Sashe 12
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lokacin Dattijo ya fito daga Masallaci yana kan hanyarsa ta koma wa gida ya ji wayarsa na ringing, da sauri ya ciro daga aljihun wandonsa sai ya ga sabuwar lamba ce dan haka yaƙi ɗagawa saboda labaran da yaransa ke faɗa masa, cewa ana kiran mutum da sabuwar number da ya ɗaga za a zuke masa jini, wannan dalilin yasa Dattijo ya ƙi ɗauka har ta katse. Bayan ta katse ya girgiza kai ya ce "Kai gara dai na ɗaga yaran nan wani lokacin ƙarya suke faɗa."
Yana shirin kiran number ya ga kira ya kuma shigowa ya yi saurin É—auka tare da karawa a kunne ya ce "Assalam alaikum."
Abir da ke kan gado ta yi lufai kamar ba ta da lakka a jiki ta ji saukar muryar Dattijo a majiyarta, wani sanyi ya ziyarce ta ta ce "Wa alaikum salam. Baba barka da rana."
"Barka dai yarinya, da wa nake magana?"
Ɗan murmushi ta yi ta ce "Ni ce wadda ka taɓa ba ni wayarka watannin baya na kira Mamana." Nan dai ta shiga faɗa masa har lokacin da Abdul ya zo ya ɗauke ta...
Baba ya murmusa sannan ya ce "Yarinya ashe ke ce? Ai kullum Zaiyan na tambayar ina Anty, in dai gari ya waye da ya ganni zai ce min "Anty ta kawo min abinci?" Sai na ce masa "Za ta dawo an jima."
Ba ta san lokacin da ta tashi zaune ba, wani irin daɗi ta ji ya ziyarce ta tana kuma yin mamakin yadda bai manta da ita ba duk da ba hankali gare shi ba, ƴar dariya ta yi ta ce "Ma sha Allah. Kenan Baba sunansa Zaiyan? Ai na sha tambayar sunan shi amma sai dai ya maimaita min abin da na tambaye shi, sunansa mai daɗi to yanzu ina yake?" Ta ƙarashe maganar tana yin baya ta jingina da jikin gado, ji ta yi kuzarinta ya soma dawowa.
Kamar Baba na ganin ta ya riƙe baki cike da mamaki ya ce "Wai dama kuna haɗuwa da shi ne bayan hakan ta faru?"
"Kwarai ma kuwa Baba, sau uku na gan shi kuma har ya min magana." Labarin komai ta faɗa masa tana jin ranta wasai, shi kuma Baba ya cika da mamaki marar musaltuwa har ya kasa ɓoye mamakin ya ce "Yarinya to ni dai a iya sanina da Zaiyan bai taɓa barin Unguwar nan ba, tun yana ɗan ƙarami yake a nan kuma ga shi kina maganar har a ƙofar Asibiti kika gan shi."
Ita ma riƙe bakin ta yi jin amsar da ya ba ta, to in ba shi ba take gani waye take gani? Ko kuwa dai Baba bai sani ba Zaiyan ke tafiya yawon sa har ya dawo bai san ya je ba? Girgiza kai ta yi ta ce "Baba Wallahi da gaske shi na gani, har fa rannan magana muka yi da shi a bakin Asibiti, yanzu yana nan a Unguwar taku?"
Ajiyar zuciya Baba ya sauke ya ce "E yanzu haka ma da zan tafi Sallah sai da na haɗu da shi a ƙofar gidana na kawo masa abinci, na ga ma duk ya rame sosai ko ba shi da lafiya ne ƙila."
Da sauri buɗe lumsassun idanuwanta wanda suka yi kama da na masu jin bacci, ƙara gyara zama ta yi sannan ta ce "Baba don Allah wata alfarma nake nema a wajan ka in zan samu."
"To Æ´ar nan ina jin ki."
"A a ba yanzu ba zan faÉ—a ma zan zo Unguwar taku zuwa gobe sai mu yi magana yadda za ka fahimce ni."
"To shi kenan sai kin zo É—in." Godiya ta masa sannan suka yi Sallama.
Bayan ta aje wayar ta shiga tunani, gabaɗaya abubuwa sun cunkushe mata duk ta rasa mafita. Numfashi ta fesar tare da sake ɗaukan wayar ta danna wa Abdul kira, sai da ta gama ringing ta katse bai ɗauka ba ta turo baki gaba, ba ta yi fushi ba ta sake kiran shi. Sai da ta kusa katsewa sannan ta yi an ɗauka sai kawai ta ɓare baki ta shiga rera masa kuka..
Shi kuwa dafe kai ya yi yana jinjina rigima irin ta Babyn nasa, ita kuka ba ya mata wahala daga kira sai kuka kuma? Ajiyar zuciya ya sauke tare da yin taku biyu ya zauna akan kujera ya jingina kansa ya lumshe idanunsa, so yake ya rarrashe ta amma bakinsa ya masa nauyi sautin kukan ta na ƙara rikita masa tunani ji yake kamar ana sukar shi in ta tana kukan , buɗe lulu eyes ɗinsa ya yi wanda suke cike da matuƙar gajiya ya ce "My Baby cries enough, faɗa min what happen kike yin rigima?" Ya yi magana yana sa hannu cikin sumar ķansa yana yamutsa ta..
Kamar tana gaban shi ta turo baki tare da kara lafewa akan gadon, cikin Shagwaɓar da ta zame mata jiki ta ce "Yaya wai ba ka dawo daga aikin ba ne? In ce dai ka ce yau hutu kake amma shi ne ka tafi Office." Ta yi maganar tana ƙara narkar da murya.
