← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 120

Sashe 57

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ji ya yi an dafa shi, cak ya tsayar da kukan bai juyo ya kalli wanda ya dafa masa kafaɗa ba ya yi shuru. Bubbuga kafaɗarsa take yana ji amma ya yi ƙiƙam kamar wani gunki, sai da ya shirya dan kansa ya juyo. Cikin tsananin mamaki yake kallon ta hawaye na bin kuncinta tana girgiza masa kai ko alamar tsoro babu a tare da ita, wanda in a da ne iya kallo zai mata jikinta ya ɗauki rawa. Sunkuyar da kai ta yi, jin bai ce komai ba sai ta kamo hannayensa ta nufi bakin gado da shi. Kamar raƙumi da akala haka ya bi ta ta zaunar da shi a bakin gadon ita kuma ta zauna a kan carpet da ke mamale a ƙasa, sai da ta goge hawaye zuciyarta na dukan uku-uku ta ɗago ta zuba masa idanuwanta da suka yi ja saboda tsabar kukan da ta ci. Shi kuwa kawai kallon ta yake yana ta tunani, ashe Laraba za ta iya zama a gaban shi ba tare da tsoron komai ba? Gyaran muryar da ta yi ya sa shi ƙifta idanu yana mai ƙare mata kallo, ita kuwa ji ta yi duk kunya ta rufe ta amma ta daure ta kawar da duk wani tsoron da yake a zuciyarta dan ta sanyaya masa zuciya. Cikin dakiya ta soma masa magana a nutse kamar ba ita ba ce ta dinga kuka mai sauti har sai da Grandma ta rungume ta ta hana ta ƙuga kuka..

"Yaya Abdul ka yi haƙuri kullu nafsin za'iƙatul maut, duk wani mai rai da ka gani a duniya ko mutum ko aljan ko damba ko ƙwari to zai amsa kiran Allah babu wanda in kwanan sa ya ƙare a duniya za a ƙara masa na wani dole ya tafi inda ba a dawowa. Ka daure ka cije nasan raɗaɗi da ciwon da kake ji a zuciyarka, amma ka yi haƙuri Mom Addu'ar mu take buƙata ba wai kuka ba, tun da yau ta yi ban ga ka ci komai ba ka fita aiki har wannan lamarin ya afku. Don Allah Yaya Abdul. " Ta kamo hannayensa cikin rawar murya gaf take da fashewa da kuka, ta ja numfashi ta ci gaba.

"Ka daure ga tea nan na kawo ma ka sha ko ka ji kuzari a jikinka, ka da ka yi rauni sosai hakan zai sa in Anty Baby ta farfaɗo ka kasa ba ta ƙwarin gwiwar dangana."

Saƙare Abdul ya yi yana kallon ta cike da tsananin al'ajabi, ashe Laraba tana da hankali har haka? Ashe ta iya maganar kwantar da hankali in mutum na cikin tsananin damuwa?

Nisawa ya yi tare lumshe idanu yana sauke ajiyar zuciya bai ce da ita komai ba, ita kuwa Laraba har ta cire ran zai ce da ita komai dan har ta soma ƙoƙarin tashi ta ji ya ruƙo hannunta tare da buɗe idanuwansa a kan ta. Sosai ta tsorata da ganin yadda idanuwansa suka yi jajur kamar an watsa masa barkono, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce "Laraba na gode da shawarar da kika ba ni, ban taɓa tunanin kina da hangen nisa har haka ba." Ya faɗa yana sauke numfashi.

Murmushi ta yi mai haɗe da hawaye ta ɗago da kanta suka haɗa idanu, a nutse ta ce "Yaya Abdul kenan, in ban nutsu ba yanzu to sai yaushe? Shekara ta fa 23 kuma tun da na taso nake ganin ƙaddarori kala-kala a rayuwata. A gabana a kan cinyata ƴar da na haifa ta rasu, a gabana ƙanwata ta amsa kiran Allah, a gabana Babana ya gama min wasiyya ya rasu, a gabana mijina ya rasu. Yanzu wanda ya ga wannan abin da idanunsa in bai nutsu ba to sai yaushe zai nutsu?" Ta faɗa tana goge hawaye a karo na barkatai..

Tsura mata idanu ya yi cike da tsananin tausayin ta, hannu ya sa ya goge mata hawaye da suka kasa tsayuwa da ta goge za su zubo, girgiza mata kai ya yi ya ce "Kenan kina nufin ba ki da kowa sai mahaifiyarki?"

Girgiza kai ta yi ta ce "Ai Mamana ta rasu tun lokacin da ta haifi ƙanwata ta biyu, ba ni da kowa duk sun mutu sai ƙanwata ɗaya itama ban san inda take ba. Na sha zuwa har gidan redio na bayar da cigiyar ta amma har yanzu shuru babu ita babu dalilin ta, daga fita School ban sake saka ta a idanuna ba har yau. " Ta ƙarashe maganar tana fashewa da kuka tuna tilo ɗin gudan jinin ta ƙanwarta..

Tausayin ta ne ya ƙara mamaye Abdul ya ce "Ki yi haƙuri kin ji, tashi ki je bayan komai ya lafa zan neme ki mu yi magana.."

Kai ta jinjina masa ta tashi ta fita daga É—akin, shi kuma ya rafka tagumi yana tunanin Mom. Sai da ya ji kansa zai rabe biyu saboda tsananin ciwon da yake masa sannan ya É—auki tea É—in da ya soma hucewa ya masa shan ruwa...

