jikin wata bishiya suka tsaya a nan. Cikin abin da bai fi minti shabiyar ba Husna ta fara nishi sai jin kukan jariri Asabe ta yi, hankalinta ya kuma tashi ta cire wa Husna hijabin dake jikinta ta rasa ya za ta yi da jaririn da ba ta san me aka haifo ba. Daukan jariri ta yi ta lulluɓe da hijabin har uwar dan ba ta da abin da za ta yanke cibiya ta rungume hawayen tausayin kansu na bin kuncinta.. Cikin jini Husna ta ɗaure ta miƙe tsaye suka ci gaba da tafiya duk da jiri na ɗaukan ta amma Asabe ta riƙe hannunta ɗaya gam tare da haɗa ta da jikinta.

'Yan fashin dake bin su suka ci gaba da haska sawon su har suka zo wajan da ta haihu, hakan yasa suka kuma bin sawon wanda jinin dake zuba jikin Husna ne yasa suke ganin inda suka nufi. Cikin 'yan mintuna suka cin musu tare da zagaye su. Kuka suke suna roƙon su su rabu da su amma suka nuna sam ba su san hakan ba, Husna ta ce ita har abada ba za ta sake dawowa garin ba su bar su su tafi cikin duniya. Ɗaya daga cikin su ya ce "Ba za ki ɓata mana aiki ba yadda aka ce mu kashe ku gabaɗaya to sai mun kashe ku, musamman ma ke." Ya nuna ta. Kafin su yi wani yunkuri suka buga musu dinkin bindiga a tsakiyar kai take dukkan su suka zube, yayin da Asabe ke ƙanƙame da jajriri dake cikin hijabi a rade a haka ta musu.

Waya suka kira ana É—agawa É—aya ya ce "Oga mun kamo su har mun aika su amma kuma matar nan ta haihu."

Daga cikin wayar aka soma magana cikin tsawa da ba da umarni.

"Kar ku yi min kuskure a aikin nan Indai abin da ta haifa da rai ku ɗauke shi ku kai cikin daji ku jefar, sannan ku ɗauko gawar matar tasa da ta maigadin ku kawo su gidan sai ku ƙarasa aikin." Yana gama faɗin haka suka ji an yanke kiran..

Ɗaukan Husna suka yi suka wuce, ita kuma Asabe suka taɓa suka ji ba ta motsi sai suka shiga duba gefen da suka dauke Husna ko za su ga jaririn amma ba su ga komai ba sai jakar da ta dauki, ganin ba su samu ba ɗaya daga cikin su ya ce "Kai yaron nan fa ya mutu sun jefar shi kawai mu wuce ita wannan mu bar ta a nan kawai."

Sai da alfijir ya keto sannan Asabe ta farfado daga sumar da da yi, saurin bude jaririn ta yi ta ga kamar ya rasu hankali a tashe ta lallaɓa ta tashi ta jakar Husna ta dinga tafiya. Sai da gari ya waye tantawarai Asabe na tafiya ta rasa in za ta shiga da jaririn nan, can gaba ta hango Asibiti ai kuwa ta nufi Asibiti da sauri har tana haɗawa sa gudu.. Ko da ta isa miƙa musu jaririn ta yi suka amshe shi aka shiga da shi ɗakin taimako, sun jima sannan suka fito suka ce bukaci ta faɗa musu jaririn waye? Har za ta sanar da su abin da ya faru sai kawai ta ce " 'yata ce ta haife shi kuma ta rasu, to ba ni da kowa daga ni sai Yayanta shi ya zauna tare da ita ni kuma na garzayo na kawo muku jaririn ku duba min shi ko shi ma ya mutu."
Chapter 110 · 0% Book details