Sashe 62
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kowa ita ya zubawa idanu sosai ta ba su tausayi, Umma kuwa wani irin kiɗimewa ta yi jin ba Khairat ba ce aka aura wa Suhal Iman ce, duk da hakan dai wani sashe na zuciyarta cike yake fal da farin ciki tun da dai an fasa auren da Abir, tashi ta yi ta iso gaban Iman tana matso hawaye ta ce "Auta ki yi hakuri kin ji, ba wai su Abbanki sun yi hakan ba ne dan su sa rashin jituwa tsakanin ki da Abir ba, sun yi haka ne dan kar mutumcin su ya zube a idanun mutanen Unguwa da ma masarautar Niamey, ki ɗauki ƙaddara kar ki bijire wa iyayenki kin ji. Yanzu kawo ta a yayyafa mata ruwa ko ta farfaɗo sai asan abin yi. "
Goge hawaye ta yi cikin tsananin jin zafi ta ce "Wallahi Umma ni ba na son Yaya Suhal, kuma kin ga ko su Anty Khairat ba a musu aure ba amma ace ni ƙarama da ni za ku aurar shi ma auren na dole? Don Allah Umma ki ce su Daddy su ba wa Anty Baby Yaya Suhal shi ne zaɓin ta a kullum." Ta ƙarashe maganar tana sakin Abir Umma ta tallafo ta ta rungume.. Umma ji ta yi kamar ta rufe Iman da duka saboda cewar da ta yi ba ta son Suhal, abin da take ta mafarkin 'ya'yanta su samu aure a gidan masu kuɗi amma ita ta samu daga sama sai ta ce ba ta so ai ba ta isa ba ma. Hararar ta Umma ta yi ta ƙasan idanu za ta yi magana Mom Yasira ta iso da ruwa mai sanyi sosai ta gumtsa ta fesa mata a fuska.. Dogon numfashi ta ja ta soma motsawa duk suka zuba mata idanu, a hankali take buɗe idanuwanta har ta gama buɗe su akan fuskar Mom Yasira da ke gaban ta a durƙushe. Yunƙurawa ta yi ta tashi zaune Umma na taimaka mata ta goge hawayen da suka zubo mata ta ɗago kai ta kalli Iman, a sauri Iman ta matso ta kama hannayenta tana sakin sabon kuka ta ce "Wallahi Anty Baby ko kin mutu ba zan yarda na auri Suhal ba bare kina da rai da lafiya, ki faɗa musu ni ba zan yarda da wannan haɗin ba ba na son su haɗani gaba da ƴar'uwata." Ta faɗa tana ci gaba da kuka..
Sunkuyar da kai ta yi tana jin yadda zuciyarta ke mata wani irin azabtaccan ciwo mai mugun zafi, ji take dama mutuwa ta yi da wannan baƙar ranar da ta riska wai Suhal ɗin ta ne aka aurawa ƙanwarta Iman? Girgiza kai ta yi ta ɗago ta kalli Iman tare da kai hannu ta goge mata hawaye tana yin murmushin yaƙe wanda Hausawa ke cewa ya fi kuka ciwo! Da kyar ta iya saita nutsuwarta ta ɗago da haɓar Iman cikin wata kalar murya mai ban tausayi ta soma yi mata magana.
"Ƴar'uwata ki amshi zaɓin da su Abba suka miki dan shi ne ma fi alkhairi a gareki, ni na yi imani da Allah ne ya rubuto ba zan taɓa auran Suhal ba ke ce matarsa shi ya sa hakan ta faru damu. Kar na kuma jin kin ce ba kya son wanda yake son Antyn ki kin ji. " Ta karahe maganar wasu hawaye masu ɗumi suka silalo kan kuncinta, duk wanda ya ji maganar Abir ya san ƙarfin hali ne kawai take saboda yadda muryarta take rawa.
Nisawa ta yi sannan ta ci gaba..
"Kaf familyn mu ke kaɗai ce a mata nake jin zan ba da raina fansa na fanshi naki, indai har da gaske kin ɗaukeni a matsayin ƴar'uwa ta jini kuma wadda kike tsananin so da ƙauna, to ki karɓi Suhal a matsayin mijinki kar ki nuna ba ki son shi saboda yana matuƙar son yayarki. Nasan dole ki ji ba daɗi Iman, amma ki daure ki yi biyayya za ki ga ribar hakan a nan gaba kaɗan, ni ma Allah zai kawo min nawa mijin in sha Allah tashi kin ji amaryar Yaya Suhal muje na faɗa miki yadda za ki zauna da shi kanwata. " Ta faɗa tana ƙoƙarin miƙewa jiri na son ɗaukar ta..
Saurin dawo da ita Iman ta yi ta ce "Anty Baby k.."
ÆŠaure fuska ta yi ta gyara zama ta ce "Kar ki ce komai Iman in dai har na isa na faÉ—a ki É—auka."
Shuru ta yi ta haÉ—iye sauran maganar tana zubar da hawaye...
Wani irin tausayin ta ne ya mamaye Abba, shi kan shi bai so hakan ta faru fa amma ya zai yi da ikon Allah? Kallon ta ya yi ya ce "Mamana zo nan."
