← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 120

Sashe 29

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri ya ɗago idanunsa ya faɗa cikin nata, kallan kallo suke ita da shi har ba ta san ba lokacin da Baba da Inna suka ba su waje, har sai ta ta janye nata idanun sannan ta ankara ba sa palon. Shi kuma saƙare ya yi yana kallon ta sai da ta janye idanunta sannan ya yi firgigit ya taɓa fuskarsa. Sake kallon ta ya yi ya ga tana masa murmushi sai ya shagwaɓe fuska yana tattaba 'yan yatsun hannunsa cikin murya irin ta taɓararrun yara ya ce "Umm Antyyy!" Ya ja sunan yana mai juya fararen idanunsa a kanta. Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Na'am Zain."

Matsowa ya yi kusa da ita ya kama hannunta ɗaya yana faɗin "To ina abincin?" Ya faɗa yana langaɓar da kai..

Murmushi ta yi ta buɗe ledar da ta kawo ta fito da chocolate babba ta miƙa masa tare da cewa "To ga shi na kawo ma sai ka ci ko."

Saurin amshewa ya yi ya sa a baki yana gatsawa bai buɗe ba, hannu ta kai bakinsa ta ce "Ha." Ta buɗe nata bakin, ganin haka yasa shi ma ya yi yadda ta yi ta janyo chocolate ɗin duk ya jiƙa ta da yawun bakinsa, hannu ta sa ta buɗe masa ta zare ta a gidan ta miƙa masa ya amsa ya sa baki...

Kallon shi take zuciyarta na ƙara tausaya masa matuƙa, murmushi ta yi tana shirin ɗauke kai ta ji abu a kusan bakinta, da sauri ta kawar da kanta, shi kuwa ganin haka sai ya ɓata fuska ya miƙe tsaye ya ce "Ni ba sarki ba ne Anty sai ki hana na ba ki kema ki ci?"

Ya tambaye ta yana aiko mata da sakon harara.

Ɗan murmushi ta yi ta miƙe tsaye ta ce "E kai Sarki ne mana Zain, kar ka yi fushi zo ka bani zan ci."

Miƙe baki ya yi yana faɗin "Na ma fasa ba ki zan cinye abuna." Ya faɗa yana juyowa ya nuna mata tare da kai wa bakinsa. Saurin amshe wa ta yi tana dariya ta ce "Allah sai ka bani marowaci, ni fa na kawo ma kò ba ka sani ba?"

Shi ma da sauri ya miƙa hannu dan ya amsa amma ta yi saurin jefa wa a baki tana dariya, ganin tana masa dariya shi ma sai ya shiga yin dariya yana matsowa kusa da ita, da sauri ta matsa ai kuwa suka dinga zagaya bayan kujeru suna ta dariya. Sai da ta gaji sannan ta soma ƙoƙarin tsayawa shi kuma ya yi saurin ɗamko hannunta yana dariya ya ce "Yawwa na kamo ki."

Murmushi ta yi ta zauna a kan kujera hannunta a cikin nasa ya zauna. Haka ya dinga mata shirme tana biye masa, har kayan da ta kawo masa ta kira Baba ya kai shi É—aki ya canza masa suka fito. Wani irin kyau ta ga ya mata shi kuma sai wani shafa kayan yake yana faÉ—in "Anty kin ga wannan kayan nawa kuwa?"

Ƴar dariya ta yi ta janyo wayarta ta ce "To zo mu yi selfi." Ɓata fuska ya yi yana maƙale kafaɗa Baba ya ce "Haba Zaiyan ita fa ta kawo maka kayan ka je ta ma photo sai ka yi kyau."

Jin abin da Baba ya faÉ—a sai ya isa gareta ya zauna a daf ta ita yana waro idanunsa ganin shi a cikin camera ya ce "Anty wannan abokina ne ya zo?"

E kawai ta ce masa dan kar ta tsaya yi masa bayani ya ce ya fasa yi, saita su ta yi ta ɗauka, ganin haka yasa ya kwanto da kanshi kan kafaɗarta yana murmishin da ya baiyanar da haƙoransa ta ɗauke su, abu kamar wasa in ta ɗauka sai ya ce mata.

"Yawwa abokina ashe dai ka gane ni." Sai ya nuna photonshi da ta ɗauka. Ita kuwa murmushi kawai take zubawa,yana surutun bai san ba lokacin da ta ɗauke shi video yana turo baki tare da langaɓar da kai gefe yana faɗin shi ma yunwa yake ji, ita kuma tana masa dariya tana cewa ba wata yunwar da yake ji sai ya ɓata fuska kamar zai mata kuka ya ruƙo hannunta ya ce to ta kaishi faɗarsa, dariya kawai take ta ce ma za ta kaishi da sun gama. Sai ya yi dariya ya ce mata "Anty kema kina Uwaye?" E take ce masa har ta gaji ta daina ba shi amsa.

Sai kusan Magariba ta shirya tafiya gida ta kira Ali ta ce ya zo ya ɗauke ya, ai kuwa tana tashi ya ce sai ya bi ta aka kama fama da shi har da kuka ya ƙulla kamar wani ƙaramin yaro yana riƙe hijabinta, ji ta yi kamar ta tafi da shi amma ba yadda ta iya tun da magani ake masa, sai da ta masa wayo ta ba shi ledar kayan ta ce ya kai daki ya dawo su tafi ya ce to, yana shiga Baba ya shiga ya rufo su ta yi saurin fita tana goge hawayen suke kwaranya bisa kumatunta, da ƙyar ta iya tsayar da kuka dan kar su tambaye ta ba'asin kukan ta iso bakin motar ta shiga suka tafi gida...

