Sashe 103
A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tashi big boy ya yi ya kwarara ihu tare da yin juyi ya kama kansa irin daɗi ya kai masa, ya ciro kuɗi daurin yan rafa ɗauri biyu ya ba su suka fita a ɗakin, kallon ta ya yi yana faɗin " Kin ga yanzu kin zama matata bari naje na shigo miki da lefenki ciki." Fita ya yi da sauri yana bude murya tare da sanar da yan palon ya yi aure, ai kuwa suka kwashi ihu aka sa sabon kiɗa tare da ƙure volume..
Ganin ya fita ta yi saurin rufo kofar ta murɗa mata key tare da yin ƙasa ta sulala ta fashe da kuka.
Yana zuwa ya ga ta rufe kofar ya yi ta bugun duniyar nan taƙi budewa, ya sa key ɗin da ke wajan shi amma yaƙi shiga saboda akwai wani a jiki, ita kuma tana jin yadda suka taru suna fadin "Amarya bude wa ango kofa zai shigo."
Da sun ce haka sai ta kara wa kukan ta ƙarfi, gabaɗaya hankalinta yana kan mijinta. Da suka gaji da magana sai suka koma suka ci gaba da shagalin bikin auren big boy..
Abu kamar wasa Abir ta yi kwana biyu a cikin wannan É—akin yunwa duk ta lakata ta, cikin kwana biyun da ta yi ta mugun ramewa saboda da ba da aikin yi sai kuka Sallah kawai take tsayar da ita daga kukan da take, ita kanta Sallar ta sanadin agogon da ke manne jikin É—akin ne take amfani da lokacin da yake nunawa ta yi Sallah.
A ɓangaren Big boy Kuwa yana nan bai tafi ba kullum sai ya kawo abinci ya aje mata a bakin kofar, wanda in zai sa a zubo sai ya barbaɗe shi da maganin bacci dan in ta ci burinsa ya cika. Sai dai in ya dawo sai ya tarar da abincin kamar yadda ya bar shi, hakan na baƙanta masa rai dan tsananin son da yake mata ya sa sai ya yi ta lallamin ta ta fito ba zai mata komai ba amma sai dai ya ji sautin kukan ta tana faɗin ba za ta bude masa ba. Wannan abu ya tsaya wa Big boy a rai ba ya so ta kamu da ciwon yunwa, haka dai yake zama a gidan idan ya ji shuru sai ya fita can baya akwai ruwan wanka irin nasu na yaran girman Turai...
Zaiyan gabaɗaya ya shiga damuwa duk yadda ya yi tunanin abin ba haka yake ba, kullum sai ya fita neman matarsa har gidan redio yake zuwa yana bayar da cigiyarta amma shuru kake ji wai shaho ya ci shirwa. Ita kuwa Tasakkawato har mamaki take in ya ce mata yaje waje kaza ya ba da cigiyar Abir, sai ta yi ta tambayarsa da ya je bai ɓata ba? Kullum haka take faɗa idan ya dawo, da ya gaji da tambayar sai ya yi murmushi ya ce "Mama kenan, to ai ni à cikin garin nan babu Unguwar da zan je na ɓata kuma ba zan tambayi kowa ba da kaina zan je, saboda a cikin garin na taso na girma da hankalina muka bar garin."
Baki bude take kallon shi har ba ta san lokacin da ya shige ɗaki ba, sai da ta ji ƙaran rufowar sannan ta ankare da ba ya nan. Ɗaki ta nufa zuciyarta ba daɗi ta yi sabo da Abir ba kaɗan ba, haka dai ta yi ta juyayi ta tura wa ƙawayenta photon Abir ta sanar da su an sace ta su taimaka mata su sa a nemo musu ita. Su kan su ƙawayen nata sun girgiza da jin wannan mummunan labarin, nan take suka mata Alƙawarin sa wa a binciko musu duk inda take ta musu godiya sosai ta sha kuka ta more sannan ta yi bacci..
Shi kuwa Zaiyan ba ya iya bacci, yau ma ya zauna yana ta tunanin yadda take ba shi kulawa tana tattalinsa kamar kwai, duk da ba ta san shi ko waye ba amma hakan bai sa da ya dawo cikin hankalinsa ta rage wani abu daga cikin kulawar da take ba shi, ko da lamarin nan ya faru a tsakanin su ba ta ji haushinsa ba iya fushinta na kwana ɗaya ne ta huce. Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon samar ɗakin abin duniya ya masa yawa, ya rasa ta ina zai fara, da neman mamansa zai fara? Ko da neman matarsa? Tashi ya yi tsaye sai kuma ya yi saurin dawowa ya zauna, computer Abir ya janyo ya nude code ya shiga Google, wasu abubuwa ya duba sai can sai ga photon wani ya bayyana sanye da ƙananan kaya fuskarsa rufe da wani kyalle, ƙura masa idanu ya yi da ɗan wasu daƙiƙu, murmushi ya saki ya fita ya shiga Facebook.. Wani suna ya rubuta *Bashow* sai ga account ɗin y fito masa ya shiga, number shi ya dauka ya fita daga Facebook ɗin ya danna masa kira. Sai da ta yi ringing ta gama bai ɗauka ba ya kuma kira, ta kusa katsewa ya ɗauka ya yo shuru bai ce komai ba, sai da wancan ya gaji da shurun ya ce "Hello."