Tashi ta yi tsaye tana jin kanta na sara mata kamar zai rabe gida biyu ta daure ta taka ta isa gaban Abba ta zauna a kusan ƙafafuwansa, kanta ya shafa yana jinjina ƙarfin hali irin nasa, itama Iman kiran ta ya yi ta zo ta zauna a kusa a Abir ta ɗaura kanta a kafaɗarta tana jin ciwon wannan lamari..
Gyara zama ya yi ya dubi Grandma da tun da ta zo gurin ba ta ce komai ba sai tagumi da ta yi, a sanyaye ya ce "Inna ina me ba ki haƙuri akan wannan lamarin, nasan za ki ce mun yi gaban kan mu ba mu neme ki ba ki gafarce mu."
Sauke tagumin ta yi ta nisa sannan ta ce "To Sulaimanu ya za mu yi da lamarin Ubangiji? Amma ya aka yi hakan ta faru shi nake son ji?" Ta faÉ—a cikin alhini..
Kallon Daddy ABBA ya yi hakan ya sa ya soma yi musu bayani..
"Inna mu kan mu abin ya ɗaure mana kai, an zo ɗaurin aure sai muka fara ɗaura na Abdul mun zo ɗaura na Mamana har ana ƙoƙarin addu'a sai ɗaya daga cikin dogaran da suka zo ɗaurin aure ya kira ni gefe, hakan ya sa na ce su ɗan dakata muka fita gefe sai ga Suhal ya zo. Ganin yadda yake a hargitse sai abin ya ba ni mamaki nake tambayar su lafiya suka nemi su keɓe da ni? Nan Suhal ke ce min Wallahi shi kwata-kwata ba ya son a aura masa mamana ayi masa musaya, abin ya girgiza ni matuƙa na nemi naji dalilin da ya sa ya ce ba zai aure ta ba sai dai ayi masa musaya, ya ce min shi kawai dai ba ya son auran ta ne a ba shi wata a cikin 'yan matan gidan. Ganin haka ya sa na tsayar da su a nan na taso su Yaya muka zo har da wakilan shi muka shiga tambayar shi ya ce shi sam ba zai aure ta ba, ganin ana jan lokaci sai Yaya ya ce masa to ya zaba wacce yake so? Ya ce mana Iman yake so ita zai aura, mun girgiza sosai da jin hakan ganin Iman ƴar ƙarama ce duk da a addinance ta isa aure amma mun so ya ce ko Yasmin yake so tun da ita ce babba, mun so mu faɗa miki amma abin ya gagara dole muka koma aka ɗaura auren da Iman inda mutanen wajan suka sha mamakin wannan juyin, saboda duk garin nan ba wanda bai ga invitation ɗin auren Mamana ba a social media. "
Mom Yasira ta fusata ta ce "Wallahi Yaya ban ji daÉ—in wannan lamarin ba Allah ya gani na so mai sunan Inna ta auri Yarima saboda nutsuwar shi ga yana son ta, amma lokaci É—aya ya ce ba ya son anya Yaya?" Ta faÉ—a tana hura hanci..
Kallon banza Umma ta mata tana jin kamar ta zabga mata mari mai zafi. Nasiha sosai su ABBA suka yi wa Iman suna ƙara gargadin ta ko da wasa kar ta nuna masa ƙiyayya, ita kuma Abir suka yi ta ba ta haƙuri tare da kwantar mata da hankali suna nuna mata muhimmacin haƙuri akan abin da ka rasa, ta ce musu ai tuni ta haƙura ta bar wa Iman da haka dai Abba ya ce kowa ya tashi ya koma a ci gaba da hidima a gyara amarya an jima za su wuce Niger..
Hannun Iman Abir ta kama suka fita Abba ya bi su da kallon tausayi, yana jinjina irin ƙaunar da ke tsakanin su. Da sauri Umma ta biyo su Iman ganin za su shiga ɗakin Abir ta kira su suka waiwayo, ƙarasowa ta yi ta kalle su a fuska ta yi kamar za ta sa kuka, amma zuciyarta cike take fal da farin ciki marar musaltuwa.
"Abir don Allah kar ki sa damuwa a ranki kin ji, ki yi haƙuri dama can Suhal ba shi ba ne mijinki, naki mijin yana can a wani waje a gaba Allah zai haɗa ku, kuma kar ki ɗauki gaba da Iman duk da nasan ƙaunar da ke tsakanin ku ba ma za ki yi haka ba amma an ce zuciya ba ta ƙashi." Ta faɗa tana dafa ta.. Murmushi Abir ta yi ta ce " Ai Umma ko raina zan ba da akan Iman ballantana wani ɗa namiji, in sha Allah ba zan taɓa ganin baƙin Iman ba dan ta auri wanda nake so. "
Jinjina kai Umma ta yi ta ce "Haka ne 'yata, to kawo ita Iman É—in a shirya ta kin ji Abban ku ya ce an jima za a wuce da ita."
Kallon Iman ta yi tana Æ´ar dariya ta ce "Amarya ki je ayi miki wanka yau za mu kora ki gidanki."
Dukan wasa Iman ta kai mata tana ƙara jin son ƴar'uwatar tata ta bi Umma suka wuce part ɗin su...