*NIGER*

Sarauniya Bilkisu tun da Yarima Suhal ya ce ba zai yarda a aura masa Fauziya ba ta kasa zaune ta kasa tsaye, ko da ta dawo ba ta cewa Fauziya komai ba duk da tambayar ta da take yi, sai bayan kwana biyu Fauziya ta kuma samun Sarauniya Bilkisu a palo tana kuka ta zauna tare da dubar ta ta ce "Anty wai ba za ki faÉ—a min abin da kuka tattauna da Maimartaba ya kira ku ba?"

Ajiyar zuciya ta sauke tana kallon Ƙanwarta ta cikin jin haushin Yarima Suhal ta muskuta, kallon Hadimarta ta yi da ke matsa mata ƙafa ta mata alama da ta basu waje, da sauri ta miƙa ta fita fuskarta ɗauke da damuwa..

"Fauziya ki yi shuru mana, kin san dai bana son ganin kukanki."

Saurin tarar numfashinta ta yi ta ce "To in ba kya son ganin kukana ki faÉ—a min maganar da aka yi mana."

Nisawa ta yi tana kallon ta, tabbas sai yau ta ƙara tabbatarwa Fauziya na mutuwar son Yarima, a sanyaye ta ce "Ki yi haƙuri Yarima ya ce ba zai aure ki ba wai ba ki masa a matar aure, shi ya sa nake ce miki ki dinga nuna ke salihar mace ce dan ki samu shiga a wajan shi amma firr ke kin kafe ba za ki nuna hakan ba." Ta faɗa tana jan tsaki.

Wani irin zabura ta yi cikin tashin hankali ta dafe ƙirjinta da ke mata wani irin zafin azaba, tuni ta gigice ta kalli Sarauniya Bilkisu ta ce "Na shiga uku! Yanzu Anty ni ce Yarima zai ce wai ban masa ba? Me na rasa na 'ya mace? Duk abin da wani ɗa namiji zai kalle a jikin mace na jan hankali wanne ne bani da shi Anty? "Ta faɗa tare da fashewa da kuka mai tsuma zuciya. A fusace Sarauniya Bilkisu ta ce "Ke kuwa kika rasa tun da ba ki iya takunki ba, a ko'ina sai kin nuna halinki da nuna ke mai izza ce, taya kike tunanin Yarima zai so ki a haka? Yarima ba ya son a wulaƙanta ɗan'adam a gaban shi, baya son mace mai rawar kai, ba ya son rashin kunya, ba ya son duk wanda ba ya ƙaunar mahaifiyarsa da mahaifinsa, ba ya son duk wanda yake cin mutumcin na ƙasa da shi. To ki faɗa min ke a cikin halin nan wanne ne ba kya yi?" Ta faɗa tana ɗaukan apple da ke gaban ta ta kai baki ta gutsira tana jin wani irin ɓakin cikin soyayyar da Ƙanwarta ke nuna wa ɗan kishiyarta, in ban da ma ita shashasha ce taya ma har za ta faɗa soyayya da jinin kishiyar ta? Matar da tafi tsana a duniya take som ganin ranar barin ta masarauta gabaɗaya, amma ga shi Fauziya ta maƙalewa Yarima mai mugun taurin kan tsiya da nuna shi jinin sarauta ne. Allah Allah take kar labarin rashin ɗa'ar da Fauziya ke aikatawa kar ya je kunnen Yarima Suhal..

Shuru Fauziya ta yi ba ta ce komai ba ta miƙe tsaye ta ɗauki wayarta, sai da ta je bakin ƙofa ta ce "Zan je wajan malamina Wallahi ko da tsiya-tsiya Yarima sai ya zama mallakina ni kaɗai, kuma in maganar na masa ladabi ne zan ƙoƙarta yin hakan dan ya ga na canza. Amma Wallahi ko yana so ko baya so sai ya aureni dan ni kaɗai Uwarsa Fulani haifawa ba dan kowacce mace ba." Tana gama faɗin haka ta buɗe ƙofar ta fita tare da bugo ƙofar ji kake garamm!

Kwafa Sarauniya Bilkisu ta yi ta ringesa ta ce "Yarinya kenan, ni na fiki sanin ta kan duniya zan nuna miki abin da babba ya hango, yaro ko ya hau kan dutse ba zai hango ba! Da kike maganar Wallahi sai na yi abin da ya fi na baya."

Sosai Yarima Suhal ya kasa sukoni saboda Papa ya ce dole sai ya auri Fauziya, sai da ya samu Mamma ya dinga mata kuka yana faÉ—in "Wallahi Mamma in kika bari aka aura min Fauziya sai na bar muku masarautar nan gabaÉ—aya kowa ma ya huta, saboda Allah ina ni ina wata Fauziya yarinyar da na sha ganin ta a hotel ita da samarin ta. Ni ina son na auri mace mai hankali da nutsuwa wadda za ta kula min da ke ta so ki kamar yadda take son mahaifiyarta, ita kuwa wannan ballagazar ko gaishe da ke ba ta yi bare ma ta girmama ki."
Chapter 29 · 0% Book details