Murmushi Zaiyan ya yi tare da faɗin "Bashowwwwww." Ya ja sunan yana sakin murmushi mai sauti duk da na yaƙe ne yake.
Daga cikin wayar Bashow ya kurma ihu murna yana faÉ—in "Abokina dama ka na nan a raye? Don Allah a ina kake?"
Gyara zama ya yi ya ce. "Ina Kano."
Bashow ya ce. "Da gaske? Yaushe za mu haÉ—u?"
Numfashi ya ja ya ce "Ka ga yanzu dai idan har kana da lokaci za mu iya haduwa yanzu tun da dare bai yi ba sosai karfe 10:00pm ce, wani abu ne ya taso shi ya sa na nemo ka dan ka kira sauran ka sanar da su dawowa ta cikin da'ira." Ya nisa sannan ya ɗaura da ba shi ɓatan Abir amma bai ce mata matarsa ba ce su taya shi neman ta.. Bashow ya jajan ta masa nan ya yi masa alƙawarin gobe su haɗu da safe sannan suka yi sallama...
Washe gari suka haɗu inda suka rungume juna cike da kewar juna, nan suka samu waje suka zauna suka tattauna sosai, bayan sun gama ya dawo gida ya harhaɗa kayansa ya zuba a cikin akwati ɗaya ya ɗauki computer Abir ya fito. Kofar ɗakin Tasakkawato ya iso ya kira ta ta fito, ganin si da akwati ta dafe ƙirji ta ce "Ina za ka je Zaiyan?"
Sunkuyar da kai ya yi ya ce "Mama zan tafi wajan Abokina, inda a can za mu ci gaba da binciken inda Jiddo take har Allah ya sa mu gano ta, ga wanne key É—in akwai kayanta a ciki in na sake dawowa zan amsa." Daga haka ya wuce da hanzari bai ma tsaya ta samu damar yi masa wata tambayar ba..
Da kallo kawai Tasakkawato ta bi bayan shi har ya fita, É—aki ta koma ta dauko Hijabi da handbag ta fito ta wuce..
A ɓangaren su Abba kuwa har sun gaji da laliban inda za su ga Abir sun zuba wa sarautar Allah idanu, gabaɗaya familyn duk sun shiga damuwa na rashin sanin inda take, Grandma har kwanciya a Asibiti ta yi saboda wannan hali da suka shiga,.. Abdul kuwa tun da ya dawo haiyacinsa bacci ya kaurace wa idanuwansa sakamakon abubuwan da suka tsaya masa a rai. Na farko dai ya ga Hafsat a matsayin matarsa ta sunnah ranar ji ya yi kamar ya shaƙe ta ta mutu, amma ya danne zuciyarsa ganin yadda take kuka da ya daka mata tsawa ya ce ta tafi gidansu zai rabu da ita, sosai ta ba shi tausayi dan shi kansa ya san Hafsat na son shi sosai kawai dai ba ya son haɗa jini ne da Alhaji Mustapha, sai dai kuma babu yadda ya iya ya hakura. Abu na biyu kuma ganin babu ƴar amanarsa a tare da shi, wannan abin shi ya fi tayar masa da hankali in ya tuna Wai ma Zaiyan ta aura kuma sun gudu, haka yake kwana yana salla a yana kuka tare da rukon Allah ya baiyana masa ƙanwarsa cikin gaggawa ya nemi yafiyar abin da ya mata.. Abu na uku kuma, bayan ya dawo haiyacinsa ya shiga wayarsa ya ga yadda ya dinga fadar sirrin duk wani abu da ya danganci aikinsa, a lokacin sai da na saki ƙara na takaicin duk abubuwan da ya tura wa su Alhaji Mustapha, abin karin takaicin wai har ma group gare su su huɗu ya shiga tashin hankali ganin irin abubuwan da ya faru, haka zai zauna ya yi ta Istigifari yana neman yafiyar Ubangiji kan cin amanar ƙasar shi da ya yi...
Su Alhaji Mustapha kuwa komai ya ci gaba dan yanzu an soma zaɓe sai zarya suke wajan duk wani malamin tsubbu da bokan da suka ji labarin aikin su na ci a lokacin, da zarar sun samu labari za su kai masa ziyara. Hakan ya sa duk suka rufe bakin mutane aka manta da maganar da Damisa ya yi, hakan ya sa hankalinsu ya kwanta har suke tunanin Damisa ya sheƙa jin shuru....
Ranar zaɓe suka je shi da tawagarsa suka kaɗa ƙuri'a ana ta ɗaukan vidéo ana saka wa a social media. Bayan an gama zaɓe aka tabbatar wa da Alhaji Mustapha shi ne ya ci Gwamnan Jahar ba ki ɗaya, ranar kusan kwana suka yi suna yin party inda aka kawo musu 'yan mata ƙanana sabuwar balaga dan dukkan su yara ne, a cikin su babu wadda ta kai shekaru 20 daga mai 19 sai mai 18 sai mai 17. Yaran nan na kuka haka suka sa aka musu allurar bugar da hankali suka aikata abin da suke so da su. Haka bayan kwanaki aka rantsar da Alhaji Mustapha ya ɗare kan kujerar Gwamna...
Damisa kuwa ya ji baƙin ciki da Alhaji Mustapha ya samu kujerar nan, abin da ya ƙara fusata shi da aka yi watsi da abin da ya faɗa, hakan ya sa ya bi ta ƙarƙashin ƙasa..