← Book details A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 120

Sashe 70

A Haka Nake Son Shi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

OK kawai Umma ta ce ta yi gaba tana sauri kamar za ta tashi sama. Da kallo ta bi bayan Umma har ta shige part ɗinta, fuska dauke da jimami ta nufi mota ta shiga saboda tana tsoron kar Umma ta yi wa Iman tas kuma ta ɓata mata shirin da take yi..

Tun kafin su je gidan take kiran Abdul dan ta sanar da shi za ta je gidansa amma yaki É—aukan kiran, hawayen da suka cika mata kwarmin idanu suka zubo, wannan wani irin wulakanci ne kamar ita yau Abdul yake sharewa kamar bai ma san ta ba a rayuwarsa. Hannu ta kai ta goge hawayen a daidai lokacin da Ali ya yi hon aka bude msa get, yana gama packing ta masa godiya ta nufi ciki. Nocking ta yi inda ta ji muryar Hafsat tana cewa "Waye?"

Sai da ta yi magana Hafsat ta ji muryarta sannan ta bude kofar suka rungume juna cike da farin cikin ganin juna, Hafsat ta bata rai ta ce "Besty Wallahi na yi fushi da ke, ace aurena 5 month's amma ki kasa zuwa gidana kamar na yi miki wani mugun abu?"

Murmushi Abir ta yi ta gyara zama tana kallon palon yadda ya tsaru ga photon Hafsat da Abdul nan sun hada goshi tare lumshe idanu aka dauke su, dariya ta yi ta ce "Oh ni Hauwa'u! Hafsy ku ne love wannan style na photo haka kamar a turai?" Ta faɗa tana kallon kofar da ake ƙoƙarin budewa.

Farr Hafsat ta yi da idanu sai kuma ta ɗan yi fuskar jimami ta ce "Allah sarki ƙawata, yanzu kema fa da ki na can a gidan sarauta." Ta faɗa itama tana kallon Abdul da ya yi tsaye a bakin kofa yana kare musu kallo. Kawar da kai Abir ta yi tana jin zafi da raɗaɗin ciwon son Suhal ya motsa mata ga kuma Abdul da ya yasar da ita kamar ba shi ba ne Mom ta kama hannunta ta damka a nasa ta ce ya kula da ita. Saurin saita kan ta yi jin Hafsat na yi wa Abdul Welcome back, ba ta CE masa ko uffan ba kamar yadda shi ma da kallo kawai yake bin ta kamar ya ga wata sabuwar halitta, kwafa ta yi ta kalli Hafsat da ta maƙale a jikinsa tana ce masa wanka zai yi ko abinci zai ci shi kuma ya wani girgiza kai ya ce takardu ya zo ɗauka an jima zai dawo. Dawowa wajan Abir ta yi tana ba ta hakuri ta bar ta ko ruwa ba ta kawo mata ba, murmushi ta yi kawai ba ta ce komai ba, sosai ranta ya sosu ganin Abdul da gaske ya wuce bai ko kalle ta ba duk da Hafsat ta ce ma Abir ta zo amma ya share maganar. A sanyaye ta dauki ruwan da Hafsat ta kawo mata ta sha kaɗan sannan ta mike tsaye tare da ɗaukan handbag ɗin ta ta ce "To ni zan tafi dan dama ba zama na zo yi zan koma gida ina so na yi bacci kafin ayi Azuhar."

Sake da baki Hafsat ke kallon ta sai kuma ta haÉ—e rai ta ce "Haba Besty kamar ana korar ki daga zuwa ki ce za ki tafi? Ki bari mana sai yamma kin ga yayanki zai koma office sai ni kadai a gidan. Amma jira ni ina zuwa minti biyu." Ta faÉ—a tana yin bedroom É—in ta da sauri.

Tana shiga suka yi kiciɓus da Abdul zai fito, harara ta aika masa ta ce "My love wai kai da Besty me ke faruwa a tsakanin ku? Me ta yi maka haka da zafi da har ka gan ta ka yi kamar ba ka san da mutum a palo ba? Gaskiya I'm not happy with that mood, wannan dai ba halinka ba ne yin haka. Sam ban ji daɗin ganin hakan ba a tare da kai, kai ne fa uban ta kuma dangin mahaifiyarta a ma cire dangin uba, ya kake so ta yi da damuwar da ke damun ta ko da yadda ka mayar da ita shara?"

Sai da ta gama maganar ya wani hade girar sama da ƙasa ya gyara tsayawa kamar yana filin daga, sai da ya shafa kwantaccan sajansa sannan ya ce "Oh my sweet ki rabu da Baby tun da haka ta zaɓar wa kanta rayuwa, ko irin ta kirani ba ta yi yanzu wata nawa da auren mu amma taƙi zuwa gidana sai yau ta ga dama ta zo? In kin gama matsa ki ba ni waje zan wuce ina makara." Ya faɗa yana son raɓa ta zai wuce ta sha gaban shi tana haɗe fuska..

