← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 120

Sashe 44

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna fitowa ya yi saurin ɗauko wani kyalle ya rufe fuskarsa ita ma ɗankwalin da ke kanta ya janyo ya rufe mata fuska suka yo wajan motar. Kiciɓus suka yi da Alhaji har yana gogar Sajida, a fusace Suhal ya juyo ya cikin kakkausar murya wadda bai san yana da ita ba ya ce "Malam ya kana tafiya kana kaɗar mutane ba ka gani ne? Ko makaho ne kai?"

Ɗago kai Alhaji ya yi yana kallon Suhal da yake shafa mata inda ya goge ta sai huci yake, zaro idanu Alhaji ya yi ganin Sajida jiki na rawa ya ce "Sweet Girl! Ina kika shiga tun ɗazu nake neman ki hankalina ya tashi?" Ya yi maganar yana son taɓa ta.

A zabure Suhal ya make masa hannu ya ce "Are you mad? Matar tawa za ka taɓa har kake cewa wai sweet girl?"

Saurin janye hannunsa ya yi yana ƙifƙifta idanu, ko dai idanuwansa ba daidai suke gano masa ba? Kamar ita yake gani fa ga kayan nan irin nata, Numfashi ya sauke ya ce "Am sorry yaro, na ɗauka 'yata ce da na kawo Asibiti ta fito ashe ba ita ba ce kayan ne iri ɗaya." Wani irin dogon tsaki ya ja ya wuce ya saka ta a mota shi ma ya shiga ya rufo glas ɗin motar ya cire kyallan yana mayar da numfashi.. Ƙiƙam Alhaji ya yi yana bin motar da kallo wadda yake mata ganin kamar ta Abdul ce, dafe kai ya yi jin kira na shigowa wayarsa ya ja tsaki ya tsaya kamar wani yake jira..

Abdul da Abir suna isa Office ɗin babban likitan suka yi nocking ya ba su izinin shigowa, a nutse Abdul ya murɗa ƙofar suka sayo kai ciki bakunansu ɗauke da sallama. Ɗago da kai ya yi yana duban su, ganin Abdul ne ya sa shi sakin fuska yana musu barka da zuwa suka amsa tare da zama. Yadda ya riƙe mata hannu sai ta ji ba za ta iya zama ba sai ta tsaya a tsaye ganin Doctor ɗin yana kallon Zaiyan, haɗe rai ta yi tana turo baki gaba ta kalli Abdul ta ce "Yaya ka faɗa masa ni so nake mu tafi." Ta Yi maganar kamar za ta sa kuka saboda mugun haushin kallon da yake yi wa Zaiyan ɗin take ji.

Kallon ta ya yi yana yin murmushin gefen bakin, dawo da kallon shi ya yi ga Doctor dan kar ta tada masa rigima ya kasa rarrashin ta, ya san halin ta sarai na kafiya akan abin da take son yi ko za a mata dan haka ya nisa tare da sake ɗaure fuska kamar ba shi ba ne yanzu ya yi murmushi ya yi gyaran murya ya ce "Doctor ina so ka rubuta mana sallama, Baby ta ce ba ta son zaman shi a Asibitin." Ya ƙarashe maganar yana satar kallon ta ta gefen idanu..

Da mamaki Doctor ya kalli Abdul sai kuma ya aje biron da ke hannunsa ya ce "To amma na ga ai bai gama shan maganin da na rubuta masa? Ya kamata ka rabu da maganar ta ka bar shi aci gana da kula da shi har a dace." Ya faɗa yana kallon Abir da ta yi kicin-kicin da fuska ba alamar fara'a a game da ita. A fusace ta kalle shi cikin faɗa ta ce "Malam kawai ka ba mu sallama mu tafi gida, ina ce dai ni ce na amince a kawo shi? To na fasa yanzu zan yi ta masa addu'a ba zai sake zama a Asibitin nan ba." Tana gama faɗa ta kama hannun Zaiyan da ke riƙe da handbag ɗin ta yana jujjuya ta ta nufi hanyar fita.

" Babyyy!" Ya kira sunan ta a fusace, gabaɗaya yau duk ya ga ta canza masa kamar ba ita ba,. Tsayawa ta yi ba ta dawo ba ganin hakan Abdul ya soma ba wa Doctor haƙuri, "Am sorry Doctor."

Ce masa ya yi babu komai ya É—auki takarda ya rubuta musu sallama, amsa Abdul ya yi ya masa sallama suka bar office É—in, ai yanawa a ransa kamar ya zane ta..

Suna fitowa sun nufi motar suka haɗu da Alhaji Mustapha yana ƙoƙarin shiga, da sauri ya kalle su yana washe baki ya ce "A a, 'yata kune a Asibiti? Waye ba lafiya?" Ya faɗa idanuwansa a kan Zaiyan da yake riƙe da hannun Abir, wani irin daɗi ya ji ya lulluɓe shi ganin Zaiyan, ya ji duk komai zai zo masa cikin sauki ya gyara tsayuwar sa yana son jin abin da za su faɗa masa.

"Daddy mune É—azu ma na haÉ—u da Hafsy, mun zo ganin mara lafiyan mu ne shi ne ma aka sallame shi za mu tafi gida."

Da sauri ya ce "Ayya, wannan ashe shi ne majinyacin da Hafsat ke faɗa min? To Allah ya ba shi lafiya ni ma Hafsat ɗin ce ta kawo mai aikin gidan ta kwana tana ciwon ciki, shi ne na ce bari na zo na duba ta ni ma ɗa na kowa ne." Ya ƙarashe maganar yana kallon Abdul ganin yadda ya yi kamar bai san da shi ba, ya ce "Abdul ya aikin?"