Lumshe idanu ya yi yana sauraron daddadar muryarta har ta kai aya a maganarta, dogon numfashi ya ja tare fesar da iskar cikin bakinsa ya ce "Baby Wallahi kin cika neman rigima, ke ba ki na zauna lafiya sai kin tasa ni a gaba kina min rigima?"
Cuno baki gaba ta yi ta janyo ƴar Teddynta ta rungume ba ta ce masa komai, sai da ya gaji da riƙe wayar sannan ya ɗauke hannun jakar computer shi da ke kan kafaɗarsa ya ce "Yanzun nan na dawo gida ko zama ban yi ba lokacin da kika kira ni, amma Kin san me?" Ya tambaye ta.
Girgiza kai ta yi tare da buÉ—e idanunta ta ce "A a Yaya sai ka faÉ—a."
Wani irin kayataccan murmishi ya yi, sannan ya ce "Ki ce Mommy ta haɗa miki abinci sai ki kawo min part ɗina mu ci abincin tare." Ya faɗa yana tashi daga kan kujerar ya soma ɓalle maɓallin rigarsa.
Murguɗa baki ta yo ta harari wayar ta ɗago da ƙyar ta runkuya ta miƙe daga kan gadon ta ce "To Yaya bari na kai maka dama ni ɗin ma ba ni lafiya in na zo sai ka sa a kawo min magani."
"Subhanallahi! Me ke damun ki Baby?" Ya faÉ—a a ruÉ—e. .
Sai ta zo kawai ta ce masa ta kashe kiran, cikin kuzarin da ta ji ya zo mata ta nufi freezer ta É—auko ruwa mai sanyi ta sha sannan ta canja kayan jikinta ta sako riga da wando jins, sosai kayan ya mata kyau ta É—aura É—an kwali sannan ta fito daga É—akin.
A ruɗe ta ƙaraso palon ganin Mommy zaune tana share hawaye, cikin damuwa ta ce "Mom me ya faru?"
Saurin goge hawayen Mommy ta yi sannan ta kirkiro murmishin yaƙe ta ce "Ba komai Mamana kawai dai kaina ne ke ciwo shi ya sa idanuna suke cika da hawaye." Ta faɗa tana gyara zaman ta. Ba ta gamsu ba da bayanin nata duk da tasan in Mommyn na ciwon kai idanuwanta za su yi ta hawaye, amma ganin yadda yanayin ta yake yasa sam ta kasa kwantar da hankalinta, durƙusawa ta yi ta ce "Mommy ni nasan a kan halin da muke ciki ne kike wannan kukan, ki yi haƙuri in sha Allah Abie zai dawo garemu." Ta ƙarashe maganar ita ma tana kuka. Janyo ta Mommy ta yi ta rungume ta zuciyarta na ƙara bugawa, tausayin ƴarta ta ya cika mata zuciya da gangar jiki, tana son faɗa mata dalilin kukan amma ba ta son hankalinta ya tashi gara ita ta ji da damuwar har komai ya yi daidai. Goge hawaye ta yi ta ce "Mamana tashi ki kira min Yayanki a part ɗinsu. Miƙe wa ta yi daga jikin Mommy ta wuce zuwa part ɗin Umma. Da Sallama ta shiga palon inda ta tarar da Yasmin da Fatima da Khairat da Iman tare da Umma, murmushi ta yi ganin 'yan'uwan nata zaune waje ɗaya gwanin birgewa ta iso inda suke ta durƙusa ta ce "Umma ina yini? Ya gida?"
Wani irin kallo Umma ta jefe ta da shi sannan ta ce "Lafiya." A takaice, abin da duk duniya Abir ta tsana ta gaishe ka amma ka amsa mata da lafiya, gani take kamar ma tambayar ta kake ba amsa gaisuwar ba, hakan yasa ta sunkuyar da kai ta ce "Yayana nake nema ko yana ciki." Ta faÉ—a duk da tasan yana cikin.
Yasmin da Fatima da suke bin da kallon tsana suka ja tsaki, Fatima ta ce "To me za ki ba shi da kike neman shi?" Ta faɗa cikin nuna tsanar da take mata ƙarara a kan fuskarta.
"Tsuwww! Rabu da uwar nacin jaraba mana, in ban da maita har ɗakin nasa ma sai kin biyo shi kamar wata uwarsa? To baya nan gulmanmiya uwar kissa da kisisina." Yasmin ta faɗa cikin ƙasa da murya dan kar Abdul ya jiyo tashin muryarta. Umma ta saki murmushi ganin hawaye kwance bisa fuskarta Abir abin ya faranta mata rai, ta rasa ma wani kalar asirce yaron Mommy ta yi da ko abinci ta yi baya ci sai na Mommy, hakan yasa ta kuma yin kwafa ta dungure mata kai tare da cewa "Shin ke da uwarki aka haifa wa Abdul ne? Wallahi duk bokon da ya muku aiki a kan yaron nan yake wannan rawar jikin a kanki sai na ga bayan ku gabaɗaya." Ta faɗa a fusace.
Iman da ta yi kicin-kicin da fuska kamar ta sa kuka ganin yadda ake wulakanta Abir ta ce "Haba Umma wannan wani irin cin fuska ne haka kuke mata? Sai ka ce ba jininku É—aya da ita ba? To Wallahi sai na faÉ—a wa Yaya Abdul ya muku dukan mutuwa mugaye kawai. "