Abir da ke tsaye palo tana jiyo tashin muryar Hafsat dan haka komai a kan kunnenta suka faɗa, wasu hawaye masu ɗumi ne suka silalo kan kuncinta ta sa hannu ta goge ta ɗaga ƙafa za ta yi gaba ta yi mutum a kusa da ita, da sauri ta matsa tare da ɗagowa ta kalle shi. Kama hnnunta ya yi fuskar nan ba alamar annuri ya ce "Wa ya ba ki izinin zuwar mini gida? Saboda kin rainani shi ya sa kike abin da ki ka ga dama ko?, To muje na sauke ki a gida shashasha kawai." Ya faɗa yana jan hannunta Hafsat na masa magana amma bai ji ba ya wuce da ita. Kuka Abir ta sa tana jin duniyar ta mata zafi, wai yau ita Abdul ke kora daga gidansa? A mota ya saka ta bai ko kalle ta ba ya ja suka bai gidan, sai da suka isa gida ya juyo ya yana kallon ta a fusace ya ce "Za ki yi shuru ko sai na kifa miki mari?"

Saurin rufe bakinta da hannu ta yi tana zubar da hawaye, so take ta fita amma ya sa lock dole ta hakura ta na sauraron fadan da yake mata na ba gaira ba dalili, sai da ya gama yi mata rashin mutumci sannan ya buÉ—e mata ta fita tana goge kwalla ta shige ciki shi kuma a zafafe y bar gidan yana ji kamar ya mata duba...

_NIGER_

Bayan Sallar isha'i Yarima Suhal ya shigo É—akin Iman ya samu ba ta nan, zama ya yi a bakin gadon yana mamakin inda ta je tun da bai gan ta a wajan su Mamma ba, wayarta da ke ringing ya hanga a tsakiyar gadon ya kai hannu ya dauka. Ganin an saka Umma a number sai ya yi picking up call É—in tare da karawa a kunne, kafin ma y yi magana ya ji Umma ta soma masifa..

"Iman ni za ki tonawa asiri a family Maitama? Wallahi zan saɓa miki yadda bakya tunani in na sake ji ko gani kin takurawa Abir sai ta yi wa mijinki magana ya kawo ki gida, uban me za ki yi a gidan in kin zo? Ki fita idanuna kafin na hada ki da Daddynku in ya dawo. In ban da ke sakarya ce a aura miki miji nagartacce mai hankali ga mulki amma kike cewa ke wai an miki auren cin amana uban wa kika ci amanar? Ki ci gaba da shashancin kika sake ki ka fusata mijinki ya koro ki to ki nemi wata uwar b dai ni ba dan banki. Ina magana kin yi shuru kin kyale ni wato ga mahaukaciya na yi ta haukana ni kadai ko? "

Murmushi Suhal ya yi yana kaÉ—a kai ya ce "Umma barka da dare, ba fa Iman ba ce ta dan fita ta bar wayar ne a É—aki, sannan ki daina damuwa da duk abin da take za ta daina in ta yi hankali."

Kwalalo waje Umma ta yi tana dafe ƙirji, hamdala ta yi da duk maganar da ta faɗa babu mai aibu a ciki, hakan ya sa ta ɗan yi murmushi ta ce "Haba Yarima yanzu kamar kai ta tasa ka gaba tana ma rashin kunya ai wannan ba tarbiyar da muka ba ta ba ce."

"Ihum Umma kenan, ai kar ki wani damu da lamarin Iman za ta fasa soon in sha Allah, sai da safe." Ya faɗa yana katse kiran; ƙin aje wayar ya yi ya shiga whatsapp inda ya shiga number Abir ya ga yadda take danne voice tana kuka take cewa ta yi masa magana ita a mayar da ita gida, murmushi ya yi ya kunna voice ɗin Abir inda take ta ba ta haƙuri tana nuna mata ta bi umarnin mijinta. Wani abu ne ya tsaya masa a zuciya jin muryar Abir ciwon so ya motsa mishi a hankali ya buɗe na Iman, nan ya ji tana faɗin ita fa a daina haɗa ta da Yarima Suhal ita wannan auren cin amanar ba za ta lamunta ba dole ya sake ta ya auri Abir, emoji ɗin dariya da dafe goshi ya ga Abir ta turo mata.. Fita ya yi daga whatsapp ɗin jin ana ƙoƙarin buɗe ƙofar banɗaki.

Kanta a ƙasa ta ƙaraso bakin wardrobe ɗin ta buɗe ta soma tsaɓar kayan da za ta saka, kusan duk wani ɗabi'u nata irin na Abir ne musamman wajan saka kaya in sun fito daga wanka su dinga ruwan idon wani kalar kaya za su saka, harɗe hannu Suhal ya yi yana kallon ta yana murmushi in ta yi wani abin sai ya ga kamar yana tare da princess ɗin sa..

Haka ta yi ta birkito kayan tana jan tsaki har da kama ƙugu, sai can ta zaɓi wata riga iya gwiwa mai laushi da hular ta, murmushi ta yi ganin kalar kayan da Abir ɗin ne ke so ta cire towel ɗin kan ta cire na jiki dan ta sa kayan ko mai ba ta shafa fa, kamar an ce ta kalli madubin da ke manne jikin wardrobe ɗin ta ga mutum ya kafe ta da idanu ba ko ƙiftawa, ƙara ta kwalla tana zubewa a ƙasa. A zabure ya sauko daga kan gadon ya yo inda take durkushe tana kurma ihun kuma jikinta na rawa ta ma kasa ɗaukan towel ɗin ta ɗaura duk ta kiɗime, sunkuyawa ya yi a ruɗe yana faɗin "Iman lafiya? Ko wani abu ya same ki?"
Chapter 70 · 0% Book details