Kawar da kai ya yi bai ce komai ba ya yi gaba ya ja hannun Abir da ba ta ji daɗin abin da ya yi wa Alhaji ba. Suna shiga motar suka samu Suhal yana ta aikin rarrashin Sajida na ta kuka tana ƙanƙame shi, ita ma a baya ta zauna ganin ya manne mata yaƙi yarda ya zauna ba tare da ita ba, suna shiga Abdul ya ja motar suka bar Asibitin..

Daret gidan da su Baba suke Abdul ya nufa, suna isa ya yi hon aka bude masa get ya shigo.

Baba na habar gidan yana jiran zuwan su saboda Abdul ya kira Baba kafin su iso ya sanar da shi za su zo..

Suhal sai da ya ja cap ɗin shi ta rufe masa idanu sannan ya tashi Sajida cikin lallami ya fito da ita, Baba ya musu jagora zuwa cikin gidan yana musu sannu da zuwa suka amsa Baba sai kiran Zaiyan yake amma fir ya ƙi ko kallon shi yana maƙale da Abir kamar wani yaron goge..

A palo suka samu Inna duk suka zauna, sai a lokacin Suhal ya janye cap É—in dan ya gaishe da su Baba, ya É—ago ya kalle su cikin nutsuwa ya ce "ina yinin ku Baba.?"

A ruÉ—e Baba ya zaro idanu ya nuna shi da yatsa ya ce....

_*Taku har kullum Maman Nusy ce*_
[6/20, 7:51 PM] Ummu Amjad: ~A HAKA NAKE SON SHI~

+966577675904

Shafi na 23

"Kai wane ne? Daga ina kake? Ya aka yi na ga kun kama da Zaiyan?" Ya jero masa tambayoyi a lokaci ɗaya yana dafe ƙirji, sosai ya shiga firgici ganin sak kamar copy ɗin fuskar Zaiyan ne aka yi aka daura a fuskar Suhal.. Murmushi Suhal ya yi ya cire cap ɗinsa ya sa hannu ya barbaza sumar kanshi da take a kwance luf-luf kamar gashin mace macen ma irin mai yalwar gashi, kallon Baba ya yi da har yanzu ya kasa zama in ya kalle shi sai ya juyo ya kalli Zaiyan da yake ta yi wa Abir ƙorafin ba ta masa wanka ba. Sajida da sai yanzu ta soma jin ciwon ya lafa ta kalli Suhal ta soma tambayar shi. "Suhal waye wancan ɗin?" Ta nuna Zaiyan da ya ɗago da kai a daidai lokacin da ta nuna shi, zaro idanu ta yi tana dafe ƙirji cikin kiɗima ta kuma yin magana, "Suhal ko dai da gaske ne na samu taɓin hankali?"

Ganin ta ruɗe ya ruƙo hannunta ɗaya ya ce "Ki nutse Sajida ba taɓin hankali kika samu ba, wannan wani mai kama da ni ne ba shi da lafiya na." Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tana kallon Zaiyan, sosai take jinjina lamarin Ubangiji buwayi gagara misali, ko a hanya ta ga Zaiyan tsaf za ta ce Suhal ɗin ta ne shi dan Abu kaɗan ne ya bambanta su..

Zama Baba ya yi yana jin sanyi a zuciyarshi, tabbas wannan lamarin ya saka masa kokwanto a zuciya, gyara zama ya yi ya dubi Abir ya ce "Ƴar nan waye wannan ɗin?"

Sunkuyar da kai ta yi tana murmushi sai kuma ta haɗe fuska tuna cewa Sajida matar Suhal ce, Abdul ya riƙe baki yana jinjina kai, ashe dai su Baby an soma girma da shirme. "Baba wannan sunan shi Suhal ɗan ƙasar Niger ne shi, kuma ɗa ga masarautar Niamey, ya zo neman auren Baby ne."

Faɗaɗa fara'a Baba ya yi yana kallon Abir da ta yi kicin-kicin da fuska ya ce "A ma sha Allah to Allah ya sanya alkhairi, yaro na tayaka murna dan wannan yarinya mutum ce har mutum, tana da hankali da nutsuwa ga girmama manya ga tausayi." Murmushi Suhal ya yi yana kallon Abir ya juyo ya kalli Sajida da ta saki baki tana kallon shi, kenan aure zai yi? Kuma wannan ita ce wadda zai aura? Wani irin kishi ne ta ji ya taso mata kanta ya sara ta yi saurin runtse idanu, hannu ta kai ta riƙe kan tana faɗin "Wash kaina zafi."

Inna ta miƙe tana cewa "Muje na ba ki magani, tare kuka zo da shi wannan yaron? Ke ƙanwarsa ce ?"

Ji ta yi maganar da Inna take mata kamar tana ƙara mata zafin zuciya ne, baya ta yi ta kwanta kanta a jikin kujerar ta ce "Ai Mama ba sai kin ba ni magani ba, an ba ni a Asibiti zan sha an jima."

Jin haka ya sa Inna ta koma ta zauna tana kallon ta, Abir da ta cika ta yi fam ta ce "Inna wannan É—in fa matar Ya Suhal ce."

Da sauri Inna ta kalle ta tana dafe goshi, sai yanzu ta gane inda maganar Sajida ta nufa na cewa kanta na ciwo kishi ne ya taso mata, kallon Suhal ta yi da yake danna waya ta ce "Kai ja'irin yaron nan me ya sa ka tafo da matarka wajan wata? Sai ta ga kamar ka yi haka ne dan ka ci zarafin ta."
Chapter 44 · 0% Book details