Haka aka yi ta karɓar gaisuwa har aka yi kwana ukun Mom Abir ba ta farfaɗo ba, sosai hankalin su Abba ya tashi sai zirya suke Asibiti suna duba ta. Bayan an yi sadakar sati Grandma ta koma Asibitin ta ce Hafsat ta dawo gida itama ta huta, ba dan ta so ba ta dawo gida cikin damuwar ganin Aminiyarta a wannan yanayi na doguwar suma..

Sai da Mom ta cika kwana goma cif sannan Doctor Bashir ya ce su zo ƙarfe 10:am na safe za ta farka. Gabaɗaya duk suka hallara har Mommy Hafsat da matar Daddyn Aruf, ba su jima da zuwa ba aka ce ta farka amma suka hana kowa shiga suka ce za su fito da ita wajan su, saboda akwai wasu majinyatan a ɗakin wanda ba a son buɗe sauti a inda suke..

Wata nurse ta kama ta ta taimaka mata suka fito daga É—akin, ganin su duk a bakin kofar ta ji wani irin kuka ya zo mata kece da shi tana nufar Mommyn Hafsat da itama ta taro ta ta faÉ—a jikinta ta fashe da kuka. Kuka take tana faÉ—in "Ummi da gaske wai Mommyna ta tafi ta bar ni ni kaÉ—ai? Waiyo Allah ni Hauwa'u! shi kenan na zama marainiya gaba da baya babu uwa babu uba? Don Allah ku ce min Mom ta farfaÉ—o tana gida a zaune."

Rarrashin ta Ummin Hafsat ke yi tana ba ta haƙuri har ta tsagaita kukan, ɗago da ita ta yi ta share mata hawaye ta kama hannunta suka ƙaraso wajan su Abdul da duk ta gama karyar musu da zuciya wasu har sun soma kuka. Sallama aka ba su suka tafi gida kowa sai jimami yake, mutuwar Mom ta dawo musu sabuwa saboda sambatun da take har suka isa gida..

A harabar gidan suka samu Baba da Inna tare da Zaiyan suna tsaye Maigadi na faÉ—a masa su Abba sun tafi Asibiti sai ga su, sai da suka gama fitowa daga motar Abdul ya nufo su yana goge hawayen da suka zube masa, rusunawa y yi ya ce "Baba ku ne tafe?"

"Mu ne É—an nan ina ita Hauwa'u take?"

Ya É—aga baki zai yi magana ya ji Abir ta kuma fashewa da kuka ta nufo inda suke, Inna ta kamo hannunta cikin kwantar da murya ta soma mata nasiha.

"Ki yi haƙuri kin ji ƴar nan, babu abin da mahaifiyarki ke buƙata sai addu'ar ki a gare ta."

Tsagaita kukan ta yi ta É—ago ta kalli Baba ta ce "Baba Mommyna ta tafi ta bar ni dama ita ta rage min."

Cikin jimami Baba ya ce "Ki yi haƙuri kin ji Allah ya jiƙan ta da rahama?"

Sai a lokacin Zaiyan ya É—ago ya ga Abir na ta kuka, saurin isowa ya yi kusan ta ya kama hannunta ya fashe kuka shi ma yana kallon ta ya ce "Anty waye ya dake ki? Baba ne ko abokina na rama miki?"

Cak ta tsayar da kukan ta shiga sauke ajiyar zuciya, ta ce "Zain Mommyna ta tafi ta bar ni." Shuru ya yi yana kallon ta kamar mai karantar wani abu a maganar da ta yi, hannu ya sa ya goge mata hawayen ya kamo hannayenta ya ce "Anty kema Babanninki sun mutu?"

Gyada masa kai ta yi ya kalli Abdul ya ce "Baba ka dinga jin tsoron Allah ka daina sace Anty, yanzu ka ga saboda haka babannninta sun mutu."

Girgiza kai Abdul ya yi ya kamo hannunsa suka nufi ciki, suma sauran suka biyo bayan su. Yasmin ta riƙe baki tana dariya ta ce "Lalle ma ki ji fa Fatima, wai Yaya ne Baba." Itama dariyar suka duk nufi part ɗin su dan dama tuni su Umma sun wucewar su tun lokacin da Abir take cewa Baba ta rasa Mom.

A palo suka zauna suna ta ƙoƙarin ganin sun kwantar mata da hankali, Laraba ce ta iso ta rungume Abir suka fashe da kuka sai faɗi take "Laraba yanzu shi kenan Mom ta tafi ta bar ni?"

Haƙuri ta dinga ba ta har ta samu ta yi shuru, miƙar da ita ta yi suka wuce ɗakinta tana kara mata nasiha akan Haƙuri da juriya yayin da ka rasa wani abu mai mahimmanci a rayuwa, da haka ta mata dubara ta kawo mata tea tana kawar da kai ta lallaɓa ta har ta shanye, ta shiga toilet ta hada mata ruwan wanka ya dawo ta ce ta je ta yi wanka. Ƙin tashi ta yi sai picture ɗin Mom take kallo wanda yake maƙale a jikin bangon ɗakin, da ƙyar ta tashi Laraba ta raka ta ta tsaya a bakin ƙofar har sai da ta ga ta cire komai daga ita sai pant da karamar rigar ciki ta fito ta bar ɗakin...
Chapter 57 · 0% Book details